Home Siyasa Ana shirin hana ADC shiga zaɓen 2027 – Atiku

Ana shirin hana ADC shiga zaɓen 2027 – Atiku

22
0

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa akwai wani sabon shiri da ake yi domin hana jam’iyyar ADC shiga zaɓen shekarar 2027.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce ya samu sahihan bayanai da ke nuna cewa ana amfani da hanyoyin siyasa da na shari’a domin hana jam’iyyar shiga zaɓen.

Ya ce manufar wannan shiri ita ce raunana ‘yan adawa tare da hana ‘yan Najeriya damar zaɓar shugabanninsu cikin ‘yanci.

Atiku ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da ƙoƙarin tantance irin jam’iyyun adawa da za su shiga zaɓe, yana mai cewa idan har gwamnati tana da ƙarfin goyon bayan jama’a, bai kamata ta ji tsoron ADC ba.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ce ana amfani da wasu cibiyoyin gwamnati, ƙarar kotu da matsin lamba na siyasa wajen tauye ayyukan ‘yan adawa.

Ya ƙara da cewa gwamnatin ƙasar ta fi mayar da hankali kan siyasa maimakon magance matsalolin tattalin arziki, tsaro, yunwa da hauhawar farashin kayayyaki da ke addabar ‘yan Najeriya.

Atiku ya yi kira ga bangaren shari’a, hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta ta INEC, hukumomin tsaro da ƙungiyoyin farar hula da su kasance cikin shiri domin kare sahihancin tsarin zaɓe.

Ya jaddada cewa hana ADC shiga zaɓen 2027 zai zama babban barazana ga dimokuraɗiyyar Najeriya tun bayan dawowar mulkin farar hula a shekarar 1999.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here