Home Siyasa Duk wanda ke son Karɓemun Mulki a 2027 Sai fa ya shirya...

Duk wanda ke son Karɓemun Mulki a 2027 Sai fa ya shirya Yaƙin Turnuku—Shugaba Tinubu ga ‘Yan adawa

23
0


Duk wanda ke son Karɓemun Mulki a 2027 Sai fa ya shirya Yaƙin Turnuku Harzuwa matakin Ƙarshe  ina fatan kun shirya ko? –Shugaba Bola Tinubu ga ‘yan adawa.
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa duk wanda ke da burin karɓe masa mulki dole ne ya kasance a shirye ya yi gogayya da shi har zuwa ƙarshe.
Tinubu ya bayyana cewa ba zai ja da baya daga neman wa’adi na biyu ba, yana mai cewa masu son kwace masa kujerar shugaban ƙasa dole ne su nuna cikakken ƙarfi da jajircewa idan har suna son kayar da shi a zaɓe.
Kalaman shugaban ƙasar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen siyasa gabanin babban zaɓen 2027, inda jam’iyyu da ‘yan siyasa ke ƙara zafafa fafatawar neman goyon bayan al’umma.
Ana sa ran furucin na Tinubu zai ƙara ɗaukar hankalin masu ruwa da tsaki a fagen siyasa, yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan makomar zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here