Hukumar zabe mai zaman kanta a Nijeriya INEC, ta fitar da sabon kundin dokoki da ka’idoji na shekarar 2026 ga jam’iyyun siyasa, tare da neman ra’ayoyin masu ruwa da tsaki domin inganta tsarin zabe gabanin babban zaben 2027.
Shugaban hukumar Farfesa Joash Amupitan ne ya bayyana hakan, yayin wani taro da shugabannin jam’iyyu a Abuja, inda ya ce sabbin ka’idojin sun yi daidai da dokar zabe ta 2026, tare da cike gibin da aka samu a tsofaffin tsare-tsare.
Sabbin ka’idojin sun kunshi gyare-gyare a fannoni kamar rajistar jam’iyyu, gudanarwa, zabukan fidda gwani, yakin neman zabe da kuma sarrafa kudade da ma sharuddan soke rajista.
Ya jaddada cewa sahihin zabe yana farawa ne tun kafin ranar kada kuri’a, tare da nuna muhimmancin gaskiya da adalci a matakan tantance ‘yan takara a cikin jam’iyyu.






