Home Siyasa Matsin Tattalin Arziki: Ina Gyara Ɓarnar Atiku Da Wasu—Tinubu

Matsin Tattalin Arziki: Ina Gyara Ɓarnar Atiku Da Wasu—Tinubu

17
0

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya ɗora alhakin yunwa da matsin tattalin arziƙin da ake fuskanta a Najeriya, kan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da wasu tsoffin shugabanni da suka mulki ƙasar.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC da aka gudanar a filin wasa na Adokiye Amiesimaka da ke Fatakwal, a Jihar Ribas.

Ya zargi Atiku, wanda ake sa ran zai ƙalubalance shi a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam’iyyar ADC, da amfani da kuɗin gwamnati wajen gina kansa lokacin da yake mataimakin shugaban ƙasa.

Tinubu ya tambayi yadda Atiku ya samu kuɗin da ya gina jami’a a lokacin da yake kula da harkokin tattalin arziƙin ƙasar, yana mai cewa kuɗin jama’a aka yi amfani da su wajen gina jami’ar.

Haka kuma, shugaban ƙasar ya tabbatar wa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, cewa ba zai yi nadamar goyon bayan APC a zaɓen 2027 ba.

Ya yaba wa Fubara bisa yadda ya yi haƙuri da girmama na gaba a lokacin da jihar ke fama da rikicin siyasa, inda ya bayyana cewa ya shiga tsakani ne domin ya taimaka masa.

Tun da farko, Fubara ya bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Tinubu, inda ya yi alƙawarin cewa jihar Ribas za ta samar masa da ƙuri’u miliyan uku a zaɓen 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here