Jigo a jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya yi gargadi mai ƙarfi kan makomar Najeriya, inda ya bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na iya “lalata Abuja” tare da yiwuwar mayar da babban birnin ƙasa zuwa Lagos idan aka sake zaɓensa a 2027.
Amaechi ya ce akwai buƙatar ’yan Najeriya su yi taka-tsantsan tare da lura da yadda al’amuran siyasa ke tafiya, yana mai jaddada cewa irin waɗannan matakai na iya sauya tsarin mulki da daidaiton ƙasa baki ɗaya.
Ya kuma buƙaci al’umma da su tsaya tsayin daka wajen kare dimokuraɗiyya da kuma tabbatar da cewa duk wani shugabanci yana aiki ne bisa maslahar ƙasa, ba wai son zuciya ko muradin siyasa ba.
Wannan furuci na Amaechi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zazzafar muhawara kan siyasar 2027, inda jam’iyyun siyasa ke ƙara ɗaukar matakai domin karɓar iko.






