2027: Kamfe Da Hatsaniya
A kalla kusan wata biyu ya rage a gudanar da zaben 2027 akwai yawaitar hatsaniya a harkokin kamfen da jam’iyu ke gudanarwa a fadin Nijeriya.
An shata yin zaben shugaban kasa da sanatoci da ‘yan majalisar wakillai a 16 ga watan Junairun 2027, sai gwamnoni da ‘yan majalisar dokokin jihohi a a 6 ga watan Fabarairun 2027.
A kwanaki bakwai da suka gabata kusan jiha bakwai ne ake ta fama da rigima siyasa na baya bayan nan shi ne na Lagos in da magoya byaan NDC suka samu rauni.
Haka aka samu hatsaniya a wurin gudanar da zaben fitar da gwani na APC a Zamfara.
Wasu jihohin da lamarin ya faru akwai Edo, Delta, Gombe da Cross Rivers.Lamarin yafi kazanta jihohin Katsina, Kebbi, Enugu, Ekiti, Ondo, Ebonyi, Osun da Nasarawa, ana ta samu hatsaniyar siyasa a wuraren.






