Home Rahoto Atiku Ya Bukaci Tinubu Ya Bayyana Cikakkun Bayanai Kan Bashin Dala Biliyan...

Atiku Ya Bukaci Tinubu Ya Bayyana Cikakkun Bayanai Kan Bashin Dala Biliyan 5 Na Bankin Abu Dhabi

11
0

Atiku Ya Bukaci Tinubu Ya Bayyana Cikakkun Bayanai Kan Bashin Dala Biliyan 5 Na Bankin Abu Dhabi

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bayyana cikakkun bayanai kan bashin dala biliyan 5 da aka samo daga First Abu Dhabi Bank.

Atiku ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su san yadda za a kashe kuɗin, sharuddan bashin da kuma yadda za a biya shi, ganin cewa nauyin bashin zai rataya ne a wuyan ‘yan ƙasar.

Ya kuma soki gwamnatin Tinubu kan yawan karɓar bashi ba tare da bayyana cikakken amfani da kuɗaɗen ba, yana mai cewa hakan na iya jefa ƙasar cikin ƙarin matsalar bashi.

A cewar Atiku, gwamnati na da alhakin yin cikakken bayani kan duk wani bashi da aka karɓa da sunan ‘yan Najeriya, domin su ne za su ɗauki nauyin mayar da kuɗin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here