Home Labarai Anga watan Ramadan a Nijeriya 

Anga watan Ramadan a Nijeriya 

8
0

Mai martaba Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ba  sanarwar ganin watan Ramadan na shekarar 1447 a yau Talata 29 ga Sha’aban  17 ga watan Fabarairu 2026.

Sarkin Musulmi ya aminta da rahotannin ganin watan da aka samu a wurare daban daban a faɗin Nijeriya.

A wata takarda da shugaban kwamitin harkokin addini na masarautar Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaid ya sanyawa hannu ya ce Sarkin Musulmi ya aiyana gobe Laraba a matsayin 1 ga watan Ramadan 1447 bayan hijira.

Ya ce Sarkin ya roƙi Allah ya sanya alheri ga ibadar azumi ya kuma roƙi mutane su cigaba da yi wa ƙasa addu’a ta zaman lafiya da cigaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here