Home Siyasa Kotu ta yi watsi da ƙarar da ake ƙalubalantar shugabancin ADC a...

Kotu ta yi watsi da ƙarar da ake ƙalubalantar shugabancin ADC a Sakkwato

14
0

Alƙalin babbar Kotun tarayya dake jihar Sakkwato ta yi watsi da ƙarar da aka shigar kan ƙalubalantar shugabancin jam’iyyar ADC a jihar Sakkwato.

Alƙalin Kotun Ahmad Muhammad  Gama ne ya ba da hukuncin a ranar Jumu’a domin masu ƙarar sun kasa gabatar da gamsasun hujjoji a gaban kotu na korafe-korafen da suka shigar.

Barista Suleiman Usman ne lauyan da yake kare shugabancin ADC a kotun ya yi bayani bayan kammala shari’ar ya ce kotu ta yi wa lamarin adalci bayan ta saurare kowane ɓangare.

Ya ce kotu ta yi watsi da dukkan ƙorafi huɗu da masu ƙarar suka gabatar domin sun kasa kawo hujja da za ta kare tuhumar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here