Home Siyasa Ka na Faransa shugaban ƙasar ya tafi UNGA amma kai ka tura...

Ka na Faransa shugaban ƙasar ya tafi UNGA amma kai ka tura wakili—ADC ta caccaki Tinubu

22
0

Jam’iyyar ADC ta soki Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, kan ci gaba da hutunsa a Faransa yayin da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya tafi birnin New York domin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA).

ADC ta bayyana lamarin a matsayin abin kunya ga ƙasa, tana cewa a daidai lokacin da shugabannin duniya ke fafutukar kare muradun ƙasashensu a Majalisar Ɗinkin Duniya, Tinubu yana ci gaba da hutunsa a Turai.

A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ya ce rashin ganin Tinubu a taron ya ƙara fito da tambayoyi, musamman ganin cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, shi ne ke wakiltarsa a wajen taron, karo na uku a jere.

Jam’iyyar ta kuma nuna damuwa kan cewa Tinubu da Shettima sun kasance a wajen Najeriya a lokaci guda, yayin da ƙasar ke fuskantar matsalolin tsaro, rashin aikin yi da tsadar rayuwa.

Abdullahi ya bukaci Fadar Shugaban Ƙasa da Majalisar Dokoki su bayyana wanda ke amfani da ikon kundin tsarin mulkin shugaban ƙasa a halin yanzu.

Ya yi nuni da sashe na 145 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, wanda ya tanadi cewa idan shugaban ƙasa zai yi hutu na tsawon lokaci, dole ne ya sanar da Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai a rubuce, domin mataimakinsa ya riƙe ragamar mulki.

ADC ta ce Tinubu ya bar Najeriya tun ranar 30 ga Agusta, kuma ya wuce kwanaki 21, don haka take neman bayani kan ko an yi sanarwar da kundin tsarin mulkin ya tanada.

Jam’iyyar ta kuma yi watsi da bayanin cewa Tinubu yana gudanar da “hutu mai alaƙa da aiki”, tana mai cewa wakiltar shugaban ƙasa a taruka ba ya bai wa wani jami’i ikon kundin tsarin mulkin shugaban ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here