ANA BARIN HALAL....: Fita Ta 15
ANA BARIN HALAL....:
*(Based on true life strory*)
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
*PAGE* 15
Washegari muna tashi muka raba kan mu, wasu sukahau gyaran gidan, wasu suka fara haɗa abun karyawa, muna gamawa kowa ta shiga wanka, wajajen ƙarfe 12:00pm muna shirin fita zuwa chan gida, a haraban gidan muna tsaye muna jiran fitowan Aunty bintu sai ga motan yayah Ahmad ta kunno kai, yana fitowa lokacin Aunty bintu ma tafito daga nata gidan, "yauwa Alhmdllh ga ango ma ya shigo sai ya rage wasu tunda har yanzu drivern bai zo ba", Aunty bintu ta faɗa tana gyara yafan gyalenta, yana fitowa ɗayan side ɗin ma aka buɗe sai ga M.G ya fito shima, yana rufe motan kowa ya ƙaraso inda muke, gaida Aunty bintu yayi tana tsokanan shi da ango kasha ƙamshi, shidai murmushi kawai yake bai bata amsa ba, sai hannu da ya miƙa ya amshi Areefh da yake hannun hafsy, wasa ya mishi yana ta ɓangala mishi dariya, sannan ya miƙawa hafsy yaron, mu kuma muka shiga gaishesu shida M.G, gaba ɗaya idon M.G yana kaina fuskan shi ɗauke da murmushi, Aunty bintu ta tambayi yayah Ahmad akan daga nan gida zai wuce? Ya amsa mata da ehh, yanzu ma yazo duba ac da aka chanja na ɗakin shine, yana so yaga ko sunyi yadda yake so, "tou shikenan bari mu baka mutum uku, dama driver muke jira, naga kuma ya ɓata mana lokaci tun ɗazu yake cewa zai fito ya kai aika ne," riƙo hannu na yayi muka fara tafiya chan side ɗinshin, yana amsawa Aunty Bintu da babu komai sai a bar mutum uku, bari ya duba ya fito,
Aunty b tace "tou maryam da hadiza kujira Aysha sai ku taho ku uku, fatima, zainab, hafsy, ummitah ku kuma ku shiga mutafi, uku a baya ɗaya a gaba,"
Ɗaga muryah hafsy tayi da ƙarfi tana "wlh yaya duk abunda ka bata nima sai an bani, don na lura da wayon da ake mun, kai da yayah mohd kowa ya samo sai ya yafito ta, yayah umar ne kawai mai tunawa da ni", tana gama faɗa ta wuce gaban motan da sauri don taga zainab tayi gaban zata shiga, anan ma sai da suka yi ɗan hali da zainab, tace dole hafsy ta koma baya ae itace babbah, amma firr hafsy taƙi fita, tana cewa ae ita tana riƙe da yaro a hannunta, ganin Aunty B bazatace komai ba yasa zainab shiga gaban ta wani ɗaure fuska kaman....., ita dai fatima dariya takeyi ƙasa-ƙasa, gefe ɗaya maryam da hadiza suka koma suna jiran mu fito.
Muna shiga side ɗin yayah Ahmad na wangale baki, domin suna gama jeren babu wanda yazo a cikin mu, Aunty ma'u ne ma naji suna hiran haɗuwa da tsaruwan gidan, haka yayah Ahmad ya zaga dani ko ina na cikin gida, "kai gidan nan yayi kya yayah, gashi kuma ba'a nan zaku zauna ba, ae da Abujan aka kai kayan nan", na faɗa hannu na riƙe cikin nashi muna fitowa daga kitchen ɗin, dariya yayi mai ɗan sauti yace, "shatu na ae kayan da suka saka a abujan yafi wannan tsari da haɗuwa, nan kawai sunfi zuba kaya mai yawa ne, chan kuma 2bed room ne 1 parlor, amma chan ae yafi kyau, komai white aka saka achan, ɗayan ɗakin ne ma suka saka Brown bed, amma parlor da nawa room ɗin komai white ne," yayah nikan gidan nan ya mun kyau irin sosai ɗinnan, kuma ya dace da kai yayah nah", na faɗa ina kallon fuskan shi, murmushi yayi kawai,
M.G ne ya bani amsa da , "sister naga alaman irin wannan kayan zamu saka miki ko? Tou kiyi gaggawan kawo mana suruki idan kina soa miki irin wannan kayan", ya faɗa yana bina da kallo fuskan shi ɗauke da murmushi, saida naji faɗuwar gaba mai ƙarfin gaske lokacin da muka haɗa ido da shi, domin wani irin kyau yake da shi kaman wani india, gashi fara'a da murmushin fuskan shi yana ƙara mishi kyau na sosai sosai ɗinnan, don na lura kaman yasan fara'an na ƙara mishi kyau shiyasa yake yawan yi, gashi da wani dogon hanci da wasu manya - manyan idon shi masu masifar haske, abunda na lura yafi A.G manyan ido da dogon hanci, shi kuma A.G idon shi basu da girma sosai kuma basu da ƙanƙanci, sai dai sukuma round ne su masu yawan gashi ido da gashin gira, gashi na lura hancin bamai tsayi bane irin na M.G, sai dai suna da masifan kyau, kuma shi bai cika buɗe idon shi waral ba, yana ɗan lumshe su kaman yana tsoron wani abu ya faɗa mishi, sannan yafi tsayi kaɗan kuma bai kai M.G jiki ba, dukkan su dogaye ne, amma A.G yafi tsayi kuma yafi haske, M.G yafi kyau amma ba lokaci ɗaya zaka fahimci hakan ba, saboda farinsu da tsayin su yasa har ake ganin kaman suna kama, amma ni ranan ƙasa - ƙasa na ƙare musu kallo har na fahimci abunda mutane da yawa basu fahimta ba, yana faɗin haka na rufe ido na a jikin yayah Ahmad, dukkan su dariya sukayi, yayah Ahmad yace, "ayshaa tana kula samari ne ma, ae inaga bata ma kula su, amma duk ranan da ta kawo mun miji insha Allahu kayan da zamu saka mata sai yafi wannan burgewa da kyau", murmushi nayi ina kallon yayah Ahmad ina jin wani farin ciki a zuciyata da Allah ya bani yayun da suke sona, buɗe baki M.G yayi cike da neman zolaya yace, "waya gaya maka mai kyau bata da samari? ae Allah kaɗai yasan yawan su, ta ɓoye maka ne, amma ni zamuyi labule nasan duk zata lissafo min su, ni kuma sai na tantance na zaɓa mata guda ɗaya gwani", ya faɗa still idon shi yana kaina, nidai juyawa nayi nabar parlon ina jin dariyan su.
Shigan mu gidan muka tarar da A.G tsaye da wasu abokan su guda uku a ƙofan side ɗin su yayah Ahmad, shi dai yana gefe yana waya, amma tunda mukayi parking muka fito ya maida kanshi kanmu, ƙura mana ido yayi kaman ranan yafara ganin mu, ganin yana wuya sai niyyan wucewa batare dana gaishe shi ba, amma na gaida sauran abokan yayan, don wasu ma sun ƙara fitowa, na juya naji muryan shi ƙasa - ƙasa yace, " Zonan" kaman zan nuna banji ba sai naji ya sake cewa, "ba ƙiranki nakeyi ba"? Da sauri na ƙaraso inda yake, bai cire wayan a kunnen shi ba naga ya wuce wurin motan shi bayan ya mun alaman na biyo shi, haka na juya na bi bayan shi jiki a sanyaye, boot ɗinshi naga ya buɗe yasaka hannu cikin wani jaka bayan ya zuge ziff ɗin jakan ya ɗauko wani envelope, miƙo mun yayi batare da ya cire wayan a kunnen shi ba, hannu biyu na saka na karɓa ina bin shi da kallon neman ƙarin bayani, "na dinner kiyi amfani da shi" yana faɗa bai sake bi ta kaina ba ya wuce inda su yayah suke, ko godiya ban samu daman yiba ya wuce, na juya sai naga idon M.G akan mu, ganin haka sai na fasa zuwa nayi godiyan kawai nayi cikin gida.
Ina shiga ɗakin ummie nah na wuce, tun a parlor na fara gaida mutane, a nan naga su Aunty b da su Aunty asma'u zaune, ummitah da maryam kuma sun fito zasuyi gidan su, nan maryam tace mun sai anjuma zasu shigo, ɗaga mata kai nayi don nasan ƙarya takeyi don tace bazata zo gayyan soɗiba, don habiba har yau bata ce mata komai ba, ko a group da jammy tayi magana bikin habiba bata ce komai ba, daga baya ma sai mukaga tayi left a group ɗin, nan kuwa jammy tafara masifa da kyar na danne ta, murmushi nayi kawai na matsa mata ta wuce, daga nan nayi ɗakin ummie na, dayake safiya ne su huɗu ne kawai a ɗakin daga ummi da goggo sai ƙawayen ummie guda biyu, gefen goggo kuma zainab ce ke zaune suna magana ƙasa-ƙasa, bayan na gaishe su na wuce wurin ummie, zama nayi a gefenta na gaishe ta, na miƙa mata envelope ɗin hannu na,ƙasa-ƙasa nake mata bayanin abokin yayah Ahmed ne ya bani wai na liƙi a wurin dinner, karɓa tayi ta buɗe, da sauri ta ɗago ta dubeni tace, "Ayshaa nasan bazaki roƙe shi ba amma meyasa zai baki kuɗi masu yawa haka, 100k ne fah ƴan 500, bounch 2, yayi yawa ae, kuma haka kawai ya baki"? Ta faɗa tana jawo wayanta, ni dai bance komai jin tana ƙiran yayah Ahmad yazo ya sameta a ɗakin mu, daga nan babu ɓata lokaci ta miƙe tace na biyota, muna shiga kowa sai ga yayah Ahmad ɗin ya shigo, dama muna shiga ta sallami su hafsy waje, ummie nuna mishi kuɗin tayi tana mishi bayanin wai abokin shine ya bani, murmushi yayi yace, "ummie A.G ne, zai bada abunda yafi haka ma, nima inayiwa ƙannen shi, wannan kuma ba wani abu bane a wurin shi, inaga jiya ne dana basu kuɗin liƙi sai M.G ya ƙara mata, shi a lokacin babu mint a jikin shi sai da muka bar wurin ya mun maganan na tuna mishi idan ya shigo ya bata nashi, nasan kuma shi nashi bugun girmane, ummie inaga babu komai rabonta ne",
"Tou kayi musu godiya dukkan su, kuma gaskiya kuɗin sunyi yawa tayi liƙi da su, ta ɗauki 20k kawai a ajiye sauran", murmushi yayah Ahmad yayi yace, "haba ummie shi da yabata 100k ae yana so yaga ƙanwar shi tayi fitan manya ne, idan bazaki bata duka ba tou a bata 50k, sai ki ajiye mata sauran, don naga hafsy umar da ishaq ke mata komai ko suma kamun ƙafa ne Allah ya sani" ya ƙarasa yana miƙewa, yana fita ummie ta dube ni, "saura ki bawa ƙawayenki da ƴan'uwanki labari, gama ke kanki baya saiti, ko hafsy kada naji labarin kin gaya mata, don magana ne da ita yanzu zata isar da shi", ummi nagama faɗa ta miƙe riƙe da envelope ɗin ta fita a ɗakin, nidai ajiyan zuciya na sauƙe na nemi wuri na zauna, ban daɗe ba saiga su fatima da hadiza sun shigo, hawa gadon kusa dani sukayi, hadiza ta miƙe kwance fatima kuma ta zauna a gefe na, "wurin habiba fah muka fito, tana ta tambayanki, mukace kina ciki, duk tayi wani iri da ita," inji hadiza, daga gefe kuma fatima tace, "duk haushinta da nakeji sai kuma ta bani tausayi, duk ta damu sai tambayanki takeyi, chan kuma sai hawaye yazo mata gashi ana mata make-up, da ƙyar ta tsayar da hawayen, shima sai da wannan ƴar yayar mamien sun tace zata haɗata da mamie tukun tayi shiru, ganin banzan kallon da ƴan'uwan da ƙawayenta kemana ne yasa muka fito", duk sai naji babu daɗi a zuciyata, tunani na komai yake damunta? Duk sai naji babu daɗi, tagumi nayi ina kallon su, sai ga hafsy ta shigo tana tambayana ina waya na? Yayah Ahmad yana ƙirana, da sauri na buɗe handbag ɗina na ciro wayan da na saka shi a silent, ina fitowa da shi ƙiranshi yana sake shigowa,, da wuri na ɗauka "Ayshaa kizo M.G nason ganinki, kiyi sauri fita zamuyi",
Ina gama jin abunda ya faɗa nayi sauri na miƙe don naje ƙiran.
*AUNTY NICE*
managarciya