RAUNIN RAYUWA
Na
Ruƙayya Ibrahim Lawal (Ummu Inteesar)
SADAUKARWA: Wannan shafin sadaukarwa ne ga masu nuna mini soyayya ta hanyar yin karar kasancewa tare da ni wurin karatun wannan labari. Allah ya ƙaro aminci a rayuwarku da yalwar arziƙi.
Page 3
Ci gaba ya yi da tafiya unguwa-unguwa yana sauke su ɗaya bayan ɗaya har sai da ya rage daga shi sai Halisa domin a cikinsu tafi kowa nisa saboda kalwaɗen (kewayen) da ake da ita. Ya rasa wace kalar rigima ce da ba za ta bi tawagar waɗanda hanyarsu take ɗaya ba. Tafiyarta idan ita kaɗai za a ɗauka wuri ne da yakamata ta biya ɗari huɗu saboda hidimar zagayen da ke ciki, ba ƙaramin mai nasiha ba ne zai iya sauke ta gun a ɗari biyu amma ga shi tana zancen talatin.
Bai tabbatar da gaske take yi ba sai da ya sauke ta ya ga ta miƙo masa cikin yanayin da ke nuna iya gaskiyarta kenan. Tsayawa ya yi yana kallonta cike da mamaki kafin ya gama yanke hukunci a zuciyarsa ya jiyo daga gefensa wani na faɗar “Apsara wutar kyau, kin yi taki kin yi ta yaro. Ya aka yi na ga kin tsaya?”
Ƙara kallon fuskarta ya yi yana gimtse dariyar da ke ciyo shi. Yanzu wannan abar ce ake yi wa kirari da kyakkyawa kuma take amsawa? Abin da mamaki a ce duk ƙwarewarta a sheɗanci ba ta fahimci cewa zolayarta ake da wannan sunan ba. A iya abin da ya iya hangowa a tare da ita, shi dai a iya ganin idonsa baƙa ce sosai irin baƙin nan mai sheƙi tana da manyan idanuwa da gajeren hanci mai faɗi, sai manyan laɓɓa masu kauri. Ba dai za a iya kiranta mummunan kai tsaye ba domin mace ‘yar gyara ce komai rashin kyaunta idan za ta gyara za ka gan ta ɗas, amma duk da haka dai ba za a saka ta a sahun kyawawa ba.
Yana nan ya shagala da karantar surar fuskarta ya jiyo tana faɗar “Wai kuɗina ne bai cika ba, talatin ce da ni shi kuma kuɗinsa hamsin ne.”
Kallon ta saurayin ya yi ya bushe da dariya kafin ya ce “Ba girmanki ba ne Apsara ya kamata ki biya cikon, kamar ke babbar yarinya a ce kuɗin ɗan sahu ɗin ma sai ciko ya biyo gyartai?”
“Ai kasan yadda lalurar take shegen bisa, gari ya ƙone fa.” Ta mayar masa tana buga kafaɗarsa da tafin hannunta.
“Don Allah bawan Allah tsahirta mini na karɓo chanji nan shagon na biya ka.” Ya nuna shagon da ke gefen hanyar kusa da su yana zaro ɗari biyar a aljihu ya fara takawa zuwa shagon.
Ba ta jira komai ba ta warce kuɗin tana kai masa duka a baya, “Shege Timaya nawa, ashe kana da kuɗi haka?”
Wanda ta kira da Timaya ya waigo yana hangame baki idonsa ƙur a kanta. Fara’ar fuskarta ba ta kau ba ta mayar da duban ta kan ɗansahun “Je ka abinka bawan Allah! Ai dama ka yi niyyar yafe mini. Me aka yi aka yi ashirin a gunka? Ai wallahi ka fi ƙarfinta yayana. To meye ma abin duniya wai sarkin fawa da kyautar ƙaho?”
Gyaɗa kai kawai ya yi yana murmushi ya buga abin hawansa cike da mamakin halayyarta ya ƙara gaba.
Yana jiyo ta cikin sautin nishaɗi tana faɗar “Na gode yayana Allah ya sa a cinikin yau ka mallaki kuɗin aure.”
Bai san lokacin da ya sake sakin wani murmushin ba ya ƙarawa abin hawansa sauri ita kuma ta juya ta mayar da akalar zancen ta ga Timaya.
“Timaya nawa. To ya ake ciki ne?”
Dariya ya yi ya ce “Wallahi komai zam-zam kamar dai yadda kike. Daga makaranta kike?”
Harara ta aika masa kafin ta amsa “A’a daga maƙabarta nake.”
“Habah Apsara tamu, daga tambaya sai baƙar magana?”
“To ai kai ne da wani zancen banza, ni fa na tsani irin tambayoyin nan na ‘yan Nigeria ga abu kuna gani muraran amma wai sai an tambaya.” Ta faɗa daidai lokacin da suka iso ƙofar gidansu.
“Ni zan shiga ciki sai mun jame.” Ba ta jira ya yi magana ba ta faɗa ciki faram-faram ba ko sallama sai ihun faɗar “Ige! Ige!! Abinci! Yunwa nake ji…”
“Ke!” Ta ji muryar da ta fi hardacewa da tsoro a duniya ta daka mata tsawa. Jikinta ya hau ɓari ta ƙame tare da kasa motsawa daga inda take har sai da ya yi mata umurnin ƙarasowa inda yake sa’annan ta je ta durƙusa a gabansa jikinta na ci gaba da tsuma kamar wacce ake kaɗawa gangi.
Tabbas da ta san ya zo gidan ba abin da zai sa ta shiga ciki da rawar kai sai dai rashin sani ya fi dare duhu.
ƁANGAREN FATIMA
Zaunawa ya yi yana ta saƙe-saƙe a ransa kamar ya bi bayanta kamar kuma hakan bai dace ba.
Ita kuwa Fatima tana isa uwar ɗakan ta zauna kan gefen gado da wayar a kunnenta.
“Wallahi lafiya lau muke inna, me kika gani ne?” Ta yi zancen tana ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi.
“A’a gaskiya ba lafiya ba Fatima, kada ki manta ni mahaifiyarki ce a iya murya ina iya fahimtar halin da kike ciki.” Innar ta mayar mata.
Gyara zamanta ta yi sosai kafin ta ce “Inna gaskiya na faɗa miki lafiya lau muke, ɓari dai na yi ɗazu da rana shi ya sa kika ji muryata a haka…”
Kafin ta ƙarasa innar ta tari numfashinta da faɗar ”Subhanallahi! Ɓari kuma? Shi ne kuma kika kasa kira ki sanar da ni tun ɗazun?”
“Abin ya zo da sauƙi ne, shi ya sa ma ban yi gaggawar sanarwa ba. Kuma yanzu da sauƙi sosai sai ɗan ciwon mara da baya da ba za a rasa ba.”
“Kai Subhanallahi! Wannan abu bai yi daɗi ba Allah ya ƙaro sauki, sannu Fatima. Yanzu wane mataki kuka ɗauka? Kun je asibiti kuwa?”
“A’a inna za dai mu je in sha Allahu”
“Gaskiya ya kamata yi hanzarin zuwa a yi miki wankin ciki, sannan ya kamata a yi kyakkyawan bincike a kan matsalar da ke haifar miki da yawan zubewar ciki, abin nan ya fara ba ni tsoro. Wannan fa shi ne karo na biyar a cikin shekara huɗu.”
Shiru ta ɗan yi na wani lokaci tare da jan numfashi a hankali ta sauke. A yanzu ita ta san gaskiyar da ba wanda ya sani a cikin wannan al’amari, sai dai ba za ta iya faɗawa mahaifiyarta batun ba ko don gudun ta ɗaga mata hankali. Abin da dai ta sani ba shakka za ta yi duk mai yiwuwa don ta kare kanta da ɗan cikinta nan gaba.
“Kin yi shiru ina ta magana, Fatima lafiya dai?”
Ta yi firgigit ta ce “Uhm! Na’am! Lafiya lau inna ki kwantar da hankali da ma na kira ne in ji lafiyarki kuma na sanar da ke wannan don ki yi mini addu’a. Ki ƙara tsananta addu’a Allah ya yi mini maganin matsalar da take janyo mini wannan zubar cikin.”
Da wannan zancen suka yi sallama da innarta bayan ta kwararo mata addu’o’in samun sauƙi.
Tana sauke wayar daga kunnenta wani kiran ya sake shigowa da dai wannan baƙuwar lambar, da ma tun tana waya take jin shigowar kira har dubawa ta yi, ganin ba ta san number ba ya sa ta share.
Da kamar ba za ta ɗaga wayar ba tun da ta ga ba layin ta ba ne ake kira, amma sai zuciyarta ta kwaɗaita mata ɗagawar ai kuwa kafin kiran ya katse ta ɗaga ta ɗora a kunnenta.
“Hello Beb!” Ta ji an faɗa daga wancan ɓangaren, mamaki ya saka ta sauke wayar daga kunne ta ƙurawa lambar ido kafin ta mayar saitin kunnenta.
“Hello Beb! Kana kan layi kuwa?”
Wani bambarakwai ta ji wai namiji da suna Hajara, ta yi murmushin takaici kafin ta ce “Yi haƙuri Beb ɗin naki ba ya kusa.”
Da fusatacciyar murya ta ji an ce “Ke wace jakar ce a cikin jakunan da har za ki ɗaga wayar babyna?”
“Babynah!” Fatima ta maimaita sunan a ƙasan maƙoshinta, kafin ta yi wani furuci ta sake jiyo an ce “Da ke fa nake magana, wace ke?”
Ba ta so tamkawa ba sai dai ta kasa jurewa saboda wani mashin kishi da ya soki zuciyarta har sai da ta ce “Af! Ashe jakunan kuna da yawa kenan shi ya sa kike tambayar wace daga ciki? To ni ɗin matarsa ce kin ga ko na fi ƙarfin wannan sunan.”
“Matarsa!?” Budurwar ta maimaita da ƙarfi cikin alamun kaɗuwa.
Fatima ba ta san lokacin da ya shigo ɗakin ba kawai ta ga dirowarsa a gaban ta yana miƙa mata hannu yana huci da zare ido.
“Miƙo mini wayata!” Ya daka mata tsawar da ta razana ta, sai dai duk da hakan wayar na hannunta ta saita sifikar daidai bakinta yadda budurwar za ta ji zancen da kyau.
“Ƙwarai kuwa matarsa ta sunna. Kodayake ba amfanin tsayawa yi wa dabba irinki wannan bayanin don ba ki san ƙima da darajar aure ba sai dai darajar gantali da watsewa…”
Kafin ta gama rufe bakinta ta jiyo saukar kyakkyawan mari a kuncinta na dama har sai da kan nata ya sunkuya ba tare da ta sani ba. Ya wafce wayar ya kashe ta gabaɗaya dai-dai lokacin da ta ɗago idanuwanta tana kallon shi. Wannan karon ba kallon mamakin da ya saba gani a idanunta ba ne, kallo ne mai cike da ma’anoni da fassararsa kai tsaye zai yi wuya.
“Ni ka mara a kan wata jaka Musa?” Ta faɗa tana dafe kuncinta tare da neman wuri ta zauna daɓas baki a sake ta kasa ɗauke idonta a kansa.
“Musa!” Ya maimaita. A iya tsawon zamansu tun lokacin samartaka kawo yanzu bai tuna tsawon lokacin da ya ɗauka kafin ya ji wannan sunan daga bakinta ba, duk irin wulaƙanci da cin kashin da yake yi mata ba ta iya faɗar sunansa. Shi ya sa yanzu da ya ji ta faɗa ya girgiza sai dai bai nuna mata hakan ba ko a fuska ya dai ba ta amsa da faɗar “An mare kin, idan kika ƙara kuskuren ɗaga mini waya abin da ya fi wannan zan miki Fati.”
Ba ta sake cewa komai ba sai goge hawayen idonta da ta yi da bayan tafin hannunta ta yi fuu ta shige ta gefensa, har saboda ƙarfin wucewar tata sai da ta ture shi ba tare da lura ba ta fice abinta tana ci gaba da sharar hawaye.
Ta sha jin labarai mabambanta a kan cewa wasu daga cikin maza suna yaudarar matansu na sunna ta hanyar tara matan banza a waje, sai dai ko a duniyar mafarkinta ba ta taɓa hasaso cewa Musa zai iya cin amanar soyayyarsu ko ya rufe idanunsa ya cutar da ita ba sai yau da ya wanke ta da tafi a kan budurwarsa wannan shi ake kira kala ji har gani.
Ta zo cikin ƙunci za ta wuce ta falo ta taka farantin naman da ya ajiye mata, naman ya watse a ƙasa farantin ya tsage. Ba ta damu da hakan ba don kallo ɗaya ta yi wa gun ta ɗauke kai tare da jan malalacin tsaki ta wuce kai tsaye zuwa kitchen ta saka sakata ta ciki. A kan tiles ta zube tana ta rusa kuka mai cin zuciya, wani irin ƙullutun baƙinciki yake tasowa daga ƙasan maƙoshinta ya tokare mata tsakiyar shi, abubuwa da yawa ne suka shiga dawo mata, ta jinginar da kanta a jikin bango sautin kukanta na raguwa. A take igiyar tunani ta yi mata dabaibayi zuwa tunanin baya. A shekarar 2015 watarana a cikin ranakun ‘yanmatancinta.
Ranar wata Laraba ana saura kwana biyar a yi ƙaramar Sallah Musa ya dira garinsu da yamma lis. A lokacin tana zaune a makarantar allonsu kusa da malama tana jiran layi ya zo kanta a yi mata bitar nata karatun, wayar da ke jikinta ta fara vibrating. Da hanzari ta ciro wayar daga jakar soson da ke kan cinyarta ta miƙar da jakar don kada malama ta ankara da wayar.
Everlasting sunan da ya bayyana kenan a jikin screen ɗin ƙaramar itel da ke hannunta. Murmushi ya ƙwace mata ta miƙe cikin shauƙi ta zame jikinta don ganin hankalin malamar ba ya kanta ta yi waje a ƙofar gidan ta samu wani loko ta maƙe a ciki. Daidai lokacin kira na biyu ya shigo da hanzari ta ɗaga da fara’arta.
“Yayana!” Ta faɗa cikin shauƙi.
Murmushi ya yi wanda take iya jiyo sautinsa kafin ya ce “Albishirinki Sweetie.”
“Goro” ta faɗa tana washe haƙora.
“Wane kalar goro?” Ya sake tambaya cikin raha. Sai da ta yi fari da ido kafin ta ce “Um! Fari kuma ƙwalelen gaske.”
Yar dariya ya yi kafin ya ce “Ga ni a garinku fa.” Jirkitar da idanunta ta yi tana ɗan lanƙwasa kanta cikin fara’a ta ce “Haba dai!” Yadda ta ja sautin da yanayin da ta furta shi ya sa ya fahimci cewa kamar dai ba ta yarda da zancen shi ba tana ɗauka kamar wasa yake yi.
Faɗaɗa fara’arsa ya yi ya ce “Da gaske fa nake shigowa ta kenan, ruwa kawai na watsa na ce bari na kira ki na sanar miki ga ni nan zuwa gida, kin san dai ba zan iya ƙara mintuna 30 a garin nan ba tare da na saka ki a ƙwayar idona ba.”
Sosai ta yi murmushi cikin alamun jin kunya ta ce “Uhmm! Ashe haka ne?”
“Ke ma ai kin san saboda ke kaɗai nake share doguwar tazara na zo nan.”
“Kamar a kunnen yayanmu wallahi. Sai ka zo.” Tana gama faɗa ta yi wuf ta kashe wayar ta rungume a ƙirjinta ta rufe ido, har a lokacin murmushin fuskarta bai kau ba, ta mayar da mintuna biyu tsaye a gun daɗi yana ratsa ta kafin ta buɗe idanunta ta fara takawa da sauri tana neman sulalewa daga makarantar. Duk da cewa a kowanne azumi akan yi hutun duka makarantun addini amma su malamarsu ta zaɓi ta ci gaba da yin wannan aikin alherin a cikin wata mai falala. Sai dai ba tsaurarawa, idan mutum bai samu zuwa ba ma duk ba matsala takan yi masu uzuri saboda ibadar azumi da ake.
Ba ta fi yin tafiyar minti bakwai ba ta isa gida, jakar littafanta kawai ta sauke a ƙofar ɗaki ta zura hannu ta sakaɗa jakar gefen bangon ɗakin na ciki.
Surar ƙaramin bokitin roba ta yi ta nufi wurin ajiyayyun kayan ruwa ta fara buɗe-buɗe. Ganin ko’ina ba ruwa sai a randa da tulu ya sa ta yi tsaye sororo na ‘yan sakanni.
Duk da tana tsoron sakawa jikinta ruwa amma sanin waye zai zo sai ta ji kamar ko da ruwan ƙanƙara za ta iya wanka tsabar jarumta don haka ba dogon nazari kan abin da zai je ya dawo ta kwarfi ruwan randar ta yi shahadar ƙuda ta afka banɗaki don ta tsala wanka.
Sai dai duk zuba wa ɗaya da za ta yi wa ruwan a jikinta sai ta callara ƙara saboda yadda sanyin ruwan ke ratsa jikinta sosai, amma a haka ta dage sai ta ga abin da zai ture naɗin Buzu.
Daidai lokacin da ta challa kara ta uku Inna ta shigo ƙofar, jiyo ihun ya saka ta ƙara hanzari tana tunkarar inda ta jiyo sautin. A ƙofar banɗakin ta tsaya tana tambayar “Waye ne a ciki? Me ya faru kike ƙara?”
Tana so ta ba wa innar amsa sai dai ba halin yin hakan saboda innar ta hane su da yin magana a cikin banɗaki a cewarta mummunar ɗabi’a ce da ka iya janyo haukacewa.
“Hauwa’u ce?” Ta sake wurga tambaya ta ji tsit.
“Fatima ce kenan?” Wannan karon sai ta yi alama ta hanyar fitar da sautin “Ehem- Ehem” da bakinta.
Tun daga nan ba ta sake jiyo motsin innar ba har ta fito daga wankan ɗaure da zanin atamfar roba, wata sassanyar iskar hunturu ta ratsa ta. Nan take ta yi wata iriyar cira laɓɓanta suna rawa, da gudu ta faɗa ɗaki ta yayibo bargo ta shige ciki jikinta na ci gaba da ɓari.
“Wanda bai ji bari ba, ai ya ji hoho. Yanzu ke fisabilillahi me ya haɗa da wankan yamma? Wankan ma kuma ki rasa da me za ki yi sai da ruwan sanyi ƙarara kuma kina sane da matsalarki?” Ba ta iya yin magana ba har lokacin sai innar ce ta sake cewa “Yaushe ma kika dawo daga makarantar? Na ga lokacin tashinku bai yi ba.”
“Yayana ne zai zo, shi ya sa na gudo daga makarantar.”
Kallon inda take dunƙule innar ta yi haɗe da yin ‘yar dariya. “Uhm! Koda na ji, shi da ma ai ruwa ba ya tsami banza. Allah ya kawo shi lafiya.”
Sai da ta kwashe mintuna goma dunƙule a gun kafin ta samu sassaucin yanayin da take ji ta yaye bargon ta fito ta zaɓo kaya na ƙasan akwati ta sanya sai dai ba ta yi kwalliya ba da ma can ba ɗabi’arta ba ce. Sai can misalin ƙarfe shida ya diro ƙofar gidan, da yaya I.b ya fara cin karo (ɗan yayan babanta). Shi ne ya yi masa iso har cikin ɗakin innan, bayan sun gaisa inna da I.b suka fice suka bar musu ɗakin.
Kallonta ya yi cikin kulawa ya ce “Na yi kewarki Sweetie, shi ne na ga gara dai na zo na ganki kar ƙwaƙwalwata ta fashe don tunaninki.”
Murmushin da ke ƙara jan ra’ayinsa kawai ta yi ba ta ce komai ba face “Ni ma haka yayana.”
Haka ya zauna ya ci gaba da zuba mata kalaman da suke ƙara saye zuciyarta amma ita kunya ta hana ta haɗa ido da shi ballantana ta fitar masa da abubuwan da take ji a ranta game da shi.
Da zai tafi ya turo mata ƙaramin akwatin da ya shigo da shi ya ce “Sweetiena wannan kayan sallarki ne.” Da murnarta ta ɗago kai ta kalle shi idanunta na aika masa saƙon da bakinta ya kasa furtawa. “Wow! Amma na gode sosai yayana, Allah ya bar mu tare har mutuwa.”
Ba ta yi yunƙurin buɗe akwatin ba sai da ya ce mata ki buɗe ki gani mana, daga nan sai ki kira Inna mu yi sallama ni zan koma tun da na ganki mun gaisa, kar asha mini ruwa a hanya. Kin ga kuma yaya ma fa bai san na ƙaraso ba.”
Ba musu ta fara buɗe akwatin a daidai lokacin da take yi masa tayin ya tsaya ya sha ruwa a gidan amma ya ƙi.
Tana kammalawa buɗe shi idon ta ya gane mata tsala-tsalan atamfa ɗinkakku guda biyu sai shaddar da ta ji aiki da lace ɗaya su ma duka a ɗinke suke ga kayan sarka, takalmi mayafi har da kayan shafa a ‘yar wata leda. Gigitaccen ihun murna ta sake ta yi waje da gudu zuwa cikin family house ɗin nasu tana kiran “Inna! Innarmu zo ki ga kayana!”
Murmushi ya sake shi kaɗai a zaune har ga Allah halin ƙuruciya da take nunawa yana burge shi.
Daidai lokacin ƙanwarta Hauwa ta shigo babbar ƙofar gidan da nufin wucewa kai tsaye zuwa ƙofar innarsu sai dai ganin ‘yar’uwarta a cikin halin murna ya sa ta rungume ta suna yi tare da tambayar ba’asi. Ita ma da ta ji ta taya ta murna sosai har ta ga ba za ta iya tsaya Innan ba ta tafi da hanzari don ganin kayan.
Bayan tafiyarsa kowa a gidan ya yi mamakin ganin irin kayan da ya kawo wanda a kallo ɗaya za a san ya kashe kuɗi masu rai. Don kuwa abin ƙwarai shi ke nuna kansa.
A ranar ta fara gano ‘yan hassadar gidansu da masu taya ta murna ta yi dacen mijin aure, wasu kuma suna faɗar duk sun ga irin waɗannan mazan, wuyar ta dai a yi auren su fara gasa yarinya wane dare ne jemage bai gani ba?
Tana zuwa daidai nan a gaɓar tunaninta ta ja dogon numfashi ta sauke “Me ya sa ban yi imani da waɗancan maganganun ba a lokutan baya?” Ta furta a hankali.
Sallama ya jiyo daga ƙofar falo wanda hakan ya tilas ta masa katse wayar da yake yi ya nufo ƙofar yana tambayar “Waye ne?”
Kafin ta kai ga amsawa ya ƙarawa fuskarsa fara’a, a’ah! Yaya yau ke ce a gidan da daren nan?”
“Eh wallahi Musa ga ni dai. Na zo barka ne nan unguwar a can ƙasanku, to da ke na yi biye-biye ne shi ya sa dare ya yi mun. Sai kuma na ga ba zan iya wucewa ban leƙo ku ba, na ce bari na duba ko ba ku yi bacci ba.”
“Ah! Wallahi kin kyauta yaya, shigo ciki don Allah.” Ya matsa mata hanya ta shige ɗakin da sallamar ta.
“Sannu yaya, ya wajen su Mari da Rufa’i? Fatan duk suna lafiya.” Ya faɗa yana ƙoƙarin zama kan carpet ita kuma tana daidaita zamanta kan kujer mai cin mutum ɗaya.
Da murmushi a fuskarta ta ce “Alhamdullillah! Duk suna lafiya. Ni kam ina matar gidan ne ban ji motsin ta ba.”
“Uhm! Ina ga ko tana banɗakin tsakar gida bari na dubo ta.” Ya faɗa yana yaƙe ya miƙe ya fice. Shi kansa bai san inda ta maƙale ba tun lokacin da ta ture shi ta fice bai kuma bi ta kanta ba ballantana ya san ya ta ƙare saboda ta gama ɓata masa rai.
Shi ne kawai ya fito falo ya zauna yana laluben number Khady baby don ya ba ta haƙuri kan abin da ya faru, yana cikin aikin rarrashin ne ya jiyo sallamar.
Ba inda bai duba ba a tsakar gidan amma bai gan ta ba ga ƙarar injin da ta cika tsakar gidan ta taka rawa wurin hana shi jiyo sautin kukanta. Kitchen ya nufa ya hango ƙofar rufe hakan ya ba shi tabbacin tana ciki ya fara bubbuga ƙofar yana kiran sunanta.
“Fatima! Fatima ki buɗe!!” Ya ji shiru sai da ya ɗan nutsu ya jiyo sautin shesshekarta.
Ita kuwa Fatima tana jiyo bugun ƙofarsa ta zabura ta miƙe tsaye tana maƙewa jikin cabinet na kitchen ɗin shessheƙarta na ƙaruwa ta tsorata da jin bugun ƙofar. ‘To da me ya zo?’ Ta tambaya a ranta. Nan da nan numfashinta ya fara yi sama da ƙasa tana janyo shi…
Ummu Inteesar ce





