Mutanen Arewacin Nijeriya musamman Hausawa sun yi fice a wurin zuwa ci rani a ƙasashen waje, sun fi yawan zuwa maƙwabta kamar Nijar, Benin, Gana da Libiya.Mutanen Arewa da yawansu sukan je neman aikin yi a waɗan nan ƙasashen yayinda wasu ke tafiya domin gudanar da sana’a ƙarama.Ƙasƙanci da bauta da haɗarin da suke sanya kansu cikin wannan neman ya sa an binciki lamarin tare da tattaunawa da waɗanda abin ya shafa domin ji daga bakinsu.
Muhammad Yusuf yakan je ƙasar Nijar daga Sakkwato ya ce “nakan je Nijar domin gudanar da sana’a a can, mutanen ƙasar ba su da matsala da duk wanda zai shigo ƙasar, za ka suna mu’amala da shi lafiya lau ba tsana ko wata kyara.
“In da matsala take tsakanin baƙo ne da hukuma na farko kafin ka shiga ƙasar sai ka yanki katin shiga ƙasar mai wa’adin awa 24, za ka biya jikka uku wanda kuɗinsa zai kai kusan 5000, bayan lokacin ya ƙare za ka sabunta shi, in da lamarin yake da muni wa’adinsa ya ƙare ba ka da kuɗin sabunta wa ba za su saurare ka ba, za su tsare ka na tsawon lokaci in ba ka yi sa’a ba za su ɗaure ka kan wannan laifin.
“Ya ce mutanenmu da ke zuwa sana’a ba su iya kama gidan haya saboda tsadar shi, sai dai ka kwana a tashar mota ka biya Mai gadi kuɗin kwana da kayan da kake sayarwa, ba irin Nijeriya ba da mutane in ba su da wurin kwana su tafi masallaci su kwana, can ba su yarda ba da an ƙare sallah za a rufe masallaci kowa ya kama gabansa.
Magana ta gaskiya in ba ‘yan uwa gare ka a can ba, kuma ba ka da kuɗi isassu rayuwar ƙasƙanci za ka riƙa yi, amma ba wata ƙyama ga mutane ƙasa.
Wani da yake zuwa ƙasar Libiya ya ce duk wanda zai tafi Libiya in daga Sakkwato ne zai bi ta Sabon Birni ya shiga Maraɗi, Tawa, Agadaz sai Libiya, in ta Illela ce zai shiga Tawa ne sai Agadaz, “Da ka bar Agadaz ka kawo Dardar in ka bi Gabas Libiya ka yi, in ka ɗauke hanyar kudu Mali za ka je, duk masu tafiyar nan suna cikin haɗarin wahala har ma da rasa rayuwa, a hanyar akwai ‘yan fashi da makami in kuka yi rashin sa’ar haɗuwa da su, za karɓe duk wani abu naku, sannan ku masu tafiyar direba ne kawai ya san hanya shi ne idonsu da zaran ya ɓata hanya dukanku margaya ne har shi domin za ku yi ta tafiya cikin hamada ba randa za ku fita har Man motarku ya ƙare ku shanye ruwanda kuka zo da shi sai mutuwa.
Matsalar da ke nan yashin Hamadar da zaran ka bi samansa kana wucewa zai rufe ba yanda wani zai biyo ya ga sawunka don haka da ka ɓace shi kenan, sai dai in Allah bai yanke kwananka ba, amma dai tabbas da ka ɓata sai ka sha baƙar wahala.
“In ka kammala da matsalar Hamada ka shiga Libiya in ka yi rashin sa’a kamar ni jami’an tsaron su suka kama ka, za su kaika ofis a tsare ka ya danganta da tsawon lokacin da za ka ɗauka a dawo da kai ƙasar ku, mu mun shafe kwana 13 a tsare wurinsu kafin su kwashe mu zuwa Nijar, kasani fa ɗan hursunan Libiya yafi ma’aikacin Nijeriya jin daɗi, domin ɗan hursuna nada wurin kwana da ruwa da wuta kullum sai an kawo masa abinci sau uku a rana, ya ci sai ya ƙoshi, abin da kawai yake damuwa anan a tsare kake ba ka zuwa ko’ina.
“Ina ba a kama ka ba bauta ce za ka yi, domin duk wani aikin ƙarfi Larabawan ba su yi ba, ku ne gadin gona da gida da gyaran hanya da sauran abubuwan wahala, amma kam suna biya za a baka kuɗi sai ka ji tsoro, kullum kana cikin fargaba ta jami’an tsaro.
Wata mata da ta tafi Libiya amma ta dawo gida, ta ce ba wani abu da ake kai mata a can in ba karuwanci ba, “anan gida agent ba ya gaya ma komai na gaskiya sai dai ya ce ma aiki ne za ka yi irin na gida wanke-wanke da shara a gida, ba wani aiki mai wahala, za ka samu kuɗi ka yi wa kanka abu mai amfaninka, za ka ɗauka taimakonka zai yi, a haka zai ɗauki nauyin tafiyarka har zuwa illela, a can za a haɗa ka da wani zuwa Ƙwanni, wani ya ɗauke ka zuwa Agadaz, wani ya ɗauke ka zuwa Libiya da ka shiga Libiya kin zama nama domin a gida za a ɓoye ku, ba wadda za ta fita sai wadda za a kai wurin karuwanci, a haka za ki ta wahala abinci ne kawai ake ba ki, kafin ki san kan gari ki gudu ko ki bi wata hanya daban Agent da kike wurinsa ya fitar da kuɗinsa da ya kashe aka kawo ki nan har da riba.Ina baiwa mata shawara su guji duk wanda ya ce zai taimake su a bar gari da su, ba wani taimako bauta ce da ƙasƙanci zai sanya su.
Sani Muhammad mai zuwa ƙasar Birnin ya ce sukan bi ta Dole kaina wasu ta tsamiya a Kamba, ba su samu wata tsangwama da mutanen can har da jami’an tsaron su, za ka ta harkokinka ba ruwan kowa da kai, ba tsangwama, hayar gidansu ce kawai ke da tsada a wata wata jika 15 kudin Nijeriya 35,400 muke biya a duk wata.Kabiru Babba da ke zuwa Ghana ya ce ba su samun kowace tsangwama a tsakaninsu da mutanen gari da hukumomi ƙasar, in ba yanzu da aka fara takun saƙa da wasu ƙabilar Igbo ba komai lafiya lau yake a can.






