Home Siyasa Buba Galadima ya faɗi Gwamna guda da ya raba ƙafa ko ya...

Buba Galadima ya faɗi Gwamna guda da ya raba ƙafa ko ya yi Tinubu ko adawa ya kasa matsaya

23
0

Gwamnoni 34 da rabi na goyon bayan Tinubu a 2027 – Buba Galadima

Wani jigo a jam’iyyar NDC, Buba Galadima, ya ce gwamnonin jihohi 34 da rabi na goyon bayan yunkurin Shugaba Bola Tinubu na neman wa’adin mulki na biyu a zaben 2027.

Galadima ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da kwamitin sasanta rikicin cikin gida na jam’iyyar NDC.

Ya ce Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, shi ne kadai gwamna da yake ganin a fili bai goyi bayan Tinubu ba, yayin da ya bayyana Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, a matsayin “rabin gwamna” saboda har yanzu bai yanke shawarar bangaren da zai mara wa baya ba.

A cewar Galadima, Mohammed ya gana da masu ruwa da tsaki na NDC da misalin karfe 3 na dare, inda aka tattauna yiwuwar hadin gwiwarsa da jam’iyyar.

Sai dai ya ce daga bisani Mohammed ya sanar da cewa ya sauya matsayinsa bayan an shawarce shi da kada ya shiga wata jam’iyya da ke da dan takarar shugaban kasa mai karfi.

“Saboda haka, Bala Mohammed yana kan shinge. Zai iya aiki tare da mu, ko kuma ya yi aiki tare da su. Shi ya sa na kira shi rabin gwamna,” in ji Galadima.

Galadima ya kuma ce jam’iyyar da ke kan mulki tana da damar amfani da karfin siyasar gwamnati wajen tabbatar da cewa ‘yan takara sun janye domin bai wa wani dan takara guda damar samun tikitin jam’iyyar.

Ya kara da cewa ‘yan adawa ba su da irin wannan damar ta rabon mukamai ko wasu abubuwan da za su jawo ‘yan siyasa zuwa wajensu, sai dai su dogara da kishin kasa da burin ceto Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here