Home Labarai
12
0

Tsaro: Gwamnatin Sakkwato ta yaye jami’an tsaro na Marshal 1,550


Gwamnatin jihar Sakkwato ta yaye jami’an tsaro na Marshall su 1,550 a yunkurinta na inganta harkar tsaro da kare rayuwar mutane a jiha.

Jami’an suna da rukuni guda hudu, kula da muhalli da tsaro da sirri da harkokin kula da ababen hawa, an ba su horo na sati takwas, in da a karon na farko aka sanya mata a cikinsu. 

Gwamnan jihar Ekiti Mista Biodun Oyebanji ne ya kaddamar da rukuni na biyu na dakarun a matsayin babban bako a wurin bukin ya nuna farincikin yadda Gwamnan Sakkwato ya ba shi damar zuwa jihar  a karon farko.

A cewarsa bayar da horo ga jami’an Marshal ya bayyana yadda ake son samar da zaman lafiya da tsaro da hadin kan kasa.

Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu a wurin ya da tabbacin samar da duk wani abu da jami’an ke bukata kama da ababen hawa da na’urar magana da duk wani abu da zai taimakawa aikinsu domin samun nasarar aikin, za a kuma tura dukkan jami’an a kananan hukumomi a 23 kowane jami’i za a aje shi a mahaifarsa domin ba da gudunmuwa.

Gwamnan ya nemi jami’an su hada kai da jami’an tsaro na kowane bangare domin ganin an tsare rayukkan ‘yan kasa.Gwamnan ya ce “duk abubuwan nan da muke yi don kara karfafa jami’an tsaron mu ne, ‘yan uwana jama’ar Sakkwato kamar yadda kuka sani tun sanda Allah ya ba mu wannan jagoranci mun cigaba da yin abubuwa da dama domin ganin an samar da tsaro, mun yi duk abin da yakamata mu yi, iyakar yin mu domin ganin tsaro ya samu, mun kai doka a majalisar dokoki domin amincewa duk wani Infoma da yake ba da sirri ga ‘yan ta’adda shi ma a dauke shi matsayin dan ta’adda.

“Harkar tsaro ba ta tabbata sai da taimakon kowa ya zama wajibi a gare mu zama wuri daya don samar da tabbataccen tsaro a fadin jihar Sakkwato,” a kalaman Gwamnan Sakkwato. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here