An Tabka Babban Kuskure a Shirin Labarina Mai Dogon Zango

A rayuwa ba Mai kudin da zai walakanta kansa da zaman Tasha Yana daura Lodi don kawai ya samu macen da zai aura Mai sonsa da gaskiya.

An Tabka Babban Kuskure a Shirin Labarina Mai Dogon Zango

Shirin LABARINA  mai dogon zango da kamfanin shirin fim Saira  na Kannywood yake gabatarwa a kowane sati dan kokarin nishadantar da makallata wasan kwaikwayon Hausa na zamani, ya zo da wata siga mai cike da kuskure wadda za ta sanya tasirin shirin ya sake karyewa bayan wanda ya yi a farko da aka nuna shirin labari ne wasu ke  bayarwa ga wasu mahalarta taro, da yawan mutane suka jingine kallon domin lamarin ya zama labarin labari.

A wannan zangon kuma  da ya zo da labarin wani talaka da aure ke neman ya gagara saboda rashin kudinsa zaren labarin ya tafi daidai in da mahankalta dake bibiyar shirin suna tsammanin za a nishadantar da mutane ne kan su rika neman aure daidai da su, ma’ana kwarya tabi kwarya domin addininka bai koya maka ka nemi auren yarinyar da ta rayu sabanin yanda kake yin rayuwarka.

Hakinka kan matarka ka ciyarda ita irin abin da take ci a gidansu ka yi mata sutura irin suturar da take sanyawa a gidansu, rashin sanin hakki ne ka je neman wadda daukakar gidansu ta fi taku don kawai kana zaton za ka samu arziki, sai ka daura kanka saman tsammani a yi soyayya ta Allah bayan kai ba ta shin kake yi ba.

Wannan shirin na wannan satin ne Darakta Aminu Saira ya nuna ba kan wannan layin ya hau ba, yana son mata da wadanda za su aminta da tunaninsa su yarda a gina su saman rashin tabbas.

Darakta yana gab da nuna tauraron shirin Al'amen shahararren Mai kudi ne ya  shirya hakan ne don ya gane Mai sonsa da gaskiya da zai aura.

In haka ya tabbata tasirin shirin ya sake karyewa domin ba za a zo da wasan kwaikwayo ba, a yi abin da ba za a iya kwaikwayarsa ba.

A rayuwa ba Mai kudin da zai walakanta kansa da zaman Tasha Yana daura Lodi don kawai ya samu macen da zai aura Mai sonsa da gaskiya.

In Darakta ya zo da wannan ya rufe kansa kab don tasiri kuma sai a Wani shiri Mai dogon Zango ba wannan ba.