Home Uncategorized ‘Yan bindiga sun kashe  mutane 12 da yin  garkuwa da 40 a...

‘Yan bindiga sun kashe  mutane 12 da yin  garkuwa da 40 a Sokoto 

15
0

 
‘Yan bindiga sama 200 ɗauke da miyagun makamai sun yi wa wata uwa da ɗanta yakan rago a ƙauyen Chaco, bayan sun kashe mutane 10 a ƙauyen Tofa sun yi garkuwa da mutane sama da 40 a ƙaramar hukumar Raɓah jihar Sakkwato.

Majiyar ta sanar da waƙilinmu ‘yan bindigar sun yi aika aikar ne a daren Lahadi ya ce ‘a jiya ‘yan ta’addan suka taru a gidan mai dake wajen garin Gandi daga nan suka tafi garin Tofa suka kashe mutane 10 suka tafi da mutane sun kai 40, a lokacin da suke dawowa suka ci karo da uwa da danta suka yi masu yakan rago a Chaco suka wuce abinsu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda baya kusa wakilinmu ya kira wayar bai dauka ba, har zuwa lokacin hada rahoton ba a samu magana da shi ba. 

“Ya cigaba da cewa ‘yan bindigan suna yanda suke so a yankin na Rabah ba tare da an dauki matakin da yakamata, akwai bukatar gwamnati ta yi wani abu kan halin da ake ciki a yankin da jihar Sakkwato baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here