Ɗarikar Ƙadiriyya ta Afrika ta ayyana goyon bayanta ga sake zaɓen Tinubu a zaɓen 2027
Jagoran ɗarikar Ƙadiriyya a nahiyar Afrika, Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya bayyana cikakken goyon bayan ɗarikar ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin neman wa’adi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Sheikh Qaribullah ya bayyana hakan ne bayan naɗin Sanata Abdul’aziz Yari a matsayin Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC, yayin da tawagar jam’iyyar ta kai masa ziyara domin neman addu’a da shawarwari.
A cewarsa, Shugaba Tinubu yana da kyakkyawar manufa da hangen nesa na ciyar da Najeriya gaba, don haka ya buƙaci mabiya ɗarikar Ƙadiriyya su mara masa baya a zaɓen 2027.
A nasa ɓangaren, Sanata Abdul’aziz Yari ya ce APC ta fara tuntubar manyan malamai da shugabannin addinai a sassa daban-daban na ƙasar nan, tare da shirya tarukan tattaunawa da al’umma (Town Hall Meetings) a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
