Home Siyasa An buƙaci kotu ta hana Tinubu yin takara a zaɓen 2027

An buƙaci kotu ta hana Tinubu yin takara a zaɓen 2027

54
0

Cibiyar inganta sauye-sauye da wayar da kan jama’a ta ‘Centre for Reform and Public Advocacy’ (CFRPA) ta shigar da kara babbar kotun tarayya da ke Kano, tana neman a hana shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 bisa zargin gabatar da takardun shaidar karatu na bogi.

A cewar takardun karar da jaridar Daily Trust ta gani, masu karar sun yi zargin cewa Tinubu ya gabatar wa hukumar zabe ta INEC takardar shaidar karatu ta bogi da aka ce ta fito daga jam’iar jihar Chicago da ke Amurka da kuma takardar shaidar kammala aikin yi wa kasa hidima NYSC da suke zargin ta bogi ce, a lokacin zaben 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here