Home Finafinnai Baɗala a Kannywood: Hukumar tace finafinnai ta Kano ta dakatar ‘yan wasan...

Baɗala a Kannywood: Hukumar tace finafinnai ta Kano ta dakatar ‘yan wasan Hausa biyu

5
0

Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta sanar da dakatar da wasu jaruman Kannywood biyu, Adam Garba da Amina Uba Hassan, daga gudanar da harkokin fim a faɗin jihar na tsawon shekara guda.

Cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran hukumar, Comrade Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a madadin shugaban hukumar Malam Abba El-Mustapha, an bayyana cewa matakin ya biyo bayan bayyanar jaruman a wani bidiyo da hukumar ta ce ya saɓa da tarbiyya.

Sanarwar ta ƙara da cewa bidiyon ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar Jihar Kano, lamarin da ya sa hukumar ta ɗauki matakin ladabtarwar domin kare martabar masana’antar Kannywood.

A cewar hukumar, dokarta ta ba ta ikon dakatar da duk wani ɗan masana’antar fim da ya karya ƙa’idojin da aka shimfiɗa, tare da gargadin cewa rashin bin umarnin na iya jawo hukunci mai tsauri.

Shugaban hukumar, Malam Abba El-Mustapha, ya kuma gargaɗi masu harkar Kannywood da su guji duk wani abu da ka iya zubar musu da mutunci ko rage darajar masana’antar a idanun jama’a.

Haka kuma, ya buƙaci masu shirya fina-finai da daraktoci su mutunta umarnin dakatarwar, yana mai cewa duk wanda ya ci gaba da aiki da jaruman da aka dakatar zai fuskanci mataki a ƙarƙashin doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here