Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 26

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 26

2
0

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 26

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 26📑

__📖 “Amaal me kike nufi da wannan irin ihun da kikayi? sai kace wani mummunan abu kika samu munayi”? Faisal ya faɗa kaman mai shirin kai mata duka, hankali a tashe Amaal ta dube shi tace, “abu mara kyau kake aikatawa mana bros, saboda Allah Hummy fah amanace a wurin mu, amma duk kabi kana son chanja mata rayuwa, haba bros ka daina abinda kakeyi mana, ba halinka bane fah”, ta faɗa idon ta ya ciko da ƙwallah.

Jan ƙafana nayi a hankali na ƙarasa gabanta, duk hankalina a tashe domin tunda na kashe waya Dr yake ta ƙirana amma tsoro ya hanani ɗauka, hannu na saka na riƙo na Amaal murya a hankali nace.

“Amaal ba laifin shi bane, laifi nane dana barshi yake zuwa inda nake, kuma bana son na ɓata mishi raine saboda danganta kar ku da shi, amma ki sani bazan taɓa juyawa Dr baya ba, ae soyayyan Dr bata da abokin haɗi a wurina, don Allah kiyi haƙuri kuma bana son maganan nan yaje wurin su Ummi, ya tsaya a tsakanin mu insha Allahu zamu magance komai haka bazai sake faruwa ba”,…..na faɗa nima hawaye yana zuba mun don ganin yadda hankalin Amaal ya tashi.

“Hummy na yadda akwai laifinki, amma gaba ɗaya laifin nawa ne dana taho da ke ƙasan mu, yanzu idan wani abu ya faru me zamu ce da Daddyn ki saboda Allah? don Allah Hummy ki kiyaye bana son wani abu ya faru da rayuwar ki ko kaɗan”.

Rungumeta nayi inajin wani irin rashin jin daɗi a zuciyata, domin ko babu komai nasan Amaal ta damu da rayuwata, kuma bata son wani mummunan abu ya faru da ni.

Mtsss…. Faisal yaja tsaki yabi ta gefen mu ya fita a ɗakin, ɗago da kaina nayi na dubi hanyar daya fita, sannan na dawo da kaina kan Amaal, fuskana cike da damuwa nace, “Amaal bana so ta dalili na ku samu saɓani da ɗan’uwanki, domin nasan irin son da kuke yiwa junan ku, bana so ta dalili na kuka sa samun fahimta, ni kawai naji ma zan koma school”, na faɗa ina juyawa zuwa kan bed ɗin.

Takowa Amaal tayi tazo ta zauna a kusa dani tana dubana da damuwa ɗauke a fuskanta, “Hummy don Allah kada ki bari faisal ya ɓata mana jin daɗin hutun mu, don wallahi kikace zaki tafi toh nima binki zanyi mu tafi tare, ni in banda neman fitina ma, sainan da 5dys fa ya dawo, amma narasa wani fitinan ne ya dawo dashi daga kammala exams ɗin shi, yawanci yana ƙara wasu kwanaki kafin ya dawo, amma ji don ya zo ya ɓata mana hutun mu sai ya dawo, ni banji daɗi ba, kema hummy ki daina sake mishi fuska, kuma gashi Dr yana ta ƙiranki bakiyi picking call ɗin ba, har ya fara ƙiran nawa, toh yanzu me zamuce mishi bayan yaji ihuna hala”.

Cikin damuwa nace, “Amaal toh kisan dabaran da zakiyi kada ya fahimci wani abu don Allah”, na faɗa ina zaro ido tsabar fargaba.

Ɗaukan wayan Amaal tayi, bayan ta amsa mishi sallaman shi naji tana ce mishi, “wallahi na buɗe ƙofa zan shigo kawai na tafi zan faɗi ban sani ba, shiyasa na yi ihu, ina ga anyi mopping wurin bai gogu da kyau ba, kaman da sauran santsin ruwa a wurin, ita kuma hummy sai ta razana ita da Bros Faisal da yake bina a baya, amma ba komai banji ciwo ba kawai naji tsorone”, ta faɗa tana maida abun dariya.

A jiyan zuciya na sauƙe, ina dubanta fuskana cike da jin daɗin taimakon da tayi mun a wurin Dr.

Miƙo mun wayan tayi tana dariya, da sauri na amshi wayan na kai kunne na, ina karɓa naji dariyan Dr yana cewa, “haba baby gaba ɗaya kin ɗaga mun hankali, na ɗauka wani mummunan abu ya same ki ne? Da wallahi saidai na taho babu shiri, don ko takalmi bana sakawa sai nazo naga halin da kike”, ya faɗa yana ajiyan zuciyaa, nima ajiyan zuciyan nayi sannan na ƙara ninka wani ƙaryan da cewa, “na ɗauka fa Amaal zata faɗi taji ciwo ne, shiyasa naji tsoro sosai, toh Allah ma kiyaye Faisal yana binta a baya shi ya riƙeta bata faɗi ba”.

“Gaskiya baby nikan bana son irin wannan tsarin, ta yayah za’ayi ƙato da shi yana shigowa bedroom ɗinku? Gaskiya banji daɗiba don zai dinga kalle mun mata”, ya faɗa ranshi a matuƙar ɓace.

“Baby kasan fa ɗakin sister shi ne, ni ban isa ina baƙuwa na hana shi shigaba”, na faɗa ina ƙasa da murya na.

“Baby shima ba escuse bane, ae ɗakin sister nashi yanzu kina ciki, ke yakamata ya dinga shigo miki anyhow ne? ae ko a musulunci ɗakin ita Amaal ɗinma bai kamata ya dinga shigowa yadda ya mishi ba, shiyasa fitinu suka yi yawa a duniyar mun ta yanzu, rape yayi yawa tsakanin ɗan’uwa da ƴar’uwa, ko kuma tsakanin uba da ƴa, nidai bana son jin yana shigowa, don yau ɗaya kinsa naji hankali na yayi matuƙar tashi, kinsa wasu abu da suka wuce shekaru da yawa sun fara dawo mun cikin zuciyata, baby yanzu muna wani irin rayuwa da rape a gida ɗaya yafi faruwa, don Allah ki kula mun da kanki idan wani abu ya faru da ke, wallahi zuciyata zata fashe, don yanzu bazan sake iya ɗaukan abinda ya faru dani a baya ba, wallahi yanzu kam saidai na rasa rayuwa ta bawai nayi nesa da mutane ba, ina kuma zan sake tafiya”? Ya faɗa daga ji hawaye ne yake zuba mishi.

“Wayyo baby wani abu ya taɓa faruwa da kai ne irin haka a baya? Don Allah baby kaban tarihin rayuwar ka, don Allah ka gaya mun wani abu kaɗan akan su Ummin ka da ƴan’uwanka, nima inaji a zuciyata zan iya taimaka ma koda da abu kaɗan ne domin hankalinka ya kwanta”.

Kashe wayan yayi, daga inda yake kuma ya fashe da kuka kaman ba Dr ba, muryah a raunane ya furta, “Baby na damu da ke, bana son wani abu ya faru da rayuwar ki, ni dama ban amince kin tafi ba, inajin tsoron larabawan nan, domin Sunfi kowanne irin mazan duniya fitina akan mace, gashi ya ga irin ki mai wuyan samu, wayyo Allah ka tsare mun rayuwar future wife ɗina, Allah uwar ƴaƴanane ka tsare mun ita”, ya ƙarasa yana kuka mai zafi, ya juyar da kanshi gefe ya furta a fili, “wayyo Ummi nah, wayyo Abba nah, ko ina ɗan’uwana Hassan da ƴar’uwata Aisha suke? Ko a wani irin ƙuncin rayuwa suke bayan bana nan? Don nasan abinda ya faru da familyn mu, duk zafin da sukaji zasi sake faɗawa wani yanayi bayan kuma sun tashi rana ɗaya sunga bana cikin su, gashi basu san inda nake ba a raye ko amace, wayyo Allah Aunty Hauwa na ko ina ta ke? Ina kakarmu? Gaskiya ina mssn ahalina, dama na yadda da ƙaddara na zauna da su, nasan da yanzu abun ya bar zuciyata, don nasan yanzu sukan sun samu sauƙi akan ni dana kasa mance komai, saboda nayi nesa da duk wani wanda zai kwantar mun da hankali, gashi zasuji tsoron nema na, saboda irin abunda na bar musu na kada su neme ni bayan sun tarar nayi nesa da su, Allah sarki ɗan’uwa na Hassan ko yayi aure? Ko ya tara iyali”? Sai kuma yayi murmushi shi ɗayan shi domin tona da Hassan idan yayi wanka yana wani taku, Ummi zatace “sai kuma wurin surkuwata ko twin”? Dariya ya keyi yace “haba Ummi gaye da ni wani batun surikuwa kuma, ae sai na cika 30yrs Ummi nah, kedai kimun fata na samu mai kyau da haɗuwa wanda tafi ƴar ki mummunan nan” zai faɗa yana nuna Aisha tsabar neman tsokana, ita kuma bata jiran komai sai ta fashe da kuka domin ta tsani ka dangantata da muni, domin Aisha ji ta keyi duk duniya babu sauran macen da tafita kyau, sai Ummi ta kwantar mata da hankali tace, “kada ki damu ƴata shima bai isa ya ƙira ki da mummuna ba, don kowa nima zai iya ƙirana da mummuna, kuma duk matar da dukkan su zasu aura ƙarya ne su samu wacce ta kaiki ballantana wacce ta fiki, sai dai ƙasa da ke auta na”, a haka Ummi ta ke kashe rikicin.

Nidai bana ce musu komai sai dai nayita murmushi, domin babu yadda za’ayi a zauna wuri ɗaya Aisha da Hassan basu yi faɗa ba, kuma kullum sai ya saka ta kuka, saidai a barni ko Ummi da aikin lallashi, idan Aunty Hauwa tana nan kuwa ta dinga goyon bayan Hassan kenan, akan sai ya auri wacce tafi Aisha komai da komai, shi yasa Aisha bata cika zuwa kusa da Aunty Hauwa ba, yanzu zakaji kukanta, domin Aunty Hauwa idan ta ga daman saka Aisha kuka sai dai kaji tace mata CINCIN BREADI wai girman jikin Aishan, shi kuma Hassan ya samu abin dariya kenan har sai Aisha tayi kuka faɗan ya ke lafawa.

NI AUNTY NICE SHA RE HAWAYE NA NAYI DON GANIN YADDA DR YAKE SHA RE HAWAYE KUMA YANA SMILLING, GA DUKKAN ALAMU YANA MSSN ƳAN GIDAN SU SOSAI.

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE
@wattpad AuntyNice.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here