Home Siyasa Adadin waɗanda su ka yi rajistar zaɓe ya kusan kai miliyan 100...

Adadin waɗanda su ka yi rajistar zaɓe ya kusan kai miliyan 100 – INEC

20
0

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce adadin masu rajista a kundin zaɓe na ƙasa ya kusa kai wa miliyan 100, gabanin babban zaɓen 2027.

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa mutane 10,772,421 ne suka yi sabon rajistar zaɓe a yayin aikin Ci gaba da Rajistar Masu Zaɓe (CVR) da aka gudanar tsakanin watan Agustan 2025 zuwa Yulin 2026.

Ya ce sabbin rajistar za su ci gaba da tantancewa ta hanyar tsarin tantance bayanai.

Amupitan ya kuma sanar da shirin hukumar na ƙaddamar da wani tsarin bibiyar shirye-shiryen zaɓe kai tsaye (real-time), wanda zai taimaka wajen sa ido kan shirye-shiryen zaɓe a jihohi 36 da Abuja.

Tsarin zai bibiyi batutuwa da suka haɗa da rabon kayan zaɓe, ɗaukar ma’aikatan wucin gadi da horas da su, fasahar zaɓe da sauran shirye-shiryen gudanar da zaɓen.

Shugaban INEC ya ce hukumar na da kimanin watanni shida kafin babban zaɓen 2027, inda aka tsara zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa a ranar 16 ga Janairu 2027, yayin da zaɓen gwamnoni da majalisun jihohi zai gudana a 6 ga Fabrairu 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here