Home Siyasa Ba za mu janye wa Atiku takara a 2027–Kwankwaso

Ba za mu janye wa Atiku takara a 2027–Kwankwaso

7
0

Kwankwaso, wanda ke takara tare da Peter Obi, ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, inda ya zargi kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC da sukar su ta hanyar yaɗa jita-jitar cewa za su janye daga takarar.

Ya ce tikitin Obi da Kwankwaso ba ya aiki da APC, kuma babu wani dalili da zai sa su janye daga zaɓen shugaban ƙasa domin goyon bayan Atiku ko wani ɗan takara.

Tsohon gwamnan na Kano ya kuma zargi ADC da mayar da hankali kan sukar NDC maimakon gabatar da ƙwarewa da cancantar ɗan takararta ga ’yan Najeriya.

Kwankwaso ya buƙaci ADC ta mayar da hankali wajen amsa zarge-zargen da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi wa ɗan takararta, maimakon kai hari kan shi da Obi.

Ya kuma soki gwamnatin APC, yana mai cewa ta gaza wajen biyan buƙatun ’yan Najeriya, sannan ya ce ADC ba ta bayar da wata mafita mafi kyau ba.

Kwankwaso ya bayyana tikitin NDC a matsayin zaɓi mai inganci, wanda zai mayar da hankali kan haɗin kan ƙasa da magance matsalolin tsaro, ilimi, noma, ababen more rayuwa, lafiya da tattalin arziki.

Ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar da su ci gaba da aiki domin tabbatar da nasarar NDC a zaɓen 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here