Home Rahoto Masu daukar nauyin Boko Haram sanannu ne — Tukur Buratai

Masu daukar nauyin Boko Haram sanannu ne — Tukur Buratai

9
0

Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Tukur Buratai, ya bayyana cewa akwai sanannun mutanen da ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci a Najeriya, amma ya ce bai kamata a dora masa alhakin bayyana sunayensu ba.

Buratai ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels , inda ya ce hukumomin tsaro sun san wadanda ke bayan daukar nauyin ta’addanci, amma akwai dalilan da suka sa ba a bayyana sunayensu ba.

Ya ce, “Ba za a ce ni ne zan dauki alhakin fadin sunayen masu daukar nauyin ta’addanci ba. Ba wai kawai ambaton suna ba ne, hukumomin da abin ya shafa sun san dalilin da ya sa ba a fitar da sunayen ba. Wadannan mutane suna cikin al’umma kuma an san su.”

Tsohon hafsan ya kara da cewa yana daukar alhakin wasu abubuwa da suka shafi rundunar sojin kasa kawai, amma ba dukkan batutuwan tsaro ba.

A shekarun baya, ana ci gaba da kira ga gwamnati da ta bayyana sunayen masu daukar nauyin ta’addanci, musamman bayan da ta sanar a shekarar 2021 cewa ta gano wasu mutane da kungiyoyi da ake zargi da taimaka wa ‘yan ta’adda.

Hukumar Nigerian Financial Intelligence Unit ma ta taba bayyana cewa ta gano wasu kudade masu alaka da ayyukan ta’addanci, yayin da hukumomin tsaro suka kara kaimi wajen binciken hanyoyin da ake bi wajen tallafawa ‘yan ta’adda.

Duk da haka, har yanzu ba a fito da sunayen wadannan mutane a fili ba, lamarin da ke janyo suka daga kungiyoyin fararen hula da masana tsaro, wadanda ke ganin cewa bayyana sunayen na da muhimmanci wajen kawo karshen rashin hukunta masu laifi.

Najeriya dai ta shafe sama da shekaru goma tana fama da rikicin ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, inda kungiyar Boko Haram da bangarorinta suka haddasa asarar rayuka da kuma raba dubban mutane da muhallansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here