Home Labarai Abin da ya biyo bayan mutuwar mutane 65 cikin ruwa a Sakkwato

Abin da ya biyo bayan mutuwar mutane 65 cikin ruwa a Sakkwato

24
0

 Jirgin ruwa ya nutse da mutane sama da 70 a garin Gorau cikin qaramar hukumarr Goronyo a Sakkwato, in da mafiyawansu mata ne da ke qoqarin tafiya gonakkinsu na shinkafa amma in da qaddara ta riga fata suka bar Duniya, a ziyarar da Aminiya ta kai a garin na Gorau an fahimci yanda ake  zaman makoki a garin lungu da saqo ganin yanda lamarin ya shafi kusan dukkan dangin garin mutum 65 suka rasu yayin da mutum 7 suka tsira, ciki har da maigari.

Alhaji lawali Gorau yana cikin waxanda suka rasa xiyansu mata a lamarin ya ce a tarihi ba su tava ganin irin wannan ibtila’i ba, “gaskiya mun yi rashi ba kaxan ba don ba mu tava gani ba, tun da aka haife mu sai wannan karon, a wannan dangi  muna da yarinya huxu duk mun rasa su akwai Hafsa Hali da Hasfa Hassan da Ramatu Lawali da Zara’u Iliyasu duka ‘yan mata ne.”

Ya ce suna cikin damuwa da alhini da rokon Allah ya ba su rahama, ba za su tava mancewa da wannan rashin ba mutum huxu a lokaci guda ba su zo lokaci xaya ba amma sun koma lokaci guda.

Aliyu Magaji Gorau uban qasa Gorau da ya tsallake rijiya da baya yana cikin waxanda suka tsira a kifewar jigin ruwan ya faxi yanda ya samu ya tsira a lamarin, “na shiga cikin jirgin mun kai tsakkiya jirgin ya xebo ruwa ya kife, akwa mutane da yawa ina tsammanin sun fi 70 za su kai 80 amma da ya kife ina ganin mu bakwai ne muka tsira.

“Waxanda suka nutse kwanannsu ne ya qare ba yanda za a yi a cikin jirgin ni kaxai ne babba bayan mutuqin jigin duka yara ne matasa, sadda ya nutse duk mutanen da ke jirgin ni suka zaburo suka riqe, bana iya kucce masu amma sai na samu dama na nutse suka qyale ni, dana sake tasowa suka riqe ni, sai na nutse na cire tufafi na sai suka riqe tufafin, ni kuma na samu wani buhun Tanka(barkono) sai na yi amfani da shi na tsira daga cikin ruwan, da na kawo ganga mutane suka fitar dani na fi awa xaya ban san mi ke faruwa ba kafin a xaura ni saman babur ya kai ni gida.”

“Bayan la’asar  ne muka koma aka tsamo mutum 48 da aka yi jana’iza su lokaci guda, sai aka cigaba da aikin ceton yanzu haka munada mutum 65 da aka yi jana’izarsu, anan ana cigaba da bincike har yanzu,” Kalaman mai gari kenan.

Alhaji Sani Dahiru shugaban qungiyar manoma masu amfani da madatsar ruwa ta Goronyo ya ba da shawara kan matakan da za a xauka domin kare faruwar hakan a gaba , “Gwamnati ne yakamata ta shigo lamarin domin yin tsari ga masu tuqa jirgin, kowane gari akwai sarkin ruwa wanda a qarqashinsu ne ake samun masu hiton mutane a jirgin ruwa a wani lokaci in manoma suka cika jirgi aka yi masa yawa ana iya samun matsala yakama a yi doka da wayar da kan mutane akan jirgin ruwa.” 

Gwamnatin Sakkwato ta jajantawa iyalan margayan 65 kuma ta ba su miliyan xaya ga kowane gida da buhun masara xaya da gero xaya da shinkafa buhu xaya.

Mataimakin Gwamnan Sakkwato Idris Muhammad Gobir ne ya jagoranci tawagar zuwa garin na Gorau, ya roqi gafarar Allah ga margayan.

Xan takarar gwamnan Sakkwato a jam’iyar ADC Manir Muhammad Xan’iya ya janjantwa mutanen in da ya tafi garin shi ma ya nemi da gwamnati ta yi bayani kan kuxi sama da biliyan xaya  da ta kashe kan sayo jiragen ruwa 20 da rigar ruwa 2000 domin rabawa ga mutane, akwai buqatar bayani domin abin da ya faru a Gorau ya nuna abin da gwamnati ta ce ta sayo ba ya hannun mutane domin amfani.

“Wannan ba maganar siyasa ba ce abu ne da ya shafi rayuwar mutane akwai buqatar a gabatar da bincike kan kwangilar da waxanda suka ci gajiya lamarin da in da aka kai jiragen da rigunan ruwan, in da har za a xauki kuxin mutane domin kare rayuwarsu suna da damar bincika in da abubwan suke domin kare rayuwa ga shiga cikin hatsari,” acewarsa.

A shekara data gabata hakan ya faru garin Kojiyo ta Goronyo in da mutum 50 suka rasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here