Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki KEDCO ta kai tallafin kayan abinci da kayan karatu a gidan yara wato (Nasarawa Cheldren Home) da ke unguwar Nasarawa da ke Kano a ranar Asabar wanda ya yi daidai da ranar yara ta duniya.
Da yake jawabinsa yayin miƙe kayan, Babban Manajan daraktan KEDCO, Alhaji Ahmed Dangana ya bayyana cewa maƙasudin zuwan shi ne sanya farin ciki da murna ga a zukatan yaran domin yawancin su ba su samu ni’imar da Allah ya bawa wadanda ba sa gidan ba,
Ya ƙara da cewa “Mun zaɓi ranar yau 27-5 2023 ne saboda ita ce ranar yara ta duniya domin mu ba su tallafi kuma mu yi hira da su, mu ji mene ne bukatunsu, sannan mu ga ta yaya za mu cigaba da taimaka masu daidai karfinmu”
Dangana ya kuma yi alkawarin samar masu da Mita, sannan yace ma’aikatansu za su riki yin karo-karo suna saya musu kati don inganta wutar lantarki a gidan.
Hajiya Aisha Sani Kurawa ita ce jami’ar kula da gidan, ta godewa KEDCO bisa namijin kokari da suka yi na kawo masu wannan tallafi, daga nan ya yi addu’a Allah ya saka da alheri.
Daga cikin kayayyakin da suka kai gidan sun hada: Shinkafa, Taliyar yan yara, Kayan karatu, Omo, sabulun wanki da na wanka, Tishu da sauransu.





