Home Siyasa Atiku ya buƙaci a gaggauta sakin matasa da aka...

Atiku ya buƙaci a gaggauta sakin matasa da aka kama a Borno don sun sanya rigunan “Tinubu Must Go”.

17
0

Ya ce idan taken siyasa ne ya sa aka tsare su, to wadanda suka bayar da umarnin tsarewar dole ne su yi bayanin yadda sanya riga zai zama laifi a tsarin dimokuradiyya.

A wata sanarwa da hadimin Atiku kan sha’anin yada labarai Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce Shugaba Bola Tinubu ya taba tsayawa tare da ’yan Najeriya da ke zanga-zangar adawa da tsadar man fetur a lokacin mulkin Shugaba Goodluck Jonathan, amma a yanzu yana jagorantar wani yanayi na tsadar rayuwa da ya sanya man fetur, abinci, sufuri da wutar lantarki suka yi tsada matuka.

Atiku ya bukaci hukumomin da abin ya shafa su bayyana inda ake tsare da mutanen, su ba su damar tuntubar iyalansu da lauyoyinsu nan take, sannan su sake su idan taken siyasa ne dalilin kama su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here