Home Rahoto Gwamnan Kano ya ba da shawara ga ma’aurata 1500 da za’a yi...

Gwamnan Kano ya ba da shawara ga ma’aurata 1500 da za’a yi wa Auren Gata

15
0

Auren Gata: Gwamna Abba Gida Gida ya shawarci ma’aurata 1,500 kan hakuri da tsoron Allah

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shawarci ma’aurata 1,500 da za su shiga shirin auren gata na shekarar 2026 da su gina zamansu bisa amana, hakuri, mutunta juna da tsoron Allah.

An bayyana hakan ne yayin taron wayar da kan ma’auratan da hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta shirya a dakin taro na Coronation Hall, inda Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa, ya wakilci gwamnan.

Gwamnan ya ce zaman aure na bukatar sadaukarwa, tausayi da fahimtar juna, yana mai kira ga ma’auratan da su warware sabani ta hanyar tattaunawa domin tabbatar da zaman lafiya a gidajensu.

A yayin taron, malamai da kwararru sun gabatar da laccoci kan muhimmancin aure a Musulunci, hakkoki da nauyin ma’aurata, da hanyoyin magance rikice-rikicen iyali.

A cewarsa, gwamnati za ta tallafa wa kowanne ango da yadin shadda, hula, buhun shinkafa da jarkar mai, yayin da kowace amarya za ta karɓi Naira 200,000 domin sadaki da jari, tare da kayan ɗaki da sauran kayan amfanin gida.

An ce za a daura auren ne ranar Juma’a a Babban Masallacin Juma’a na Kano da kuma hedikwatar dukkan kananan hukumomi 44 na jihar, kafin a kammala shirin ranar Lahadi da rabon kayan tallafi ga sabbin ma’auratan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here