Home Siyasa Ƙaratowar zaɓe ne ya hana Tinubu aiwatar da dokar haraji da za...

Ƙaratowar zaɓe ne ya hana Tinubu aiwatar da dokar haraji da za ta ƙara matsar da talaka—-Kwankwaso

18
0

Sen Rabi’u kwankwaso Yace karatowar Zaɓe ne ya hana Tinubu ƙaddamar da dokar Haraji domin yasan zata cutar da talakawan kasa amma bayan zabe idan kuka bari Ya zarce sai ƙaddamar da ita

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jinkirta fara karɓar haraji bisa sabbin dokokin haraji da aka amince da su, saboda fargabar rasa zaɓen 2027.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen NDC a Jihar Jigawa, wanda aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar.

Ya ce duk da cewa an riga an amince da ƙudurin dokokin harajin tare da mayar da su doka, gwamnatin tarayya na nuna jinkirin fara aiwatar da su saboda fargabar illar da hakan ka iya haifar mata a siyasa gabanin zaɓe.

Kwankwaso ya yi gargaɗin cewa idan APC ta sake samun nasarar lashe zaɓen 2027, ‘yan Najeriya za su iya fuskantar ƙarin nau’o’in haraji.

Ya ce: “Da zarar sun samu dama ta biyu, Allah Ya kiyaye, ‘yan Najeriya za su sha wahala daga nau’o’in karɓar haraji daban-daban. Za su riƙa shiga gidaje suna bincike har ƙarƙashin gadaje domin karɓar haraji.”

Tsohon gwamnan Kano ya kuma yi zargin cewa shugaban majalisar dattawa ya ƙaurace wa zaman amincewa da dokar harajin ne da gangan, domin gudun kasancewa cikin waɗanda suka amince da ita.

Kwankwaso ya ce idan aka zaɓi NDC, jam’iyyar za ta soke harajin da ta kira marasa amfani, ta samar da ingantaccen ilimi tare da ɗaukar nauyin karatun ‘ya’yan talakawa.

Ya kuma buƙaci ‘yan Najeriya da kada su sake bai wa APC dama ta biyu, yana mai cewa sake zaɓen jam’iyyar zai jefa makomar ƙasar cikin haɗari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here