Home Rahoto Bayan Kashe mutane 17 ɗan takarar Gwamna a ADC ya baiwa Gwamnatin...

Bayan Kashe mutane 17 ɗan takarar Gwamna a ADC ya baiwa Gwamnatin Sakkwato shawara

23
0

Dan takarar gwamnan a jam’iyyar ADC, Honarabul Manir Muhammad Ɗan’iya ya bayyana alhini da damuwarsa kan harin da ‘yan bindiga suka kai kai ƙauyen Ɗangulbi dake ƙaramar hukumar Tureta, a Sakkwato wanda rahotanni suka ce ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 17, ciki har da masu yawon sallah 7.

Ɗan’iya ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, mai tayar da hankali da kuma wani abin tunatarwa game da kalubalen rashin tsaro da ke ci gaba da addabar al’ummomi a jihar Sakkwato da sauran sassan Najeriya.

A cikin wata sanarwa wanda sakataren yada labaransa, Aminu Abdullahi ya fitar, ɗan takarar gwamnan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, al’ummar karamar hukumar Tureta da daukacin al’ummar jihar.

Ɗan’iya ya nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa wasu daga cikin wadanda suka rasa rayukansu matafiya ne da suka dawo gida domin gudanar da bukukuwan Sallah tare da iyalansu, yana mai cewa hakan ya kara sanya lamarin ya zama mai matukar tayar da hankali.

Ya jaddada cewa yawaitar hare-haren da ake kaiwa al’ummomi a sassan jihar na bukatar karin hadin kai da dabarun tsaro masu dorewa tare da samun cikakken hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya, ta jiha da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin Sakkwato ta yi aiki tuƙuru domin ganin ta magance matsalar tsaron ta hanyar amfani da dubarun zamani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here