Home Rahoto Akwai yiwuwar samun ruwa da tsawan a Sakkwato da wasu jihohin Arewa—NiMet

Akwai yiwuwar samun ruwa da tsawan a Sakkwato da wasu jihohin Arewa—NiMet

19
0

Hukumar Kula da Yanayi ta ƙasa, NiMet ta yi gargadin yiwuwar samun tsawa da ruwan sama ranar Jumu’a a wasu sassan jihohin Arewa.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar gargadin yanayi da Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa, NiMet ta fitar.

Sanarwar ta ce jihohin da zasu fuskaci tsawar sun hada da Sokoto, Zamfara, Katsina, Kano, Kaduna da Kebbi, yayin da ake sa ran ruwan sama zai bazu zuwa sassan wasu jihohin.

NiMet ta bukaci mazauna wuraren da ambaliyar ruwa ke yawan faruwa, wuraren da ke gangare da kuma wuraren da ba su da ingantattun hanyoyin ruwa su kasance cikin shiri.

Hukumar ta kuma bukaci masu ababen hawa su yi taka tsantsan yayin ruwan sama tare da guje wa hanyoyin da ruwa ke kwanciya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here