Home Siyasa Gwamnan Zamfara zai koma APC

Gwamnan Zamfara zai koma APC

2
0

Rahotanni na nuni da cewa jam’iyyar APC ta cimma matsaya da gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare kan sauyin sheka daga PDP.

Jaridar Punch ta rawaito cewa jagororin APC a Abuja, sun yi wa gwamnan alkawarin tikitin takarar 2027 ba tare da hamayya ba.

Har ila yau, sun gindaya sharadin kasafta mukamai bisa tsarin 60/40, inda gwamnan zai tsira da kaso 40, sai kuma tsagin Ansaru da zai ja kashi 60.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa gwamnan zai sanar da sauyin shekar tasa nan da bayan Sallah, amma a baya gwamnan ya sha nanata cewa makomar zamansa a PDP ta danganta da hukuncin da kotu ta yanke kan halascin babban taronta na kasa da aka gudanar a Ibadan.

Dauda Lawan Dare, shi ne gwamnan PDP daya tilo da ya rage a yankin arewa maso yamma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here