ADC ta zargi Gwamna Abba da hana ta kafa allunan yakin neman zabe a Kano
Wani jigo a jam’iyyar ADC, Salihu Tanko Yakasai, ya zargi Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da hana jam’iyyar kafa allunan yakin neman zabe a sassan jihar.
Yakasai ya yi zargin ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook da jaridar Daily Trust ta gani, inda ya ce gwamnatin jihar na takaita damar jam’iyyar wajen tallata harkokin siyasarta.
Ya bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tuna cewa mulki ba ya dawwama, yana mai cewa iko na Allah ne kuma Shi ke bayar da shi ga wanda Ya so.






