Home Labarai Atiku ya ba da tallafin miliyan 20 ga iyalan masu haƙar ma’adinai...

Atiku ya ba da tallafin miliyan 20 ga iyalan masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu a Neja

22
0

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 20 ga iyalan masu hakar ma’adinai 37 da suka mutu a hannun Hukumar Tsaron farin kaya ta Civil Defence a Jihar Neja kwanan nan.

A cewar wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya bayyana bayar da tallafin ne yayin wata ganawa da iyalan masu hakar ma’adinan da suka rasu.

Sanarwar ta ce ɗan takarar na ADC ya kuma ziyarci Minna, babban birnin Jihar Neja, inda ya jajanta wa Sarkin Minna kuma Shugaban Majalisar Masarautu ta Minna, Mai Martaba Alhaji (Dr.) Umar Farouk Bahago, da kuma tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya).

Ya bayyana cewa Najeriya ba za ta iya tabbatar da makomarta ba tare da karfafa wa matasa ba, tare da faɗaɗa damar da suke da ita da kuma ba su damar gudanar da sana’o’i na halal kuma masu amfani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here