Home Rahoto Ko ƙaddamar da Kasuwar kayan Gwari zai samar da walwalarsu a Kebbi

Ko ƙaddamar da Kasuwar kayan Gwari zai samar da walwalarsu a Kebbi

11
0

Gwamnan Kebbi Dakta Nasir Idris ya kaddamar da sabuwar kasuwar kayan gwari a wani bangare na alkawalin da ya yi wa mutanen yankin.A lokacin bukin kaddamar da kasuwar Gwamnan ya tuna halin da ya samu kasuwar a lokacin da ake sake ginata tana a kware ba wurin mai fadi da ake iya gudanar da kasuwanci.

Ya bayyana cewa dalilin sake gina kasuwar ya faru ne kan kiraye-kiranye da ‘yan kasuwar suka rinka yi ga gwamnati ta shigo ciki don samar musu da yanayi mai kyau a harkar kasuwanci.

Gwamna Idris ya ce sabuwar kasuwar an gina ta ne domin ta kara inganta rayuwar ‘yan kasuwa musaman masu harkar kayan miya da sauran kayan abinci, kan samun wuri zagaye da za ka iya aje kayan kasuwancinka ba tare da wata tsangwama ba.

Ya matsa aikin zai taimaka wurin bunkasa tattalin arziki da zai shafi mutane masu kramin karfi a jiha, ya godewa Allah da ya ba shi kwarin guiwar kammala aikin aka bude domin amfanin jama’a.

A kalaman shugaban masu kayan Gwari Ummaru Basiru ya bayyanna gidiyarsa ga Gwamnan kan cika alkawalin da ya yi.”Wannan cigaba ne da zai bunkasa kasuwanci”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here