Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 35

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 35

16
0

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 35📑

__📖 Cikin muryan ɓacin rai Baba umar yace, “wallahi suwaiba na rantse miki da Allah, kika sake jifan matata da sunan karuwa, toh a bakin auren ki, ke idan kina da hankali koda karuwa na aura tana shirin haifa mun ɗa ko ƴa, ya kamata ki jefe ta da sunan karuwa? Ni na ɗauka idan kinji mai ƙiranta da wannan sunan sai inda ƙarfinki ya ƙare, amma kece da bakinki kike faɗa? Gaskiya banji daɗi ba, kuma bana son sakeji da ga yau”, ya karasa maganan yana miƙewa tsaye ya wuce toilet ɗin da yake parlourn, don wataran yafi son shiga wurin, especially idan dare ne, don yasan lokacin babu baƙon da zai shigo ballantana yaga fitowan shi.

Suwaiba kuma haɓa ta riƙe tana mai matuƙar jin tsoron furucin Baba umar, gashi ta sha dukan tsiya, ga rashin iya maganan ta da kula da miji ya jawu ko ta kan maganan ta ba abi ba, juyawa tayi ta dubi ƙofan ɗakin Aunty hauwa da ta leƙo ta ƙurawa suwaiba ido tana murmushi, a hankali Aunty hauwa ta ƙaraso cikin parlourn ta zauna gefen suwaiba tana ta jujjuya idon ta tana rausaya jikinta, ta gefen ido ta kalli suwaiba tana murmushin iskanci tace, “suwie darling! Wato ke baki san ta yadda ake bariki ba kuma kice zakiyi bariki? ae ba’a kishin banza yanzu, an waye suwaiba, ana kishi ne na nuna kulawa da miji da tsafta da kyautatawa, bawai banzan kishi irin naki ba, idan kince irin shi zamuyi toh ina mai tabbatar miki kece a ƙasa, gara ma ki saduda mu zauna lafiya, don ni babu mugunta a zuciyata, idan kace zaka shiga gona nane kawai zan taka maka burki iya sanin ka, so ina mai jan kunnen ki da babban murya suwaiba, idan kunne yaji toh jiki ya tsira”, bata jira mai suwaiban zata faɗa ba ta wuce ɗakinta ta barta tana share hawayenta.

Wani irin kulawa Aunty hauwa ta ke nunawa Baba umar, har sai da yakai ranan da zata karɓi girki dole sai ka gane rawan kan shi, don ko zaman parlour ba ya iya yi, a haka har hutun Aunty hauwa ya ƙare, tazo gidan mu yakai kusan sau biyar, wani lokacin Ummi zata je damu gidan mu ɗauki Aunty hauwa muje shan iska cikin lagos, wataran muje gidan abokan su Abba da Baba umar, a haka har Aunty hauwa ta koma Narabi, ko kwana biyu bata wuce ba ta koma school.

Ten october 1980, shine ranan da aka haife mu nida Hassan, yau kuma ya kama 10 october 1985 Aunty hauwa ta haifi ɗiyar ta mai masifar kama da ita, lokacin da Aunty hauwa ta haifi ɗiyarta munyi tsalle da murna nida Hassan badon komai ba, sai don jin daɗin date of birth ɗinmu yazo ɗaya da sabuwar ƙanwar mu, ranan Aunty hauwa saida ta gajji da amsan wayan mu, don ko ta ajiye bata wuce 1hr zamu sake ɗauka muce, “Aunty ki saka mana kukan sistern mu”, ita dai dariya kawai ta keyi, a dole sai ta ɗan bugi babyn ta fara kuka.

Munajin muryan kukanta zamu fara tsalle nida Hassan muna tambayan Aunty, “Aunty don Allah muryan babyn irin na waye a cikin mu”? Dariya Aunty ta keyi tace, “muryan kukanta na rikici irin na Babana hassan ne, idan kuma tayi muryan wasa na Aminina Hussain ne, saboda haka muryan kune dukan ku”, dariya zamuyi tayi muna murna, chan kuma sai Hassan yace, “Aunty dani take kama ko”? Nan ma dariya Aunty hauwa ta keyi tace, ” toh maganan gaskiya baby kam da Ummi ta ke kama”.

Mu kuma jin tace da Ummi take kama sai duk muka fara tsalle muna cewa, “yehhhh Ummin mu tayi baby mai kyau”, ita dai ummi da ta gajji sai ta karɓe wayanta tama kashe gaba ɗaya ta ɓoye.

Umma ce ta tafi zama wa Aunty hauwa, inda Goggo da Addagana sukaje suka ga baby suka dawo, Kawu Auwal ma da Aunty ummi sunje sunga baby tare da Uncle Baba, ranan da sukaje kuma ranan muka zo tare da Ummi ana sauran kwana uku suna, Uncle baba yana kallon babyn yace, kai wannan yarinya tayi kwaɗayi kam, dubi bakinta ɗan mitsul kaman ba ita bace tazo ta cinye mana ayan gidan mu, zuɓun mu, ferfesuop, gwaten tsaki, kai Bappah da su Mama sun kashe kuɗi kam a ɗan wannan mutsilan bakin, na ɗauka yara uku ne zasu fito domin irin cin da tayi ashe ɗaya ce me kama da uwa ma bada mama”, ya juya yana kallon ummi yana dariya yace, “Adda Ummi nah! Duk da kuna kama da wannan mai kan zabuwan”, ya nuna Aunty hauwa da bakin shi yana dariyan neman tsokana, ita kuma sai hararan shi ta keyi tana kallon kawu auwalu akan ya saka baki, shi kuma sai kallon su ya keyi yana murmushi, don shi kafin kaji bakin shi a abu toh sai abu ya ɓaci, don dayawa ana cewa na ɗauko halin shi, amma har gara ni sau babu iyaka ina magana fiye da shi, uncle baba ya cigaba da maganan shi yana dariya, “wato ummi yarinyar nan sak ke, kaman ke kika haifeta, wallahi kyaun nan dai naki ta ɗauko, don uwar ta kanta yayi kojeje haka kaman na ƴan gabɗori”, ya ƙarisa yana dariya, kowa da yake parlourn dariya yayi, ita kuma Aunty hauwa hararan shi tayi tace, “kuma wallahi kada kazo mun ranan suna, don ban gayyace kaba, kuma ƴar nan ko ta girma bazata ce maka kawu ba, kana ji kana gani zata ce maka Baba ƙarami mai kan kwakwa”, ta faɗa tana hararan shi, hattah umma da tashigo da abinci wa su Ummi sai da tayi dariyan maganan Aunty hauwa, nida Hassan kuma duk wanda ya ɗauke ta sai mu koma kusa da shi muna taɓa yatsun ƙafan ta, Ummi ta karɓi babyn a hannun Uncle Baba tana murmushi tace, “naga ranan da zaku girma wallahi Baba, daga kai har hauwa ban san waya fi shiririta ba”, ummi ta ƙurawa babyn ido tana duban ta da murmushi, chan ta dubi Kawu auwal tace.

“Auwal dubi ƴar nan babu ƙaryah fa gaba ɗaya da ni take kama, nifa ko su Hassan dana haife su a cikina toh wallahi banji son su ba yadda nake jin son wannan yarinya, don Allah dubeta tun tana ƙarama kamanin ta ya nuna sosai, wannan kam idan ta girma za a daina cewa muna kama da hauwa trouble, sai dai ace ga mai kama dani”, Ummi tana dariya tace, “hauwa wannan yarinyar kam ni zan raine ta, don gaskiya ta shiga raina matuƙa, ke kuma na sanki da dauriya zaki haifu wasu kwanan nan”, ta faɗa tana duban Aunty hauwa da ta buɗe baki tana kallon ta, kawu auwal yana dariya yace, “maganan ki dutse babbar ya uwa, nima ina bayan ki, kinga su twins sun samu sister”.

Kallon Aunty hauwa uncle Baba ya tsaya yanayi, yana jiran yaji abinda zata ce ta tofa, Aunty hauwa ta kalli ummi tace, “gaskiya Ummi kinga wannan ƴa macece, ki bari sai na haifi namiji sai na baki ki haɗa ki zama maman ƴan maza, nikan ina son wannan ɗin, amma kiyi fatan Yayah auwal su haifi ƴa mace sai su baki, don kinga Aunty ummi sai wani ɓoye cikinta ta keyi cikin hijabi, bata san sa’idawa har sun gani sun sanar dani ba”, ta faɗa tana dariyan uncle baba daya buɗe baki yana matan kallon marar sirri.

“zakuji da shi ae da gulmar ku, kullum kuna ɓatar da mutane akan ku baku zaman lafiya, kuma wallahi Adda Ummin mu, duk gidan mu babu masu gulma na haɗin kai kaman wanda sukayi gware suka zo duniya irin Hauwa da Baba ƙarami, babu garin Allah da zai waye basu ƙira junan su ta waya sunyi gulma ba, kuma duk halin da hauwa ta keyi shiyake ƙara ɗaurata akan network”, Kawu auwalu ya faɗa yana duban su yadda suke ta dariya har da tafawa.

Daidai lokacin Baba umar ya shigo suka gaisa da su ummi, inda ummi take gaya mishi yadda sukayi da Aunty hauwa akan babyn, yana murmushi yace, “wallahi babbar ya nidai na baki uwata duniya da lahira, duk ranan da hauwa ta yaye ta ki karɓeta, ko ina raye ko bana raye, na baki ita don na yaba da karamcin ki, kuma wallahi naso saka miki takwara da yarinyar nan, toh sai mahaifina yace yana so nasaka sunan mahaifiyata, amma insha Allahu idan Allah ya sake bamu ɗiya mace toh tabbasa, NANA FATIMA zan saka, amma wannan ma bai ɓaci ba in sha Allahu na baki ita duniya da lahira”.

Gaba ɗaya jikin kowa yayi sanyi, murya a hankali Aunty hauwa tace, “insha Allahu ma hero kana nan sai munyi ƴaƴa goma sha biyu tare da kai, kuma insha Allahu wannan yarinya shayar da ita kawai zanyi, ina yayeta zan bawa Ummi nah, don nima ikon tace ballantana abinda na haifa”, hawaye ta share a idon ta ta dubi Ummi da ita ma lokaci ɗaya jikinta yayi sanyi, “Ummi na miki alƙawari ko nuna so bazanyi wa wannan yarinyar ba, kuma zan nuna miki ni ɗin ƴar halak ce, domin zan kawar da kaina akan ɗiyar nan, dama ni Hassan da Hussain ne nawa ƴaƴan”, ta faɗa tana share hawayen ta.

Ranan sunan ƙanwar mu taci suna mai girma da daraja, wato sunan uwar muminai, NANA AISHA ƴar uwar da babu irin ta a duniya ƴar’uwar da muke mata son da bamuyiwa kan mu, wanda muka kasance ƴan biyu kyautar Allah, amma bamu son junan mu yadda muke son ƙanwar mu Nana Aisha, wanda yawan ci munfi ƙiranta da Aisha”.

anyi suna da kwana biyu mukaje misau muka gaida su Bappah, muka ƙara kwana biyu tukun kawu auwal suka rako mu jos domin mu shiga jirgi mu tafi lagos, mun tsaya a Narabi muka sake ganin sistern mu Aisha, muna cikin farinciki muka shige airpot muka tafi lagos.

Aisha tana da shekara ɗaya Ummin mu ta haɗa mana birthday party a lagos, lokacin Aunty hauwa ta gama school ta dawo lagos da zama, Ranan kaman baza mu mutu ba don daɗi, gashi Aishan mu tana tafiya abin sha’awa, ga wani kyau da gashi da yarinyar ta ke dashi, wanda kowa ya ganta sai ya ƙara ganinta, kaya iri ɗaya Ummi ta saya mana, wani wandon jeans ne Blue da wasu rigunan polo Red colour, sannan Baba umar ya saya mana wasu kuma, namu baƙin wandon jeans da blue riga, ita kuma Aisha blue skirt na jeans da pink riga, ranan iyayen mu sun kashe mana kuɗi ba kaɗan ba, Aunty suwaiban Baba Umar babu yadda ta iya da masifan Aunty hauwa, dole ta dawu kaman wata yarinyar ta don tsoro, duk inda Aunty hauwa ta juya ta haka take juyowa, sai dai kuma Aunty hauwa babu matsalan cutar da mutun, saida buhun bala’i kawai, shima idan an taɓo ne, mun samu kyaututuka kam babu iyaka.

Mama da Addagana da su kawu auwalu da uncle baba da Aunty ummi da Ɗanta wanda baifi 5month ba mai sunan Bappah, ana ce mishi Affan, duk sun zo mana lagos, daɗi muke ji kaman babu gobe, haka akayi ta pictures ana raha, da dare ranan Aunty hauwa tace ita a gidan mu zata kwana, domin ganin ƴan uwa duk sun haɗu, haka Baba umar ya amince mata, akan tayi kwana biyu idan su Mama da Adda sun tafi zaizo ya ɗauke ta, abin daɗin kuma aranan ya bawa Aunty hauwa da Aunty suwaiba kyautar mota, Aunty hauwa ta ɗauki Ash, Aunty Suwaiba kuma ta ɗauki black, duk muka haɗu muka taya su murna, baby Aishan mu kuma ya bata kyautan gidan gonan shi da yake garin Narabi, sannan ya buɗe mata account ya saka 5million a ciki.

Duk wannan kyaututtukan a gaban Abban mu akayi shi, bayan an ƙira baban narabi an sanar mishi, Baban Narabi yana dariya yace, “Toh godiya muke Baban mu, domin wannan kyauta da kayiwa uwargida na wani da ita kayiwa, domin zan cigaba da riƙe mata har sai ta girma, idan mai sonta ya fito sai muyi shaɗi da shi, wanda yaci gasan ya aureta ya riƙe mata, don nasan ni zan cinye gasan”, ya faɗa yana dariya, duk su Abba ma dariyan sukayi domin a handsfree Baba Umar ya saka.

Aunty Suwaiba tana dariya bayan ankashe wayan tace lallai muƙi wayon Baban Narabi, wannan golden girl ɗin ƴar mun ae sai mun darje mazan duniyan nan kafin mu yarda mu bata mijin, ina zata kai Baban namu alokacin”? Kowa dariya yayi ana kallon Aisha da ta ɗale kan cinyan Babanya sai ja mishi gashin gemun shi ɗan kaɗan da ya ajiye ta keyi, shi kuma sai bin ta da dariya yakeyi.

Chan kuma ta koma tana jan gashin kanshi sai gwalamniyan surutu ta ke mishi yana ta dariya, yana duban ta da murmushi a fuskarshi, batare da ya dubi idon kowa ba yace, “Gambo” Abba ya ɗaga kai yana duban shi batare da ya amsa ba, Baba Umar yayi murmushi yana kan wasa da jelan gashin Aisha yace, “Gambo duk duniyan nan idan ka cire Baban narabi da uwata da ta daɗe da rasuwa, toh Allah bai taɓa sakamun son abu ba aduniyan nan irin Aisha Humairah, ina sonta har ban san irin shi ba, wataran idan suna bacci da uwar sai na tashi basu sani ba, na ɗauketa nayita kuka, domin ina jin ajikina kaman bazata samu gatan mahaifi ba, kaman bazan daɗe tare da ita ba, sai inajin tausayinta hala ko ita kaɗaice rabo na? Ko bazata samu ɗan’uwa ba? Hala ita kaɗai zata kasance abinda zan haifa, amma idan na tuna tana da kai tana da Ummi, tana da Hassan da hussain, sai na samu nutsuwa a zuciyata, domin nasan bazata taɓa maraici ba a duniya, bazata taɓa kukan rashin ƴan’uwa ba, domin Hassan da Hussain sun ishe ta rayuwa, ga kuma Affan ta samu ƙanin ta abokin wasan ta, yadda Hauwa da Baba ƙarami sukeyi haka ita ma zata samu nata ƴan’uwan”, ya faɗa fuskan shi da murmushi yana share hawayen idon shi kuma.

Jikin kowa yayi sanyi gaba ɗaya a parlourn, a hankali Aunty suwaiba ta saka hannu ta ɗauki Aisha tana share hawayen idon ta tace, “narasa mai yasa kake yawan irin wannan zan tukun kwanan nan, nifa har kasa ina jin tausayin kaina da kuma hauwa da wannan yarinyar da Allah ya bamu kyautanta, duk da ka ƙwace mana ita ka kyuatar, amma bamuyi fushi ba, muna fatan baɗi hauwa ta haifa mana ƴan biyu, ta bani ɗaya ta riƙe ɗaya, bayan wani shekara ta kawo mana ƴan uku, lokacin kuma ni zan ɗauke su dukkan su, amma idan kana wannan furucin sai kasa jikina yana sanyi, faɗuwar gaba na yana yawaita, tsoro yana kamani, ina ji ajikina kodai bani da rabon riƙe ɗan ka a hannuna ne har na koma ga ubangiji”? Ta faɗa tana share hawayenta.

Juyar da kai Aunty hauwa tayi tana kuka a hankali, murya yana rawa tace, “nidai ka daina faɗar mun da gaba na hero, muna nan tare har tsufan mu insha Allahu, ke kuma suwaiba ki daina mun fatan haihuwa dayawa, kema insha Allahu baɗi zaki haifa mana ƴan biyun, kidai na fitar da rai daga alkhairin Allah, kuma ni nama fasa kwanan ku tashi mutafi gida kawai, idan yaso mubar musu Aishan a gidan su ni nama yaye ta daga yau,” ta faɗa tana miƙewa.

Baba umar yana dariya yace, “wallahi baki isa cire mun uwata a nono tana shekara ɗaya ba, ke hauwa kifita a idona fah”, ya faɗa yana dariya, sannan ya dubi Ummi da ta sunkuyar da kanta tuntuni tana dariya yace, “Babbar ya uwa, wallahi kada kibari koda wasa Hauwa ta cire mun uwa a nono, kuma ko wani irin tashin hankali ne zai sameta toh ta maida hankalinta akan uwata”, ya faɗa yana miƙa hannu wa Abba da yakasa cewa uffan sai kallon kowa yake yi kawai.

Aunty suwaiba ita ma miƙewa tayi tana dariyan hauwa tace, “ke kuluwa yaufa babu inda zaki bimu, kima je ki gyara wurin kwanciyar da kyau yau a gidan nan, kibar ni yau nabi mijina, ke kuma bayanzu ba, ki zauna ciki ƴan’uwanki kusha hira, ki kula mun da sanyin idona kuma da kyau, ki bata nono tasha ta ƙoshi bayan kin mata wanka ta huta gajjiyan yau”, sannan ta ɗago Aisha ta sake duban Ummi tace, “Ummi naso ace idan ɗiyata ta girma na haɗa ta aure da Hassan ko Hussain, amma kuma Babanta yace su ɗin ƴan’uwanta ne, ke kuma uwace, toh na haƙura ina yiwa hasken zuciyata addu’an Allah ya bata miji nagari jarumin gaske, wanda zai sota da amana, saboda bana son Aisha tasan ba Ummi bace ta haifeta, kuma bana son ta san su Hassan ba ƴan’uwanta ciki ɗaya bane, saboda haka Ummi da Abba mun bar ku da ɗawainiya Allah ya baku ikon riƙewa, ke kuma Hauwa kiyi haƙuri da rayuwa ki rungumi kowani irin ƙaddara da hannu bibbiyu a rayuwar ki, ki yafe mun rashin fahimtar ki danayi a baya, kuma insha Allahu zaki haifo mana wasu yaran masu irin kyaun ki da sakalcin ki da wannan rikici da yangan,” ta kara faɗa tana guge hawayen ta tana dariyan Aunty hauwa da ta tashi ta rungumeta tana kuka, daga baya ita ma Aunty suwaiban kukan ta fara.

Ganin haka sai Baba umar yazo ya jawo hannun Aunty hauwa yana dariya yace, “bari muyi waje na rarrashi kayata kafin ku fito,” ya jata sukayi waje, parlourn kuma duk anyi tsit, sai sautin muryan kukan Aunty suwaiba ,Ummi da uncle Baba da Aunty Ummi da wata ƙanwar Baba Umar da tazo daga jos kawai akeji, wanda ita ma a wurin su Aunty hauwan zata kwana, sai da suka bawa Baba Umar da Aunty hauwa good 30minutes tukun suka bi bayan su, lokacin nida Hassan duk mun yasu a parlourn munyi bacci, ɗayan gefen ma Affan yayi bacci acan ɗaki wurin su Mama wanda basu san me akeyi ba a parlourn, amma Aisha idon ta biyu tana rungume jikin Aunty suwaiba, a haka suka fita waje inda su Aunty hauwa suke zaune a mota ita da Baba Umar yana ta aikin rarrashinta.

Kiss Baba Umar yayiwa Aisha bayan ya miƙa ta wa Aunty hauwa, sannan ita kuma ya ɗan lakuce kumatun ta yana murmushi yace, “bye bye my heart”! Aunty suwaiba tana tsokanan ta tace, “hauwa yau kam na miki wayo na tafi da miji na, zamuje muyita shan soyayyah babu ke, yau har rawan da kika taɓa mishi ina kallon ki ban kula ki ba zanje na mishi”, ta faɗa tana dariyan Aunty hauwa da ta ke hararan ta da wasa, a haka suka shiga mota suka tafi suna ta ɗaga musu hannu.

Dama su Aunty suwaiba basu bar gidan mu ba sai wajen 12:00pm na dare, toh Ummi suna dawowa aka tattare gift ɗin da muka samu aka kai ɗakin mu, sannan kowa yayi wanka yayi shirin kwanciya, wanda Aunty hauwa ko Aisha batayi wa wanka ba, sai share hawayenta ta keyi, Ummi ce ta ɗauki Aisha tayi mata wanka ta bata cerelac ta sha, ta tafi da ita ɗakinta wurin Abba, suna nan har wajen 2:00 ita da Abba basuyi bacci ba, Abba sai juyi yakeyi, chan sai Ummi ta dube shi tace, “me ya hanaka bacci ne”?

Murmushi yayi yace, “ke mai ya hanaki baccin”? Ajiyan zuciya Ummi tayi ta dubi Aisha da ta ke ta kallon sillin ido ta nuna mishi ita tace, “ga wanda ta hanani bacci, domin nafi so tayi bacci tukun”, juyawa yayi ya kalli Aisha, a hankali ya jawo ta kusa da shi yace, “auta na me ya hanaki bacci”? Aisha ta kalle shi kaman ta gane mai yace, tana gwalamniyanta tace, “Dada” wato tana nufin Daddy, yadda take ƙiran Baba Umar da shi.

Abba zai bata amsa sai yaji ƙaran wayan shi, da sauri ya tashi ya ɗauka ya kai kan kunnen shi, bayan ya amsa Ummi taji yana amsawa da “ehh nine, akwai wani matsalah ne officer”? ya faɗa jikin shi duk rawa yakeyi, da sauri ya miƙe jiki na rawa ya ce, “INNALILLAHI WA’INNA ILAIHIR RAJI’UN” , sannan da ƙarfi yace, “Officer kuna wani asibitin ne”?

A ɗakin su Aunty hauwa kuma Aunty Ummi da take kwance gefen Aunty hauwa ta fara bacci kawai taji Aunty hauwa ta miƙe zaune da ƙarfi tace, “Wayyo Mama zuciyana yana tsinkewa, nikan mama kawai zan bi mijina, ina tsoron wani abu ya same shi”, ta tashi da sauri tajawo hijab ɗin da sukayi sallah ta saka ajikinta, tayi hanyar parlour tana faɗin, “nikan sai naje na tashi Abba ya kaini wurin miji na”, Adda zuba mata ido tayi tana kallon ta, Aunty Ummi da ƙanwar Baba Umar ma tashi sukayi suka miƙe tsaye suna kallon ta, suma daga dukkan alamu shirin binta sukeyi, Mama da sauri tace, “ke Hauwa kada kije ki tashi bawan Allahn nan, kiyi haƙuri zuwa safiya sai ya kaiki idan Allah ya kaimu”, amma ina Aunty hauwa tunin tayi parlour, wanda da sauri su Aunty Ummi suka bi bayan ta, tana fitowa parlourn kuma yayi dai-dai da fitowar Abba cikin gudu-gudu Ummi na binshi a baya a ruɗe tana tambayan shi lafiya ina zaije a cikin daren nan?

Abba yana ganin Aunty hauwa yaja ya tsaya ya ƙura mata ido jikin shi sai rawa yakeyi, itama ƙura mishi idon tayi tana kuka tace, “nikan Abba ka kaini wurin mijina nikan”, ta ƙarasa da sunkuyawa ƙasa tana kuka, rufe idon shi gam da ƙarfi yayi ba tare da ya furta komai ba, Ummi kuma sai tambayan shi ta keyi abinda ya faru?

ZAINAB IDRIS ta group ɗina mai suna MUYI NISHAƊI wannan shafi nakine kyauta na baki, kuma na cika miki alƙawarin yi miki typing mai yawa yau, da fatan zai faranta miki, nagode sosai da kulawanki gareni, da kuma book ɗina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here