Jam’iyar APC a jihar Sakkwato ta bi sahun takwarorinta a jihohi 36 na Nijeriya in da ta gudanar da zaven fitar da ‘yan takarar Sanatoci da za su yi wa jam’iyar takara a babban zaven 2027.
Zavukan sun haxu da cikas na rashin halartar mutane da yawa, abin da aka danganta da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake fama da shi.
Wasu na ganin rage goyon baya da karkashin jam’iyyar ne ya sa hakan mutane ba su da yaƙini kanta don haka suke ƙauracewa taronsu ko da za su gyara.
Yankuna uku da aka zavo ‘yan takara da za su nemi takarar kujerar majalisar dattijan tarayyar Nijeriya sun haxa da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sakkwato ta Arewa da Sanata Ibrahim Xanbaba Sakkwato ta Kudu da Alhaji Umaru Ajiya Sakkwato ta Gabas an tabbatar da su ba wata hamayya.
Sani Abubakar shugaban mazaɓa xan siyasa ne daga qaramar hukumar Dange shuni a kalamansa ya ce shugabanni kawai ne aka gayyata a taron APC duk wanda ba shi da muƙami ya zo ne don kansa, “abin da ya sanya baka ga mutane da yawa ba, wasu suna nesa ne na yi magana da wasu suna kan hanya, ba mu da wata fargaba da ikon Allah za mu yi nasara,” a cewar Sani.
“Na gode Allah da ya bani wannan damar ta samu zaman xan takarar a wannan jam’iya, ina tabbatar muku abin da muka yi a baya za mu yi wanda ya fi shi na alheri, za mu xaura daga in da muka tsaya, zan tabbatar da lungu da saqo na na mazava ta sun amfana da aiyukkan cigaba, za mu cigaba da wannan hali na waqiltar mutane kamar yadda ya dace,” Kalaman sanata Ibrahim Xanbaba.
Alhaji Umar Ajiya ya ce yana fariciki ga wannan rana da aka tsayar da shi takara, “kun yi kira kuma na karvar kira, ‘ya ku ‘yan uwanan mutanen gabascin Sakkwato nasan kuna cikin wani qunci da yardar Allah wannan quncin zai tafi, mafiyawancinku ba ku barci da ido biyu, ba ku iya zuwa gona domin noma, ba ku iya zuwa kiyo, ba ku iya zuwa Kasuwa, ba ku zuwa Makaranta saboda makarantun sun koma wurin kwanan ‘yan gudun hijira za mu yi qoqarinmu don ganin samu sauqi,” kalaman Ajiya.
Masu sharhi a jihar Sakkwato suna ganin akwai ƙalubale gaban jam’iyyar APC a jiha in ba su sake sauyin yanda suke mu’amalar mutane ba za su iya shan mamaki ganin yanda mutane ke ƙwauracewa tarukkansu na siyasa.






