Home Labarai Yunwa ta sanya mutanen Nijeriya daina yinƙurin mallakar Gida ko mota—-Atiku

Yunwa ta sanya mutanen Nijeriya daina yinƙurin mallakar Gida ko mota—-Atiku

3
0

“‎Tsadar Rayuwa A Gwamnatin Tinubu Ta Tilasta Wa Ƴan Najeriya Watsi Da Shirinsu Na Sayen Gidaje Da Motoci Sai Fafutukar Abinci”, In Ji Atiku

‎Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce tsadar rayuwa ta sa ƴan Najeriya sun fara watsi da shirinsu na sayen gidaje, motoci da sauran kadarori.

‎Atiku ya yi nuni da wani binciken CBN da ya nuna raguwar ƙarfin saye, inda ya ce iyalai na kashe mafi yawan kuɗaɗensu wajen abinci, sufuri, wutar lantarki da sauran buƙatun yau da kullum, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.

‎Ya zargi gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da mayar da hankali kan alƙaluman tattalin arziƙi, alhali kuwa rayuwar talakawa na ƙara tsananta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here