Home Siyasa Atiku ya bukaci INEC ta bayyana kamfanonin da za su buga kayan...

Atiku ya bukaci INEC ta bayyana kamfanonin da za su buga kayan zaɓen 2027

9
0

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bukaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana sunayen kamfanonin da ta bai wa kwangilar buga muhimman kayan zaɓen 2027, tare da bayyana hanyoyin da aka bi wajen bayar da kwangilolin.

Atiku, ta bakin daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Phrank Shaibu, ya kuma bukaci hukumar ta tabbatar ko ta musanta rahotannin da ke cewa kamfanin Hitech ko wani kamfani mai alaƙa da shi ya samu kwangilar buga kayan zaɓen.

Ya nuna damuwa kan rahotannin sauya wasu manyan jami’an sassan hukumar, musamman sashen gudanar da zaɓe da na rajistar masu zaɓe, yana mai cewa INEC ta bayyana dalilan sauye-sauyen da kuma ƙa’idojin da ta bi wajen naɗa jami’an.

Atiku ya kuma nemi hukumar ta bayyana kamfanonin da aka bai wa kwangilar, kayan zaɓen da kowannensu zai buga, jihohin da aka ware musu, kuɗin kwangilolin da kuma matakan tsaro da za a bi wajen bugawa, adanawa da kai kayan zaɓen.

Ya ce rahotannin da ke cewa sama da rabin muhimman kayan zaɓe, ciki har da na zaɓen shugaban ƙasa, za a bai wa wani kamfani da ba a bayyana sunansa da cikakken bayanansa ba, na buƙatar gaggawar bayani.

Haka kuma, ya nuna damuwa kan rahotannin cewa kamfanin Nigerian Security Printing and Minting Plc (NSPMC) zai buga kayan zaɓe na jihohi 15 zuwa 17 kacal, yayin da kamfanoni masu zaman kansu za su kula da sauran jihohin.

Atiku ya ce ya kamata INEC ta tabbatar da cewa ba a yi siyasa ko nuna son kai wajen bayar da kwangilolin ba, yana mai cewa duk wani rashin bayyana bayanai kan lamarin na iya rage amincewar jama’a ga zaɓen 2027.

Ya kuma yi gargaɗin cewa bai kamata a ɗauki wani jami’in INEC a matsayin wanda ba zai yi adalci ba saboda ƙabila ko asalinsa, sai dai hukumar ta tabbatar da gaskiya da bin ƙa’ida wajen gudanar da ayyukanta.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma bukaci INEC ta bai wa jam’iyyun siyasa damar sanya ido kan tsarin samar da kayan zaɓen, tare da amfani da ƙwararrun kamfanonin cikin gida wajen buga takardun zaɓe masu muhimmanci.

Atiku ya jaddada cewa jam’iyyar ADC za ta sa ido sosai kan shirye-shiryen zaɓen, tare da sanar da masu sa ido na cikin gida da na ƙasashen waje idan aka samu rashin gaskiya ko rashin bayyana bayanai.

Ya ce dole ne INEC ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa za a gudanar da zaɓen 2027 cikin gaskiya da adalci, yana mai gargadin cewa duk wani yunƙurin maguɗi zai fuskanci adawa ta hanyoyin dimokuraɗiyya da doka ta amince da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here