Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 34

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 34

26
0

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 34📑

__📖 Murmushi Bappah yayi yana duban mama yace, “kinji abinda ɗanki yake faɗa ko”? Tana dariya ta dubi Aunty Hauwa tace, “kije ki gaida Adda ko”, tashi Aunty hauwa tayi ta nufi ƙofar ɗakin Adda, wanda ta shimfiɗa taburma tana ƙulla ayanta mai sugar.

Gefen tabarmar Aunty hauwa ta zauna, idon ta na kan ayan, ta gaishe da Adda, bayan sun gaisa ne Aunty hauwa ta saka hannu ta ɗebi ayan ta kai bakin ta, lokaci ɗaya ta rufe idon ta don tsabar daɗin da ya ziyarci ƙwaƙwalwarta, ganin haka Adda ta ɗago wani ledan ta ƙullu mata mai yawan gaske ta miƙa mata, gyara zamanta tayi a gefen Adda ta maida hankalinta kan cin ayan.

Adda tana gama ƙullawa ta dubeta tace “ko zakici rogo”? Ido Aunty hauwa ta ɗago tana kallon Addan cikin nutsuwa tace, “dama ki soya mun shi ya koma ƙosan rogo”.

Tashi Adda tayi ta ɗauko rogon ta saka attaru da ajino da albasa ta kirɓashi yayi laushi, sannan ta haɗa murhunta ta ɗaura mangyaɗa, ta fara soya mata, lokacin kuma Mama ta fito tsakar gidan domin Bappah ya koma ƙofar gida domin fara ƙiran sallan azahar da akeyi.

Dukkan su alwala sukayi, bayan sun idar da sallah ne Adda ta zuba mata ƙosan rogon a pilet, tace ta karɓo yaji a wurin Mama, da sauri ta tafi parlourn mama ta karɓo yajin, a tare suka fito ita da maman, kafin kace me ta cinye rogon nan, mama ta miƙo mata zuɓu guda 2, a wurin ta zuƙe su, sannan ta yi hamdala ta wuce ɗakin mama ta kwanta akan three sitter maman, lokaci ɗaya bacci ya ɗauke ta.

Ana ƙiran sallan la’asar ta buɗe idonta da ƙaran wayanta ya tasheta, amma bata iya ta tashi ba ta jawo wayan ta kai kunnen ta, muryan Baba Umar taji yana mata sallama, hira sukayi na zuwa wani lokacin yana kuma tambayanta yanayin jikintan, haka dai suka ɗan ɓata lokaci kaɗan, sannan ta tashi ta fito domin yin alwala.

Tana idar da sallan mama ta shigo ido ta ƙura mata ganin ta sunkuyar da kanta ƙasa tana jan charbi, a hankali ta ɗago suka haɗa ido da mama.

“Hauwa ga gwaten tsakin an kawo miki, amma ina ga bayanzu zakici bako?” murmushi Aunty hauwa tayi tace, “yanzu kai mama, kinji wani irin yunwa dana ta shi inaji kuwa”?

Mama ko da sauri ta jawo kulan ta ɗauko pilet ta miƙa mata, wani murmushin daɗi Aunty hauwa tayi, ta ɗauko ta zuba cikin pilet ɗin, sai wani ƙamshin gyaɗa yakeyi, ga tantaƙwashi rututu a ciki, Aunty hauwa dariya tayi tace, “Allah sarki hajiya umma, irin wannan daɗin yau ina zan kaishi”? Sannan ta dubi mama tace, “mama kada abawa kowa duk zan cinye zuwa anjima, don nasan Baba ƙarami yana zuwa ya gani toh sai wani ikon Allahn, don sai yaci”, ta faɗa tana ɓoye coolern a bayanta.

Dariya mama tayi tace, “muma umma ta mana coolern mu daban, kuma Baba kam ae shi ya kawo, babu yadda banyi da shi bama ya tsaya yaci, amma yaƙi yace pepesoup ɗin kayan cikin kawai yake jira, amma wannan kam ya bar miki”.

“Chabb ɗi jam, mama kada ma kibashi, ni nafi son saifa da hanji ma kawai, idan akwai yaɗi a ciki ki bashi mama”, ta faɗa tana kai loman gwaten, kallon mama tayi tana murmushi tace gaskiya umma badai iya kwamacalan girki ba kam, zwaii kenan”, ta faɗa tana maida dariyanta.

Hararanta mama tayi, “da yake ta rufa miki asiri ta farfaɗo da ke ae dole ki faɗi haka, amma akwai gobe zan ce kada ta dafa miki komai ta barki da halinki”, dariya dukkan su sukayi.

Zuwa dare mama har ta mata pepsoup ɗin, ga wani bread muƙeƙe da Bappah ya sayo mata, tana zaune a gefen Adda tana ci, sai zuba santi ta keyi, Baba ƙarami kuwa sai mita yakeyi wai ancika mata kwano, shi kuma an saka mishi ɗan kaɗan, Bappah yana dariyan su yace, “banda kai Baba, ae dole naka yazama kaɗan, saboda yanzu ae tana gaba da kai, kuma ita ta zama baƙuwa, dole a karramata, kai kamma da tuwo miyar kukan ka aka baka, kabarta ta cinye daɗin”, gaba ɗaya su mama dariya sukeyi, wanda Baba ƙarami kuma ya turo bakin shi gaba yana hararan Aunty hauwa.

Ranan kam anji daɗin hiran, don ana idar da sallan ishaa yayah Auwal yazo, basu sukayi bacci ba sai wurin ƙarfe sha biyu, shima don ganin hamman da Aunty hauwa keyi ne yasa suka tashi.

Kwanan Aunty hauwa uku Baba Umar yazo ɗaukanta, acikin kwanakin kuma ta zaga duk inda yakamata taje gidan ƴan’uwa, ranan da yazo duk wani abu namu na gargajiya, umma da Mama da Adda duk sun haɗa mata ita da Ummi, hattah ƴan gabɗori saida suka aiko musu da bushashshen zogale mai yawan gaske, haka Baba Umar ya tattara ta sai NARABI kwana ɗaya sukayi suka wuce lagos.

Gidan Baba Umar 2bedroom ne, dole sai ya bar mun room ɗinshi, ya zama yana bin ɗakin mune, ranan da naje ansha drammer tsakanin su da suwaiba, don firr ta rufe idonta tayita zazzaga mishi rashin kunya, a dole babu inda Aunty hauwa zata kwana a gidan, ae tana da gidan ƴar’uwa ta tafi ta kwana mana acan idan ba neman magana ba, a wurinta kenan.

Kusan dukanta Baba Umar yayi tukun ta nutsu, Aunty hauwa kuma ko kallon ta batayi ba, ɗakinta da aka nuna mata ta wuce, bata jira komai ba ta wuce toilet don yin wanka, tana fitowa ta ɗaukin wayanta dayake ta ringing, ganin sunan Ummi akai ya saka Aunty hauwa murmushi, da sauri ta kai wayanta kunnen, suna gama gaisawa, ummi ta mata sannu da zuwa, sanin halin Aunty hauwa da rashin haƙuri, suwaiba kuma da baƙin kishi, yasa ta ja kunnen Aunty hauwa sosai, dariya Aunty hauwa ta ke tayi, “Ummi kenan, kina ga daga zuwan mu mata ta so ta maida gidan kaman filin sambisa, toh nidai na yau nayi shiru saboda naga yadda mijinta zai ɗau mataki, amma wallahi! Wallahi!! Ummi zuwa gobe kam zan nuna mata hauwa’un kule mage”, Aunty hauwa ta ƙarasa faɗi tana kwashewa da dariya.

“yanzu hauwa saboda Allah kin mun dai-dai? Ina gaya miki komai haƙuri akeyi amma kina nuna mun ke baki san da haka ba? Toh wallahi naji kinyi wani abu na rashin mutuncin toh zaki haɗu da ɓacin raina”, ummi ta karasa faɗa ranta a ɓace.

Aunty hauwa dariya tayi tayi kaman bata damu ba, haka sukayi sallama kowa ya ajiye wayan.

Duk yadda suwaiba take tunanin hauwa ta wuce saninta, domin da Aunty hauwa ta buɗe buhun bala’inta har saida suwaiba ta daina zaman parlour, kullum sai dai kaji ta a ɗaki ta ƙure volume ɗin wayanta tana jin waƙa, wai don ta ɓata ran Aunty hauwa, dayake Aunty hauwa bata son hayani sai ta zama shine hanyar ɓata mata rai, amma Aunty hauwa ko kula ta batayi, watarana, sai da tabari suwaiba ta cikata da ƙaran waƙe-waƙe ta gama, ta fito zata shiga kitchen ɗaura abincin rana, da yake girkin suwaiba ne, wanda sukeyi kwana ɗaɗɗaya, Aunty hauwa ta ɗauko wani wayan cavel, ta samu suwaiba a gadon baya ta dinga tsula mata tana, “ni sa’ar kice da zan ce na hana ƙure vulome a gidan nan amma zakiyi kunnen uwar shegu”, suwaiba irin ƴan firit ɗin nanne masu ƙaramin ruwa, kuma ga ruwan ciki, amma sai neman faɗa, Aunty hauwa kuma ƴar duma-duma ce, ga faɗa inda ta shiga bata nan ta ke fita ba, sai da tayiwa suwaiba lilis, kuma tace dole ta dafa musu doya da miyan stew don yau ita shi ta ke kwaɗayi, babu yadda suwaiba ta iya haka ta tafi kitchen ta fere doya tana kuka ta ɗaura , a zuciyar ta tana ƙissama abinda zata gayawa Baba Umar idan ya dawo, don ita bazata iya da dukan Hauwa ba, don yau shi ne rana na biyu kenan, gashi Aunty hauwa sauran ta 10days kafin ta koma, ita kaman bazata iya zaman kwana goma tare da ita a gida ɗaya ba, haka tayita aikinta tana share hawaye.

Baba Umar sai dare ya dawo gida, da yake kullum sai 8:00 na dare yake shigowa, idan ya tafi tun 7:00am na safe, ko ruwa bai shaba, suwaiba ta fashe da kuka ta fara zayyana mishi irin dukan da Aunty hauwa ta mata, har da ƙari saida Suwaiba ta faɗa, shidai kallonta ya tsaya yana yi, wani zubin sai yaji kaman ya fashe da dariya, amma ya dake yace ta ƙira mishi hauwan.

Aunty hauwa tana fitowa cikin wani jeans da t.shirt mai shegen kyau, ta ɗaure tulin gashinta da wani yellow ribon kalan t.shirt ɗin, har inda Baba umar yake zaune taje ta tsuguna a gaban shi ta gaishe shi cike da ladabi, ga wani juya ido da take mishi, sai wani ƙamshin daɗi ta keyi, fuska a sake ya amsa mata yana ta duban fuskanta da yasha kwalliya, har yaso manta dalilin ƙirantan da ya saka aka mishi, don ba ƙaramin son ƙamshi ya keyi ba, amma ga suwaiba sam taƙi turare, sai tace wai yana sakata mura da ciwon wuya, haka ya haƙura da ita, iya kacinta ta guga roll-on.

Bayan Aunty hauwa ta gaishe shi sai ta gyara zamanta a ƙasa dai-dai inda ƙafafunshi suke tana mai binshi da murmushi, sai wani rangwaɗa ta keyi, gaba ɗaya ya maida hankalin shi kanta, sai jin muryan suwaiba yayi cikin kika tana cewa, “bazaka mata maganan abinda ta mun bane, ka tsaya kana kallonta”?

Kallonta yayi fuskan shi a ɗaure yace, “me kika gaya mun tayi miki ma”? Hararan Hauwan tayi tana turo baki alaman zata fashe da kuka tace, “babu abinda na mata ta kamani ta min dokan kawo wuƙa, kuma wallahi bazan yadda ba sai ka sakata ta tsaya na rama duka na”.

Murmushi mai inganci Aunty hauwa tayi, muryah ƙasa-ƙasa irin na cikakkun mata da suka san kansu a gaban miji tace, “Hero kaci abincin tukun ka huta sai ka saurari haushin da ta keyi, Allah ya huci zuciyar ka, haushi mana zance domin miji ya wuni a waje nema mana halal ɗin mu, ya dawo a gajjiye ko ruwa bai sha ba, ki haushi da ƙorafi akan kishiya? Gaskiya Suwaiba ki gyara tsarinki, ta yayah hero zai samu nutsuwa da mu? Ya dawo bamu san a wani hali yake ba mu hau kai ƙara wurin shi? Ki bari yaci abinci yayi wanka, idan yazo parlour ya xauna sai ki kawo mishi ƙaran yau ni Hauwa na dake ki da kika ce mun karuwar gwamnati, ni kuma na kasa haƙuri nayi miki dukan tsiya domin kada bakinki ya saba da faɗin mun gama karuwanci mukayi aure, kinga idan na haihu ɗanmu yaji abinda kike jifan iyayen shi da shi bazai ƙira ki da mummy ba, kuma ni nafi so yarana suce miki mummy, ni kuma mamie, Hero kuma daddy”, ta ƙara faɗi tana wani kanne mishi ido tana shafa cikinta tana ta rausayawa.

Kuka suwaiba ta fara murya da ƙarfi ta faɗi,”wallahi da gaske ki karuwar ce hauwa, domin duk wacce taje school of nursing sunan ta karuwa, kuma karuwancin kikayi ae kika aure mun miji, yanxuma shi kikeyi agabanshi, jaka karuwa kawai”, ta ƙara faɗa tana kuka mai sauti.

Rausaya kai Aunty hauwa tayi kaman zata yi kuka ta dubi Baba Umar bayan ta miƙe tsaye tace, Hero zan koma ɗaki, don bazan iya cigaba da jin kalmar karuwa da matar ka ta ke yawan jifa na dashi ba, saboda bana son hayani, nafi so kaɗan huta tukun sannan ka sanar mata yadda na kawo maka budurcina lafiya ƙalau gidanka, kuma ka…..” sai ta kasa ƙarasawa ta yi ɗakinta tana share hawayen idonta.

Juyawa yayi yana hararan suwaiba, zuciyar shi sai ta fasa ta ke mishi don jin kalmar karuwa da ta dangana matar shi mai daraja da tayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here