Janafty
KANA NAKA..!
*
Book 1
03
Asalin kakanmu wanda ya haifi iyayan mu maza ni da Yaya ishaq bakatsine ne wanda ya fito daga Tsatson katsinawan Karofi.
Karofi kamar Anguwa ce ko wata alkarya dake cikin Garin karamar hukumar Dutsenmah ta Jahar katsina.
Tunda ga Dutsenmah,Katsina Kankara,malumfashi bakori,mahuta da Sauran kananan hukumomin dake zagaye da Garin katsina ba wanda bai san Waye Alhaji Sulaiman Karofi ba,Saboda tun lokacin yana Raye shekaru sama Hamsin da wani abu da suka gabata an yi Attijirin mai kudi,Domin kaf yankin nan ba inda ake siyan Siminti sai a wajensa manyan manyan Store yake kama haya ana cikamai su da Siminti tun yana matashinsa da wannan sana’ar ya fara kuma alhamdulillah ita ta Daukakesa har kuma Allah ya Dauki Rayuwarsa bai sauya sana’a ba.
A yadda Babanmu ya bamu labari Lokacin yana raye Saboda muma ko da mukazo Lokacin Allah ya karbi Ran Alhaji Sulaiman sai dai mun sha Labarin kirkinsa da Dattakonsa bakin Babanmu.
Ya sanar damu cewa Alhaji Sulaiman Kamfani kamfani na Siminti Mota mota ke shigowa Karofi Domin saukemai Siminti kuma ba’a sati duk sai ya kare bayan manyan yan kasuwa yana saida ma marasa karfi da masu siyan daidai misali sannan karin Daukakarsa baya tsawwalla kudi i ya abunda Allah yasa ya samu sai ya sanya musu albarka.
Mutum ne akace nagari kamili mai sanin Darajan dan adam da Dattako,da kowa yake yabonsa Daga uwa har uba duka haifaffun karofi ne,Kenan ba shi da wani garin da ya wuce mai Karofi alokacin.
Yana da matar auransa Daya Hajiya Suwaiba(Hajiyar karofi) ita ta Haifamai manyan ya’yansa guda Uku Hajiya Fatima ce Babba(Hajiyar Dala) sai Hajiya Aisha(Goggon karofi)
Sai karamin su Alhaji Kabiru(Baban katsina)
Sai Autan su Alhaji Sidi( Babanmu)
Wanda rabonsa ne yasa aure ya kullu Tsakanin Mahaifiyarsa Asiya da Alhaji Sulaiman Karofi.
Alokacin baya in aka auro mace daga wani waje ta shigo inda bata san kowa ba,to akan samu a makotan da aka kawo ki kina samu yar D’aki da zata rika shigowa tana tayaki zama da yan aikece aikece to haka ne ya faru da Hajiya Suwaiba ita din yar cikin garin Dutsemah ce kuma auran Soyayya ne ya kulla Tsakanin su mai karfi kafin ta kai su ga aure.
Yadda na samu Labari Hajiya tun tana matashiyarta macece mai kirki da Sanin ya kamata sai dai akan mijinta bata da kauda kai tana son shi Shiyasa take bala’in kishinsa.
Tun sanda aka kawota garin gidan da Alhaji Sulaiman ya gina gefen katangar gidan su Asiya ne, wanda garun gidan Alhaji Sulaiman shi ne garin gidan su Asiya talaakawa ne Futuk,mahaifinta mallan Haruna ya rasu bayan doguwar jinyar da yayi a baya masarin bishiya ne an ce Tun wani Sare wata bishiya da yayi shikenan bai kara lafiya ba har ya rasu Daga Asiya sai mahaifiyarta Atika suke Fafutukar Rayuwa to lokacin da aka kawo Hajiya Suwaiba Asiya ta kan shiga ta taimaka mata da yan aike ce aike ce tunda daman Asiya bata da kiywuya Lokaci kadan suka saba da Hajiya tun balle data fahimci suna cikin Halin matsi ita ke taimaka musu da abinci suturu har kuma ta saka Alhaji Sulaiman shima ya tallafa musu.
Cikin lokaci kadan Asiya ta zama yar Dakin Hajiya Suwaiba duk wanda yasanta yasanta da Asiya,Suna tare ta yi goyon cikin Fatima ta haifeta kowa yaga Asiya sai yaba da kokarinta da Himmanta Hajiya kuwa har ga Allah ta ke tare da Asiya bata taba jin wani abu aranta game da ita ba..
Ana haka har ta sake haihuwan Aisha,lokacin ne Alhaji Sulaiman yazo mata da mganar da ta kusa girgizata wai zai auri Asiya saboda yayi jihadi sannan ta zama abokiyar zamanta na Har Abada.
Ance a lokacin Hajiya Suwaiba tayi tashin Hankali har sai da ta koma gida Ma’ana tayi yaji kuma hakan baisan an fasa ba sai dai ta Dawo ta iske ya gyara ma Asiya dakin dake kusa da nata har an yi biki Asiya ta tare,Ance sillar wannan gabar daga wannan auran ne Hajiya ta kullaci Asiya da Mahaifiyarta Atika akan sun yi auran cin Amana ita kuwa Asiya bata mgana sai kuka ba Laifinta ba ne,Ita batace tana son Alhaji ba shi yace yana sonta batare da sun sani ba ya je ya gabatar da kansa wajen Dangin babanta su kuma sun ga Alhaji ga kudi ga Dattako nan da nan suka basa da Atika tayi mgana suka Rufeta da fada dole tayi shuru.
Sanadin wannan auran ne komai ya fara ko nace shine sillar komai bazan ce Hajiyar karofi ta fara assasan wutar kiyayyar ba Tunda kafin ta Mutu ta yi Tuba tuba irin na Taubatul nasuha.
Zan iya cewa Tsantsan Rabo ne kawai ya kawo mahaifin mu wannan Duniyan,Asalin sunansa ba Sidi ba ne Sidik ne Asiya ce ke kiransa da Sidi har ya bisa zuwa girmansa.
Kusan Lokaci daya Asiya da Hajiya suka yi goyan yaransu ita tana goyan Babanmu ita kuma Hajiya na goyan Baban katsina.
Hajiya ita ta ke zaunar da ya’yanta tana fada musu auran cin Amana mahaifinsu yayi da Asiya har aka samu Sidi saboda haka shi ba Dan’uwan su ba ne bare ne tunda auran cin Amana ne to ba d’an Sunna ba ne shege ne, mgana fa har ta fita Domin ba inda Hajiya bata yada mgana gidan biki ko suna har yakai ga Asiya ko Atika suka daina fita Saboda kananun mganganu.
Har sai da Alhaji Sulaiman yaji ya tsawarta mata ya kuma ja kunnenta da sai ya iya Rabuwa da ita Saboda haka ance ta sha kuka Ranar Asiya tasha zagi da gorin ita ta zama gatan taa ammh Daga karshe ta saka mata da Auran mijinta.
Adalilin irin wada’nan kalaman na bakin Hajiya suka yi tasiri a zuciyar Babbar yarta Hajiya Fatima(Hajiyar Dala) wanda har mahaifin mu ya koma ga Allah bata kaunace sa ba Duk da kuwa an ce Kafin Asiya ta bar gidan Duniya sai da ta rika rokon Hajiya gafara ammh taki yafe mata sai daga bayan ta jima ita da Atika a kushewarsu sannan Hajiyar Karofi ta gane kuskuranta ta gyara alokacin kuma komai ya kure mata.
Babbar Bakincikim Hajiya ganin da tayi Sidi da Kabiru sun taso kan su daya sannan komai Alhaji Sulaiman zai yi musu tare ne,ita kuma bata so har ko yaushe a shege take kallon Sidi Tunda auran cin Amana ne..azaba da ukuba ba wanda Sidi bai shata a hannun Hajiya ba ko kasheshi Hajiya zatayi Asiya ko Tarin ta bamai ji a Tsakar gida tana da hakuri da kawaici sannan ga Ladabi da Biyayya ko da ta auri Alhaji bata daina yi ma Hajiya bauta ba sai dai bata gani Laifinta daya meyasa ta auran mata miji..?
Babanmu ya fada mana yana d’an Shekara goma sha uku a duniya Mahaifiyarsa Asiya ta rasu da tsohom ciki ta fito daga makewayi jirin Hawan jini ya fardar da ita kwananta Daya asibiti tace ga garin ku nan da Farko Mutuwar ta daki Hajiya ammh Daga baya sai ta saketa.
An yi tashe tashen hankula Har sai da iyaye suka shiga ciki kan zaman babbanmu a wajen Hajiya kememe ko tace bazata rika dan shege d’an cin Amana ba sai Atika aka kai mashi ta rikesa Gefe D’aya Alhaji Sulaiman na kula dashi sai dai duk yadda Hajiya taso ta raba Kabiru da Sidi ta kasa wannan jinin na yawo ajikinsu..sannan Fatima ce kadai ta ke bayanta Aisha kuma babu ruwanta bata Cika Daukan mganarta ba..
Babanmu ya d’anda’na gudarsa a Hannun Hajiya tun da duka bai Rufe shekara biyu a hannun Atika ba,ta rasu sakamakon amai da guduwa shi kuma Alhaji Sulaiman yace hajiya bata isa ba Sidi zai zauna agidan nan tunda shima gidan ubansa ne kamar sauran ya’yanta wannan dalilin ya kawo babban baraka tsakanin ma’auratan,In yana gidan Sidi zai zauna cikin salama ammh da zarar ya fita sai abunda Allah yayi ukuba ba irin wacce bai gani ba,Hajiya ta taba Cire masa riga ta zane shi da wayar radio mai karfi kawai saboda sun fita shi da Kabir suka dawo jikinsu duk kasa shine ta rufesa da dukan meyasa yake jan Kabiru ai ba Daya suke ba shi da’n Shege ne Kabiru kuma yaron sunna ne da sahihin aure ya samar dashi Ance sanadin dukan har sai da Sidi ya suma saboda azaba wannan dalilin yasa Alhaji Sulaiman ya saki Hajiya saki daya sakin daya girgizata ta Dade bata gidan ta kuma kwashe ya’yanta duka ta tafi dasu shi kuma sai ya kyaleta iyayenta sun shiga ciki ammh ba’a samu daidaito ba Saboda Hajiya ta riga ta kara hawa dokin naki kan bazata rike Sidi ba shi kuma Alhaji Sulaima yace ba inda zai kai shi in bazata rikesa ba to ta barshi kusan shekara daya Alhaji sulaiman shi ya Dinga wahala da Sadi komai shi ke yi mai Hajiya kuma ta Dauka Alhaji Sulaiman zai sauko yazo ya bata Hakuri sai taga ba haka ba ne ga su kabiru suna ta Damunta da Babansu shi kuma tunda haka ta faru bai taba Takawa wajenta ba ai yace ba shi yace tatafi da ya’ya ba ita taga dama Saboda haka ba zai bisu ba in har ya’yansa ne zasu nemesa.
Ganin Ba riba ne yasa da Umarnin Iyayanta Hajiya ta dawo gidan Alhaji Sulaiman ammh an yi musi tsakani da Sidi ba ruwanta da shi,Shi dai yana bata girmanta domin kamar uwa ya Dauketa ita kuwa ta tsani ma ta Bude ido ta gansa don dai bata da yarda zatayi.
Cikin wannan Halin Rayuwa ta rika ganganrawa Alhaji sulaiman bai tara dukiya ya rika siyan kaddarori ba sai dai ya gina ya’yansa ya basu kyakyawan ilimin zamani,Matan daga Sakandiri yake aurar da su,Ammh dukkansu sai da ya kai su Hajji suka sauke Farali Hajiya fatima Soja ta aura dan kano ne chan aka kaita,ammh daga baya an sauya mai wajen aiki ya koma Kudu,Kafin zuwa yanzu sun zauna garuruwa da dama kafin ya yi ta samun karin girma har ya kawo matsayin da ya kai a yanzu.
Sai Hajiya Aisha da ita kuma d’an karofi ta aura kuma kamar aboki yake wajen Alhaji Sulaiman sai dai tun alokacin ba’annin juna ba ne..
Alhaji sulaiman bai bar gidan duniya ba sai da ya gina ya’yansa sannan ya aurar da su bayan mata ma har da mazan har kuma ya bar duniya bai ga Nadamar Hajiya suwaiba(karofi),kan Asiya da zuru’ar ta ba,har alokacin bata ganin duk wani daya shafi zuru’ar Asiya da Atika da Daraja saboda abunda ya faru.
Daga kabiru har Sidi sai da suka fara samun Takardan Education kafin su Dora degree din su,Baba kabiru fanni Biology ya karanta,shi kuma Babanmu sai ya karanta Fanni Kasuwanci Business admistration.
Bayan kamallah karatun su dukkansu sun samu aiki Kabiru ya fara koyarwa a wata makaranta gwamnati dake Karofi shi kuma Sidi sai ya samu aiki a wani ma’aikatan littafai dake katsina chan ya tattara ma ya koma Saboda gidan baya mai dadin zama Hajiya ko zai gaisheta sau dubu bazata amsa ba sai tayi kamar bata gansa ba,Sai dai yana bata girmanta a matsayinta na uwa bai taba riketa aransa ba kuma kullun haka Alhaji Sulaiman ke gaya masa Hajiya uwa ce garesa komai zatayi mai kada ya Daukesa a wani abu ya Dauka ajizanci ne na D’an adam.
Shiyasa bai taba kallonta da wani abu ba,Balle da suka taso kamar uwa daya uba daya shi da Kabiru in ba mutun bai sani ba zai dauka uwar su daya ubansu daya sai an fada maka ne zaka san ba Uwa dayace ta haifesu ba ammh suna Diban kama Dukkan su Dogayen katsinawa ne marasa Lalaci Sannan shi kabiru yafi Sidi haske Saboda Hajiya farace,Sakamakon ita Asiya baka ce shiyasa sai hasken sa ya zama mai Duhuwa..
Yana shigowa karofi duk bayan Sati hudu kuma duk alherin da zai yi ma Dangin Mahaifiyarsa,zai yi ma Hajiya sai dai bata karba yana sauke ledan zata Dauka ta kone daga baya sai ta Daina konawa Tunda Alhaji Sulaiman ya ja mata kunnen tana albuzuranci da Dukiya da kaya watarana zanin Daurawa sai ya gagareta sai ta tsorata ta Daina Konawa sai dai ta Sadakar da su.
Kabiru ya riga Sidi aure saboda shi Daga baya shima katsinan ya koma da koyarwa a wata babbar sakandiri,Achan ya hadu da Saudatu ita din buzuwar yamai ce Kasuwanci ke shigo da su Katsina ta Jibiya anan suka Hadu Allah ya hada kauna Tsakaninsu har ta kai su ga aure Saudatu(Mama kofar soro) farace Doguwa kyakyawa kin kowa kin wanda ya rasa ga gashinta har gadon Baya Hajiya tayi alfahari da wannan auran ganin kamar Kabiru ya kece sa’a cikin maza zai auri buzuwa,Barin ma Hajiya Aisha da itace kamar makwafin Hajiyar tafi kowa Fi’ili da karairata Ita Hajiya Fatima babu ruwanta ita datake ma kusa.
Har chan yamai akaje aka nema ma Kabiru auran Saudatu,suka kuma Tare a gidan su dake karofi inda Alhaji Sulaiman ya gina musu barayi guda biyu,Na kabiru da Sidi shima sai da Hajiya ta rika yada mganar ai shi ba Dan gida ba ne bashi da gadon Alhaji shi dai bai kulata ba sai dai yayi mata addu’an shiriya tunda ganin Shekaru sun fara ja Hajiya bata Sauya ba,bai tunanin zata iya sauyawa sai dai shiriyan Allah kawai.
Tun zaman Saudatu karofi taga gata wajen Hajiya kamar ta lasheta barin ma har zuwa ake yi ganinta Saboda kyanta da gashinta,sai taji dadin haka Domin daman tana bakincikin Sidi na aikin kamfani Kabiru kuma ya zama malamin makaranta in tayi mai korafin haka dariya yakan yi kafin yace”Hajiya kenan ko wani bawa da kika gani yana tafe da kaddaransa arzikinsa da aurensa da Haihuwarsa da Mutuwarsa'”
In yace mata haka sai dai ta kallesa ta Harareshi kafin tayi kyafci Sai tace”Ai daman haka zakace Yaron nan Sidi ya gama dakai kai da Aisha Fati ce kadai tasan ciwo na”
Sun riga sun Saba da Halinta shiyasa suke Lallabata su rabu lafiya,yana katsina sai sati sati yake zuwa ganin gida Tun auran su daman Hajiya ta gama karanta ma Saudatu kaf Waye Sidi da auran cin amanan da Asiya tayi da mijinta,Sannan ta fadamata Sidi ba dan sunna ba ne An haifesa da cin Amana ne,shi yasa ta tsane shi duk da ta Lura Kabiru na bala’in ji da kaunar Sidi shiyasa ranar da ya fara kawo mata shi kadahan kadahan ta karbesu sai faman tab’e baki take yi Sidi na lura da ita bai yi mamaki ba Daman yasan za’a rina shiyasa baya fatan in yayi aure ya kawo matarsa wannan gidan yasan ta zama Nama.
Sai da Kabiru da Saudatu suka Haifi Diyar su ta farko Fatima suna kiran ta Binta sunan Hajiyar Dala taci.
Ashekaran Sidi yayi aure auran da Hajiya taji dadinsa tunda ba auran kece sa’a ba ne,Sidi yar’uwansa ya aura da kakansa na wurin uwa da kuma kakan TAMADINA na wajen Uwa itama sun hada iyaye daya,su biyu kadai mahaifinsu ya haifa kafin ya rasu Tamadina da Usman kuma ba uwarsu daya ba kowanne da Tsatson sa Ita ta Madina mahaifiyarta haifaffiyar karofi ce ita kuma mahaifiyar Usman yar karaye ne dake kano Lokacin data gama Takaba ta roki alfarman Tafiya da Usman garinsu aka bata Tun yana da Shekaru goma aduniya ya bar Karofi.
Hafsatu(Tamadina) shine ainihin sunanta,kuma ta samo sunan ne tun tana karama tun da bakinta ya bude duk wanda yayi mata mgana sai tace madina zata tafi shikenan Hafsatu ya bace sai dai tamadina,sannan Tamadina Bebiya ce kuma ba Ciwo bane da shi aka Haifeta mganar ta baya fita Sosai sannan bata ji sosai,ahaka taso cikin rashin gata tunda kaf zuru’ar su Asiya ba wani mai arziki sai Buga buga kawai.
Tamadina baka ce kuma gajera shiyasa duk wanda yasan Tamadina ya ganni ni Fa’iza zai san kammaninta da suffanta duka na Dauko sakamakon su ya Asiya sun Dauko Tsawon babbanmu da Hasken Fatarsa ni kuma hatta bakin Tamadina ni na Dauko shi har da gadon Rashin ji, na duk daga wajenta na gaje shi.
Ba auran Tausayi Sidi yayi da tamadina ba shi ya ganta yaji yana sonta kuma manya suka shiga ciki,Musamman Alhaji Sulaiman da ya shige ma Sidi gaba,har akayi auran da farko yaso ya tafi da ita Katsina ne sai Alhaji Sulaiman ya hana yace ya barta agida kamar yadda Dan’uwansa yayi shi kuma bazai iya yi mai gaddama ba sai ya bar Tamadina a gidan karkashin Hajiyar Karofi da Saudatu(Mama kofar soro)
Ba iya ni na wahala da Mama ba Mahaifiyata ma taci wuyarta ita da Hajiya suka maidata kamar jaka gashi Tana da lalura sai su yi ta zaginta bataji,Gashi ba daman tayi mgana sai Hajiya ta hantareta tana fadin”Ta fi chan Dangin maciya Amana..Dangin bakake munana kawai masu bakincikin munafunci”
Kalaman tun tamadina bata gane su har ta fara ganesu ta kuma Haddace su,In Sidi na nan ne take samun salama sannan tana jin dadin zama da Uban mijinta Alhaji Sulaiman.
Da kuma Hajiya Aisha(Goggon karofi),Sai Kabiru wanda shima ba ruwan shi ammh Hajiyar Dala sai abunda ta manta cin mutumci in tazo gidan nan Tamadina sai tayi kuka Taruwa suke yi su yi ta cin mata Mutumci wani Lokacin batama jinsu har Jin dadi take yi da Allah yasa bebiyace ita da ta kunshi bakinciki.
Bayan Haihuwar Saudatu in da ta Haifi ISHAQ Bayan Haihuwar Saudatu,Tamadina ta haifi yarta mace Aka saka mata suna Asiya sunan mahaifiyar Sidi taci,Shekara shida tsakaninsu an yi sunanta ba jimawa Alhaji Sulaiman ya kwanta jinya ciwon sugar da bai tashi ba Gabadaya duk abunda ya tara sai da ya kare wajen neman mgani daga karshe bai tashi ba ya koma ga Allah.
Rasuwar sa itace silar Wargajewar komai an yi ta rigima wajen raban gado,Domin Hajiya ta yi tsaye tace Sidi bai da gadon Alhaji Saboda shi din d’an cin Amana ne ganin rigiman tayi girma sidi ya tattara matarsa suka koma katsina ya kama Hayar Daki biyu da Tsarkar gida sai kitchen,Ya kuma ce ya yafe gadon har Abada aka rasa rai ma aka Hakura ballatana Duniya tun faruwar lamarin yasan Hajiya bazata taba kaunarsa ba kawai sai ya Hakura wanda ya hada ya raba,Tundaga Lokacin sai ya Dade bai je karofi ba Sai dai suna mgana ta waya da Kabiru da Aisha tunda su kam basu yar da Zumunci ba..
Ko shekara basu shafe a katsina ba ya samu aiki a wani kamfanin Sarrafa leda dake malunfashi sun basa matsayi mai girma da gidan zama ya tattara tamadina suka koma malumfashi da zama
Acikin shekarun da suka gabata abubuwa dadama sun faru ciki har da Sauyin rayuwar da kowa ya samu Sannan da Nadamar Hajiya,Rana daya ta rika kuka tana a kira mata Sidi ta nemi afuwarsa dayake ita kadai ce agidan yanzu Kabiru shima ya Tattara sun koma cikin katsina da zama Tunda ya zama principal bayan yaje ya karo karatunsa
Sidi yayi matukar mamakin nadamar Hajiya daman bai taba riketa ba ya riketa yana share mata hawaye tare da Fadin bai taba riketa acikin Ransa ba kowa yaji dadin wannan al’amarin ban da Hajiyar Dala domin har Abada bazata kaunaci Sidi da zuru’arsa ba.
Hakama Saudatu(Mama kofar soro) itama ta tsani Sidi da zuru”arsa ganin tafi TaMadina komai na bangaran kyau da Nasaba ammh a bangaran jin dadin gidan miji,Sai dai su goga domin bata fita komai na inganta Rayuwa ba, Sidi na yima Iyalansa komai sun gado Halin Dattako wajen mahaifin su Alhaji Sulaiman
Shekaru goma da suka gabata.
A cikin wad’anan shekarun goman,komai ya faru kuma ya kare,mun fara samun ingantattaciyar Rayuwa a malunfashi,Bayan haihuwar Ya Asiya sai Yaya mariya sai ni Fa’iza da aka Haifeni da Laluran Raunin ji sai autarmu dataci sunan Tamadina Hafsatu ita an haifeta ma ne Babanmu na cikin Tsananin jinya shima Ciwon sugar yayi gado wajen mahaifin su Alhaji Sulaiman shima kamar shi din sai da komai ya kare tas wajen neman mgani kafin rasuwarsa sai da aka yanke mai kafa Da Hannu bazan taba mantawa ba ina Aji hudu na matakin primary a asibitin gwammatin garin Malunfashi Babanmu ya rasu a hannun Alhaji Kabiru(Baban katsina) da Tamadina Mutuwar da Sanadinta ta gama gigita Rayuwarmu gabadaya sanadinta muka san halin Rayuwa muka san maraici da rashin gata.
Da gidan da muke ciki kadai muka Tsira shima da aka saida shi duk a bashi ya tafi tunda jinya yayi kusan shekara uku sai da komai ya kare aka koma cin bashi duk da Baban katsina na Tallafa mana shi da Hajiyar Karofi.
Mutuwar Babanmu shine Silar Barowarmu Malumfashi muka koma Karofi daga Lokacin kuma komai na Cigabaman mu ya tsaya,Tamadina tana gama Takaba gidan su ta koma,mu kuma ta barmu gaban Hajiya da Farko da nan aka barmu da mun samu Rayuwa mai inganci saboda Hajiya tana kaunarmu kwatankwacin kaunar da take yi ma Sauran jokokinta.
Ammh sai hakan bai samu ba Baban katsina ya tara su Hajiyar Dala yace zasu rabamu a Tsakaninsu Saboda Rage ma Hajiya Dawainiya,Shi farko Yaya Asiya yace zai dauka Ita kuma Goggon Karofi tace zata Dauki Yaya mariya ta hadata cikin ya’yanta ta rike Tsakani ga Allah.
Shi kuma Baban Katsina sai yace Hajiyar Dala ta Dauke ni Tunda Hajiya ta maida ma Tamadina Hafsatu tunda tana karama ne Lokacin sosai tace ta riketa tukunna har sai ta yi wayo sosai.
Ai Hajiyar Dala agaban kowa da kowa ta Daka tsalle tace bazata Daukeni ba takai gidanta ban ko ji sosai ta Daukan ma kanta Lalura ita bazata iya ba har Hajiyar karofi sai da tayi mata mgana tace bazata Dauki kowa ba,Sai aka kyaleta Baban katsina da ya fara fada Hajiya ta hanasa tace ita zata rikeni shi ya tafi da Ya Asiyan kawai ita zata rikeni Hajiyar Dala najin haka sai tace sai dai ta Dauki Yaya Asiya tunda ita Lafiyarta kalau Baban katsina yaso ya hana sai Hajiya tace abata,wannan shine Dalilin Rarrabuwarmu Yaya Asiya a kano ta tashi Ta samu tayi karatunta har Sakandiri ita kuma Yaya mariya ta taso Hannun Goggon karofi itama tayo karatunta ita kam har matakin N.C.E,Sai Hafsatu wanda Baban katsina yace in ta kara girma shi zai Dauketa Tunda ni Hajiyar karofi zata rikeni ammh duka Dawaniyata Na hannunsu.
Naji dadin barina a karofi da akayi Saboda Tamadina da Hafsatu sai kuma Yaya Mariya dake kusa Damu ko da yaushe suna gidan Hajiya tare damu Ni dai Dakyar Hajiyar Karofi ta bari na gama nakai aji Biyar na matakin primary domin na rubuta jarabawar fita ba sai fada take yi Me zan ji a makaranta ko me zan gane Tunda ba ji nake yi sosai ba,Baban Katsina ya so nayi karatu ammh sai yaga bayan Hajiya Nima bana so Saboda ina shan Dariya da Wulakanci a makaranta wajen Sa’annina Saboda yanayin mganata da raunin ji na sannan kuma ni bakace bani da kyau shiyasa sai karatun ya ficemin Daga raina na,na saka araina sai mai gata ko mara Lalura yake zama mai ilimi bani da na ke nakasashiya ba.
Ammh Hajiyar karofi bata bari nayi Sakaci da na addina ba,Ta sakani Islamiya da Hadda da Makarantar allo ta Safe da Dare,Shi kam ban yi sakaci ba Kuma dayake karatun Qur’ani ne da Liffafan addini ina ganewa sannan Hajiya bata hanani ba shima na Bokon bazata iya juran dawowa da nike da kuka bane Saboda har waka ake yi min bebiya mamarta ma Bebiya sai nake jin guilt din abun acikin raina da yasa naji na Tsani bokon gabadaya sai Hajiyar Karofi ta maramin baya domin gatan Duniya ba wanda bata nuna min ba.
Rikon Hafsa ya koma Hannun Goggon Karofi Saboda Tamadina tayi aure a Dutsenmah ta auri wani magini ne matan sa Biyu itace ta uku,Sai Baban katsina yaso ya karbi Hafsah Mama kofar soro ta daka tsalle tace bazata rike zuru’ar Tamadina ba dangin Maciya Amana da Bebaye ba Hajiya tayi kuka kamar ranta zai fita tasan duk abunda ta Shuka ne take gani ta zaunar da Mama da Hajiyar Dala ta gaya musu komai ta kuma yi kokarin cire musu wannan Tunanin ammh batayi nasara ba Dole ta zuba musu ido ganin abun na neman ya lalace Sai Goggon Karofi ta raba Gardama ta Dauketa kawai ni da Farko ban san matsala ko matsin Rayuwa ba, sai da sanadin ciwon Hajiya ya wujijjiga Rayuwata. sannan na kara Fahimtar bamu da gata sannan maraici ya gama Lullube rayuwarmu tun a baya na Fad’a muku ita kanta Tamadina ba su da wani gata balle mu yi Tunanin samun gatan ta barayinta gatanmu kenan Dangin Babanmu su kuma k’alilan din su ke son mu da Kaunarmu.
Bazan taba mantawa da wata rana na Dawo daga allon Safe ina shiga Dakin Hajiya na ganta kwance ba yadda take ni na Ruga na je na kira Goggon Karofi tazo ta gani,aka kwashi Hajiya sai asibiti ashe Faduwa tayi ta samu shanyewar barin jiki,ta koma sai dai a kwantar a tayas,ganin haka yasa Goggon Karofi suka yi shawara da Baban katsina ta maida Hajiya da ni gidanta tana kula Damu gabadayamu,Ko wata uku Hajiya batayi tana jnya ba,jikinta ya kara Rikicewa ga nauyi yayi ma Goggo yawa Mijinta ma’aikacin gwamnati ne ammh kuma akwai Dawainiya shi kuma Baban katsina Lokacin ya na matsayin Daractan Ilimi ne na Katsina gabadaya ya samu Rufin asiri sosai.
Shiyasa Saboda ya rage mata nauyi yace zai daukeni alokacin cikin Fargaba ta kallesa kafin tace”Abban Ishaq kana ganin ba matsala..?
Ajiyar rai ya sauke tabbas akwai matsala yasan Halin Saudatu ammh kuma ai gidansa ne kuma shi ke auranta Dole Fa’iza ta zauna karkashin kulawarsa shiyasa cikin karfin Hali yace”Kada ki damu ba wata matsala ta had’a kayanta da zarar na tashi da ita zan wuce”
Nayi kuka kamar zan mutu da naji Goggo tace na shirya nabi Baban Katsina gidansa Yaya mariya ne da Goggo suka rika Lallashina ni nasan gidan bamai kaunata,Daga maman har Anty Binta da Ya Ishaq wanda in dai suka yi Hutun Makaranta yakan Biyo Baban katsina ya gaida Hajiya wlh baya kallona bazan taba mantawa da Ranar da ya fara ganina agidan Hajiyar karofi ba kallon Sama da kasa yayi min kafin ya kauda kai ya yamutsa Fuska ya kalli Hajiya yana Fadin”Hajiya wacece wannan mummunar bakar yarinyar..?
Hajiya cikin yar Dariya tace”Baka gane ta ba ko..?
Fa’iza ce yar wajen Marigayi Babanka Sidi”
Ina kallo ya kara kallona ya yamutsa Fuska kamar yaga kashi kafin yace”Hajiya bata da kyau Sannan ban taba ganin baki irin bakinta ba kamar ta shafa shuni”
Yafad’a cikin Sigar Tozarci ita ko Hajiya Dariya tayi kafin tace”Kuma kai nayi ma kamu ba”
Agaba na ya Tofar da yawu kafin yace”Allah ya tsareni Hajiya ai ni Matata bata zo duniya ba tukunnah”
Alokacin Hajiya bata Dauka wani abu ba ammh ni da na taso cikin wannan yanayin nasan tozarci ne nayi kuka Sosai.
Ina kuka ina komai Baban katsina ya sakani a mota yana bani baki sai Katsina Hajiyar karofi kuma bata mgana Sosai jikinta yayi zafi,sai dai bin mutane da ido kawai sai hawaye bata mgana.
Tana kallona zan tafi na rike hannunta ta gyadamin kai ina kuka tana Hawaye itama a mota ma kukan na Dinga sharba sai da Baban katsina ya jawoni jikinsa yana Lallahina Fadi yake yi”Kwantar da Hankalinki Fa’iza zan kula dake kwantacin yadda sidi zai kula da dake in yana raye”
Lokacin ba jinsa nayi ba ammh nasan Lallashina yake yi.
Sai dare muka isa katsina anguwar Kofar soro Makeken gidan da Baban katsina ya gina Tun ranar da na saka kafata acikin gidan nan ban kara farinciki ba har fita ta zuwa gidan Ishaq babu abunda ya Sauya.
Nasan dai Baba na gaba ina Binsa a baya da jakar kayana ina kalle kalle har Babban Falon gidan in da mama ke zaune ita da Yaya Ishaq sai Anty Binta da tayi aure ammh acikin garin katsina Sai Jamal wanda ke bi ma Yaya ishaq sai Karamar su Badariya.
Dukkansu Baban suka zuba ma Ido da farko Mama ta fara mai lale bata ganni ba sai da ya juya yana kallona kafin yace”Saudatu ga Fa’iza ta Dawo Hannuna da zama har na aurar da ita ki kaita Dakin yaran nan ta yi wanka ta Huta”
Ai ranar naga tashin Hankali agabanmu Mama ta dinga Bala’i tana fadin bazan zauna mata agida ba Dangin munana maciya amana Dangin kurame me zatayi dani ban da akara mata wahala Fada dai sosai tana Fad’a Baban katsina na Fad’a har yakai ga Baba ya kusa saka ma Mama Hannu sai da su Ya Ishaq suka Shiga Tsakani ita kuma tayi shewa tace da ya sa ke ya mareta wlh bazan zauna mata agida ba.
Ranar a falo na kwana rakub’e ina rawan sanyi da tsoro,Duk naji mganganun Mama Saboda da karfi take mganarta Tunda Baba ya shige Ciki itama ta shige a Fusace ban kara ganin kowa ba Badariya ce tazo wajena Anty Binta tajata suka tafi gidanta saboda Kada ta rabe ni Jamal kuma daman ba wani babba ba ne alokacin tashi yayi ya shige Dakinsa ko ajikinsa Ya Ishaq ne ya taso yazo gabana yana min kallon Tsana da kaskanci kafin yace”Dama kece Kurman nan..?
Ko Bebiya ma zan ce..?
Ban ji sa ba shiyasa na kura masa ido kauda kai yayi ya wuce yana fadin”Abubuwan sun yi miki yawa..ga baki ga Muni ga maraici ga Ki kurma”
Daga haka shima ya Tsallake ashe wasa farin girki wani kukan Rahma ne Duk yadda Baban katsina yaso ya inganta Rayuwata ya kasa Domin Mama tafi karfinsa bashi da yarda zai yi da ita,Tunda nazo gidan ta sallami Duka yan aikinta a shekaruna sha Uku a duniya na bautu da aikin Wahala nau’i Dabam Dabam,in na tashi Tun asuba bana komawa sai wani Daran abinci kuma sai an rage nake samun naci Tun ban iya girki ba har na iya aiki kuwa ba wanda ban iya ba In Baba yayi mgana sai tace zata koreni.
Nayi wahala da Mama da ya’yanta sannan nayi wahala da Anty Binta da Ya’yanta Ya Ishaq ko ta gabansa na Gifta sai ya Hantare ni da Mummuna,baka,Tun bana Fahimtarsa har na fara gane hantara ce da Tsana shi da Anty Binta sun ce basa son kallon Fuskata baki na da muni na yayi yawa.
Baba yaso ya maidani makaranta Mama tace zai yi asaran kudin sa ne Tunda baji nake yi ba Sai yace zai maidani islamiya Dakyar ta amince ina zuwa ta Lasar zuwa shidda na yammah ammh sai nagama duka aikina sannan zan fita,anan na samu na Sauke alqur’ani daman kum na d’an yi nisa a karofi,sannan nayi karatun Sauran Littafan Addini da wannan zan iya cewa na Tsira a zamana a gidan Baban katsina.




