Home Rahoto
7
0


Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shattima ya jagoranci jana’izar Alhaji Abubakar Alhaji da ya bar duniya yana da shekaru 88 bayan jinya da ya yi a asibitin Abuja.

An yi masa sallah a gaban mai martaba Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar da aka gabatar a babban masallacin Jumu’a na Sarkin Musulmi Muhammadu Bello dake harabar gidan Sarkin Musulmi a birnin Sakkwato da Marecen Alhamis.

Tawagar gwamnatin Sakkwato ƙarƙashin jagorancin mataimakin Gwamna Idris Muhammad Gobir ne suka tarbi baƙin da suka hallarci Sallah domin Gwamna baya gari.Margayi Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki da Sardauna ‘yan uwa ne na jini in da suke yaya da ƙene ne jinin Usman Danfodiyo ne.
Alhaji Alhaji an haife shi cikin iyalin Muhammad Sani haka ma ana kiran sa da Alhaji Alhaji domin an haife shi a ranar Sallah Babba(Layya) a lokacin da mutane ke wurin aikin hajji, ana kiransa da Sarkin Shanun Dogondaji, ya fara Sikandarensa a Kano daga baya aka maida shi Kwalejin Gwamnati ta Katsina.

Ya tafi kwalejin ciniki ta Bournemouth da jami”ar  da karatu ta Berkshire in da ya samu digiri kan Political Economy.

Alhaji ya yi kwasa-kwasai a makarantar horar da al’umma ta Hague da IMF a Washington.Ya fara aikin gwamnati a shekarar 1964, ya zama mataimakin Sakatare a ma’aikatar kuɗi, bayan ya tafi wasu kwas da ya dawo aka tura shi ma’aikatar kula da Kamfanoni nan ya zama babban mataimakin Sakatare a 1971, an sake mayar da shi ma’aikatar kuɗi a 1975, ya zama babban Sakataren a ma’aikata Kasuwanci a 1978 da 1979, aka sake mayar da shi ma’aikatar kuɗi. Ya shiga lamarin Najeriya da masu biyar bashi na waje, ya shiga cikin tawagar yarjejeniyar Nijeriya Lome ll.Alhaji an mayar da shi Ma’aikatar tsare-tsare kafin Shugaban ƙasa Janar Babangida ya ɗaga shi zuwa ƙaramin ministan Kasafi da tsare-tsare 1988 zuwa 1990 da 1991 ya zama ministan Kudi daga baya. Ya zama babban jekada Ambasa zuwa Ingila(United Kingdom).Margayin ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here