Home Siyasa APC ta fitar da jadawalin zaɓen fidda-gwani, ta saka kuɗin takarar shugaban...

APC ta fitar da jadawalin zaɓen fidda-gwani, ta saka kuɗin takarar shugaban ƙasa ₦100m

3
0

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana jadawalin shirinta na zaɓen 2027, inda ta saka zaɓen fidda-gwani na takarar shugaban ƙasa a ranakun 15 zuwa 16 ga Mayu, 2026.

A cewar takardar jadawalin da Sakataren Tsare-Tsare na Ƙasa na APC, Sulaiman Argungu, ya sanya wa hannu a ranar Litinin, jam’iyyar za ta fara sayar da fom ɗin neman takara daga 25 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu, 2026 a hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa.

Haka kuma, an bayyana cewa ƙarshen karɓar fom ɗin zai kasance 4 ga Mayu, 2026.

Farashin fom ɗin takara

APC ta saka:

₦100m na takarar shugaban ƙasa (₦30m neman takara + ₦70m na fom ɗin tsayawa takara)

₦50m na gwamna

₦20m na Sanata

₦10m na Majalisar Wakilai

₦6m na Majalisar Jiha

Sauran jadawali

Tantance ‘yan takara: 6 – 8 ga Mayu

Fitar da sakamakon tantancewa: 11 ga Mayu

Duba ƙorafe-ƙorafe: 12 – 13 ga Mayu

Zaɓen fidda-gwani shugaban ƙasa: 15 – 16 ga Mayu

Sauran matakan zaɓe:

Majalisar Wakilai: 18 ga Mayu

Sanata: 20 ga Mayu

Majalisar Jiha: 21 ga Mayu

Gwamna: 23 ga Mayu

Kammala duk ƙorafe-ƙorafe: 25 ga Mayu

Rangwame ga wasu ‘yan takara

APC ta kuma ba da rangwame ga:

Mata

Matasa

Masu nakasa

Wadannan za su biya kudin fom ɗin neman takara kawai da kashi 50% na fom ɗin tsayawa takara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here