An gurfanar da Jabir Mu’azu Gwarzo a gaban Babbar Kotun Jiha mai lamba 23 a Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Halima Aliyu Nasir, bisa zargin kashe matarsa amarya Maryam Sulaiman.
Mai gabatar da ƙara, Babban Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a na jihar, Barista Abdulkarim Kabir Maude, tare da Barista Safiya Yahaya Yalwati, sun roƙi kotu a karanta masa tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Jami’in kotu, Mas’udu Ibrahim Gwangwazo, ya karanta tuhumar, inda wanda ake zargi Jabir Mu’azu ya musanta aikata laifin.
Masu gabatar da ƙara sun nemi a ba su lokaci domin fara gabatar da shaidu, yayin da lauyan wanda ake tuhuma, Barista Dini Abdu Usman, ya ce ba su da wata adawa da buƙatar. Daga nan kotun ta sanya ranar 3 ga watan Afrilu domin ci gaba da sauraren shari’ar.
Tun da fari dai ana zargin lamarin ya faru ne a ranar 10 ga watan Yuni, 2026 da misalin ƙarfe 2 na rana a garin Fada, layin Minista da ke ƙaramar hukumar Gwarzo, inda ake zargin ya soki matar da wuka tare da yanke hannunta da kafaɗarta.
Bayan zaman kotun, Babban Lauyan Gwamnati Barista Abdulkarim Kabir Maude ya bayyana cewa gwamnati na ci gaba da bin shari’ar domin tabbatar da adalci, yayin da lauyan wanda ake tuhuma Barista Dini Abdu Usman ya ce za su kare haƙƙin wanda yake wakilta ta hanyar doka.






