Home Labarai Atiku ya caccaki Fadar Shugaban Ƙasa kan kwatanta Najeriya da China da...

Atiku ya caccaki Fadar Shugaban Ƙasa kan kwatanta Najeriya da China da batun ƙwace kadarori a Amurka

17
0

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki Fadar Shugaban Ƙasa kan amfani da tsarin shari’ar ƙasar China wajen kare Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya na mai cewa hakan ya ƙara jawo hankalin jama’a kan zarge-zargen da su ka shafi tsohon tarihin shugaban.

Atiku, ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya ce Fadar Shugaban Ƙasa ta kauce wa mayar da martani kan muhimman batutuwan da ya taso, maimakon haka ta mayar da hankali kan cin mutuncinsa.

Ya ce kwatanta batun da China ba ya taimaka wa gwamnatin Tinubu, domin a cewarsa ƙasar China na da tsauraran dokoki kan laifukan safarar miyagun ƙwayoyi da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.

Atiku ya jaddada cewa ba a taɓa samun shi da laifin cin hanci ba, safarar miyagun ƙwayoyi ko wani laifi a kowace kotu a Najeriya ko wata ƙasa ba.

Ya kuma ce idan gwamnati na son amfani da China a matsayin ma’aunin gaskiya da riƙon amana, to ya dace a tambayi yadda hukumomin ƙasar za su ɗauki batun ƙwace dala 460,000 da gwamnatin Amurka ta yi a wata shari’ar farar hula da ta shafi zargin kuɗaɗen da ake alaƙanta da safarar miyagun ƙwayoyi da halasta kuɗaɗen haram, batun da ya taɓa shafar Shugaba Tinubu.

Haka kuma, Atiku ya ce gwamnatin Tinubu ta fi dacewa ta mayar da hankali wajen magance matsalolin tattalin arziki, yunwa, rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ke addabar ‘yan Najeriya, maimakon shiga cece-kuce na siyasa.

Wannan martani na Atiku ya biyo bayan saƙon mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, wanda ya zargi Atiku da cin hanci a lokacin da yake mataimakin shugaban ƙasa, tare da cewa da ace ɗan ƙasar China ne, da tuni yana gidan yari. Atiku ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa babu wata kotu da ta taɓa samun shi da wani laifi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here