Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jihohi sun amince da ɗaukar matakan gaggawa domin rage kuɗin sufuri a faɗin Najeriya, da nufin tabbatar da cewa ’yan ƙasa sun fara cin gajiyar sauƙin kuɗin mota daga ranar 1 ga Oktoba, 2026.
Shirin zai mayar da hankali kan ƙara amfani da motocin da ke amfani da Gas ɗin CNG da kuma motocin lantarki, waɗanda kuɗin gudanar da su zai zama me sauƙi idan aka kwatanta da motocin da ke amfani da fetur.
Tinubu ya ce motocin da ke amfani da CNG na iya rage kashe kuɗin mai da kaso 60 zuwa 80 cikin 100 idan aka kwatanta da motocin da ke amfani da fetur.
Shugaban Ƙasar ya bayyana cewa an riga an sauya tsarin motocin sama da 120,000 domin su riƙa amfani da CNG, yayin da ake kuma kera ƙarin na’urorin sauya tsarin motoci sama da 100,000.
Haka kuma, ya bayar da umarnin ƙara gina tashoshin cika CNG guda 500, wanda zai kai yawan tashoshin da ake shirin samarwa a faɗin ƙasar zuwa 1,000.
Tinubu ya ce Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi za su kafa kwamitin haɗin gwiwa domin fara aiwatar da waɗannan matakai. Ya jaddada cewa sauƙin da za a samu wajen kashe kuɗin mai ya kamata ya haifar da raguwar kuɗin sufuri kai tsaye, musamman ga masu zirga-zirga a cikin jihohi.






