Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 25

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 25

10
0

°ƘADDARA TA RIGA FATA°

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 25📑

__📖 “me kake so kaji? Bayan kasan kai ɗin yaya nane, akwai abinda ya fi shi girma ne a wurina”? na faɗa bayan na xare hannu na daga na shi ina binshi da kyakkyawan murmushi a fuskana.

Juyar da kanshi yayi alaman yayi fushi, “gaskiya ni bazan taɓa amincewa da wannan hukuncin ba, kawai da ne kike ƙanwata da ban ganki ba, amma yanzu nima zuciyata ta amince da miƙa miki ragamar rayuwata, saidai kawai idan baki sona ki fito fili yau ki gaya mun, don bana barin ɗakin nan sai naji abinda ke zuciyar ki game da ni”, ya faɗa yana ƙara ɗaura hannun shi saman kafaɗa na, ya kuma ƙura mun idon shi masu masifan haske da kyau akaina.

A hankali na sauƙe a jiyar zuciya, sannan na ɗago ido na na dubi Amaal alamar neman a gajinta,… Tsaki taja ta harare ni, “common my friend ki gaya mishi gaskiyan yadda ya ke a mine ɗinki, kawai kina da wanda kukayi alƙawarin aure da shi, wanda sanadin soyayyan da kike mishi ne muka sako shi a rayuwar ki don ya kawo mana a gaji bawai shima ya dawo yace yana sonki ba”, ta faɗa tana wani abu kaman zata zo ta yanka mun mari.

“Don Allah kibar shirmen da kike yi a wurin, idan ba zaki iya zama a wurin ba ki fita ki bamu wuri, so kam zata soni, me zatayi da mutumin da ya kusa haifanta, kuma bai damu da miƙa mata soyayyan shi gaba ɗaya zuwa gareta ba”, yana gama hantarar Amaal ya juyo kaina cikin sassauta murya, “plzz mine kiji dani mana”.

Ɗaga mishi kaina nayi ba tare da na furta komai ba, sai dai murmushin da bai bar kan fuskana ba nakeyi, “nikan mine ki buɗe baki kimun magana kada zuciyata ta fashe, wallahi ina miki son da zai iya halakani a yau ɗaya, plz kice wani abu mana dear”, ya faɗa yana damƙe kafaɗa na da ɗan ƙarfi sosai.

“Na amince muyi soyayyah amma bance maka zan aure ka ba, domin nayi alƙawarin auren Dr”, na faɗa ina juyar da idona kan Amaal, bayan na cire hannun shi da ya ɗaura a kafaɗa na.

Mtssss taja tsaki ta kalleni cikin ƙanƙance ido, “wallahi sis babu ruwa na nikan baza ki sakani jin kunyan Dr ba, kuma ke kaɗanki kiyi shirin amsan tuhuma a wurin shi, kada ma ki yadda ki sako ni a ciki, amma kin ban mamaki Hummy, ashe akwai wani sauran ɗa namiji da zai ɗau hankalinki bayan idon Dr”? Ta faɗa tana bin mu da kallon banza daga ni har Faisal ɗin.

“Get out my friend, ki fita a ɗakin nan ki bamu wuri, ke wacce iriyar ƴar’uwa ce wanda bata kishin nata ɗan’uwan sai wani daban da a sama kika sanshi, kuma kije ɗin itama bazata nemi taimakonki ba, shi ma ya sani wannan flower mai kyaun ae bazai zama ta shi bace shi kaɗai, dole muma mu so ta, Allah ya bawa mai rabo sa’a kawai, fita kibani wuri kafin na tashi nazo inda kike yau kiyi kwana hospital”.

Kuka Amaal ta fara yi, wanda daga gani na ɓacin raine, tana duban shi tace, “bros don tsabar son kai irin naka na rashin gaskiya shi ne kake fatan ka tashi ka dake ni har nayi kwanan hospital? Wallahi sai na faɗawa Abbu abinda kake shirin yi na rashin amana”, sannan ta ƙarasa bakin ƙofan ta riƙe tana kallona tace, “ke kuma idan baki rabu da shi ba sai na gayawa Dr kuma yanzu ma zanje na haɗaki da Ummi, kuma babu ruwa na da ke, bana son ƙawa da ke tunda baki riƙe amana” ta juya ta fita cikin ɓacin rai.

“Bros toh kayi haƙuri mu bar wannan maganan, kaga ran Amaal ɗita ya ɓaci, ina tsoron taje ta gayawa Dr Hussain zaiji haushi na, don Allah kayi haƙuri”.

Yana wani murmushin da bai kai ciki ba yace, “bafa zan taɓa haƙuri ba, domin sonki shi ne rayuwata, kina son ganin bana a raye ne”?

Juya kaina nayi alaman a’a, “toh ki bar ni a yadda nake so, mai rabo ya samu cikin mu” ya faɗa yana tashi tsaye.

Hannun shi cikin aljihun wandon shi ya ƙura mun ido bakin shi ɗauke da murmushi, nima ƙura mishi idon nayi domim wani irin kyau Faisal yake mun, ga shi da wani ƙwalisa kaman shi kaɗaine namiji a saudi, murmushi na sakeyi da naga yadda yake wani bina da kallo kaman zai lashe ni, ina kallon yadda yakeyi yasa naji kunya na sunkuyar da kaina ƙasa ina wasa da yatsuna.

“Ki shiryah da yammah na kaiki yawo kiga wurare, yanzu zanje naci abinci na kwanta na huta ko ƴanmata na”, ya faɗa yana fita a ɗakin.

Buga ƙofan da ƙarfi ya saka ni ɗago idona da sauri, Amaal ce kaman an wani jehota ta faɗo ɗakin, sai harara ta ke sauƙe mun, tayi kaman zata yi magana kuma sai ta fasa ta juya ta fita ta bar mun ɗakin, ajiyan zuciya na sauƙe ina taɓe baki na ɗaga kafaɗa ta alaman ko a jikina, kallon wayata nakeyi cike da tsoro, ganin number Dr nah da yake yawo a saman screen ɗin, har ya yanke ban iya na ɗaga ba, a karo na biyu wani ƙiran ya sake shigowa, bansan lokacin da naji zufa a jikina ba, chan cikin zuciyata ina raya kodai Amaal ta gaya mishi wani abu ne? har zai yanke shima da ƙyar na ɗaga.

“Hello” na iya faɗi ba tare da wani kuzari a jikina ba, daga ɗaya ɓangaren naji shi yana cewa, “yes hello baby, yayah naji voice ɗinki kaman kina bacci na tashe ki”? Da sauri na gyara zama na da muryah na nace, “bansan na fara baccin ba yanzu fah na ɗan kwanta”, na faɗa ina jin bugun ƙirjina yana ƙaruwa.

“toh ina Amaal ta tafi ta bar mun ke? Nifa idan bazata baki kulawa ba zan taho na ɗauke abuna kawai muje Daddy ya mana aure, don nafi so ni da kaina na dinga baki kula baby, ki gaya mun bata baki kulawa ko”?

lokaci ɗaya naji tausayin Dr nah cikin zuciyata, runtse idona nayi sannan nace “lahh Dr na muna tare da ita fa, sai da taga na rufe ido ne inaga ta bar ɗakin, amma Amaal tana bani dukkkan kulan daya kamata har ma ina jin nauyi da kunyan yadda suke mun, ka kwantar da hankalinka babyn baby”, na faɗa ina ɗan fitar da muryana don hankalin shi ya kwanta.

Ajiyan zuciya ya sauƙe da ɗan ƙarfi, sannan yayi ƙasa da muryah yace, “baby komai na duniyan nan yayi mun zafi, ashe bansani ba mun shaƙu haka? Gaskiya baby na gajji da kaɗaici, next week insha Allahu zan zo na dubaki, idan yaso ko 1week sai nayi mu juya tare, don na gajji wallahi baby, ko ina baya mun daɗi”, ya faɗa kaman zaimun kuka.

Dariya nayi a hankali nima cikin kewan shi nace, “baby toh ae da sauran hutun mu, kuma inajin daɗin wurin wallahi, kawai kaima kazo mu zauna har sai mun gama hutun tukun mu tafi gaba ɗaya”, na faɗa ina dariya.

Shima dariyan yayi, “haba baby bakijin kunya dukkanmu muje mu taru musu a gida? ae suma zasu kuremu, nidai zanzo nayi 1week, kuma a hotel zan sauƙa ba a gidan ba”.

“Baby meyasa bazamu zauna wuri ɗaya ba? Nikan da kai nake son zama baby”, na faɗa ina masa kukan sakalci.

“idan kina son mu zauna wuri ɗaya ae babu matsalah baby, kawai zanje na gayawa Daddy mun amince aure muke so, sai kawai a ɗaura mana mu zauna a gida ɗaya tunda kema yanzu kina son hakan”, ya faɗa yana dariya.

Da sauri nace “nifa bance aure zamuyi yanzu ba baby, kawai nafi so mu zauna wuri ɗaya ne dakai”, na faɗa ina zaro idona don ganin Faisal daya buɗe ƙofan ɗakin ya shigo.

Kai tsaye inda nake zaune ya taho fuskan shi a ɗaure, ni dai zuba mishi ido kawai nayi ina ganin ikon Allah, daga cikin wayan kuma inajin dariyan da Dr nah yake ɓaɓɓakawa, abin tsoro da mamaki kawai jin Faisal nayi ya hau kan gadon ya ɗaura kanshi akan lap ɗina, sannan ya ɗauki ɗayan hannu na ya ɗaura akan shi yana shafa kan nashi da hannuna, kuma ya wani runtse ido kaman maijin bacci, ga wani ɗan ubansun ƙamshin da yake tashi a jikin shi, wanda lokaci ɗaya naji yana sanyaya zuciyata daga bugawan da tafara daga farko.

“Baby tunda kina son mu zauna wuri ɗaya ae kawai aure ne ya kamace mu, domin gudun kada Baby yayiwa babyn shi ɓarna, azo ana cewa ba haka aka soba, kinga zance ya lalace ƘADDARA TA RIGA FATA kenan, wanda ba hakan za a so ba, so kawai muyi haƙuri na zauna a hotel ɗin ko baby nah”.

kasa bashi amsa nayi saboda yadda Faisal ya saka hannun shi yana ta matsa mun cinyoyina kuma yana mun wani tafiyan tsutsa, runtse ido na nayi bansan lokacin da na sauƙe ajiyan zuciya mai ƙarfi ba, wanda saida Faisal ya buɗe idon shi ya ɗaura su akaina, shi kuma baby daga ɗayan gefen shima ajiyan zuciyan yayi, murya ƙasa-ƙasa yake cewa, “baby ko dai na zo ne kina da buƙatan ganin babyn ki kusa da ke”?

kasa bashi amsa nayi saboda maida hankali da nayi kan Faisal domin na ture hannun shi da yake mun yawo da shi akan cinyana, wanda yanzu yake shirin kaiwa kan gwiwa na, kuma lokaci ɗaya naji numfashina yana shirin ɗaukewa, bansan lokacin dana furta, “wayyo don Allah kabari inajin wani iri”.

Faisal murmushi ya farayi batare da ya daina ba saima ƙoƙarin kai hannun shi kan gwiwa na yakeyi, daga ɗayan ɓangaren kuma cikin wani irin murya mai cike da shauƙi naji Dr yana cewa, “wayyo baby nima abinda nakeji kenan ki daure na samu Daddy ko auren muyi daga baya sai muyi bikin auren yadda kike so”, ya faɗa yana sauƙe ajiyan zuciya mai ɗan ƙarfi.

Runtse ido na nayi da ƙarfin don abinda Faisal ya keyi yafara shiga jikina, amma da Allah ya taimakeni kawai sai naji muryan Amaal da ihu tana cewa, “meye haka bros”?

Da sauri ya tashi ya zauna ni kuma nayi saurin kashe wayan na ƙura mata ido bayan na miƙe tsaye.

Kallona besty nah miss xerks tayi, cike da damuwa tace, “besty dama ma’anan sunan book ɗin naki kenan yau nake gani a tare da Faisal da Hummy”? Ba tare dana ce mata komai ba na runtse ido na cikin damuwa na cije lips ɗina

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here