Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 33

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 33

15
0

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 33📑

__📖 Ana haka magana ya fara ƙarfi tsakanin Aunty Hauwa da Baba Umar, domin wani so suke yiwa junan su kaman me, amma Ummi nah ita bata so hakan ba, domin tanaga kaman Suwaiba zata ce ita ta haɗa ƙanwarta da mijinta, amma koda Abba yace mata babu ruwanta, kada ta damu da maganan mutane sai kawai ta yi shiru ta bisu da addu’a.

Ranan da Aunty Hauwa ta gama hutu, Baba Umar ya matsawa Abba akan shifa dole su tafi tare da ita, domin aje anema mishi aurenta, don bada wasa yakeyi ba, kada yana chan lagos wani yazo ya ƙwache mishi ita, babu yadda Abba ya iya dole suka biyota.

Tadawo da washe gari mutanen jos sukazo har misau neman aure, babu wani wasa da hankali akayi komai cikin mutunci da dattaku, a ranan iyayen Aunty Hauwa suka bawa Baba Umar auren ta, shi kuma Baban Narabi ya sake neman a saka musu auren bada daɗewa ba, da ƙyar dai aka yadda akan idan tagama wannan year ɗin sai ayi, domin da iyayenta sun fi son sai ta gama karatun gaba ɗaya, amma haka aka tsayar da magana nan da 5month.

Ko wani ƙarshen wata sai Baba Umar yazo mata hira har bauchi, toh ganin irin rawan kan da yakeyi ne ya tunzura matar shi ta fara bori, wanda har gidan mu taje tayiwa Ummi kacha-kacha, ko kaɗan Ummi bata mayar mata magana marar daɗi ba, sai haƙuri kawai da take bata.

December Ummi suka tafi misau domin saura 1week bikin su Aunty Hauwa, daɗi nida Hassan mukeji, domin zamuje misau muci masan gidan sarkin dabji, sai murna mukeyi.

Ranan thursday Aunty Hauwa tayi walima a cikin fadan sarkin misau, a cikin wani hall mai suna GWANI MUKHTAR waliman yayi matuƙar armashi inda malamai mata kusan kala uku sukayi wa’azi, ranan friday 2:300pm aka ɗaura auren Aunty Hauwa da Baba Umar, kuma a ranan akayi wuni, ranan saturday aka wuce da ita kai tsaye chan Narabi, inda dama Baba Umar yayi gidan shi mai kyau, wanda idan sunzo suke sauƙa a wurin, gida ne mai 4bedroom, saboda haka sai aka bawa Aunty 2bedroom inda kowani ɗaki ɗaya yana kallon ɗaki ɗaya, da toilet a tsakiyan su, ɗaya aka maida mata parlour ɗaya kuma bedroom, ita ma Suwaiba haka aka mata, shi kuma Baba Umar aka bar mishi main parlour da toilet ɗin ciki don baƙi, amma ya yanke shawaran yanzu zaina bin ɗakunan su, amma idan ya samu sarari zai zo yayi ɗaki a cikin parlourn.

Baba Umar Allah bai taɓa basu haihuwa ba, domin sau biyu suwaiba tana ɓari, amma daga baya abun sai yayi shiru.

Ranan Baba Umar ya nuna murnan shi da yaga Aunty Hauwa a gidan shi, kuma matsayin matar shi, daɗin abinma suwaiba ba tazo bikin ba, saboda haka ya samu ya mori amarchin shi da Aunty har na tsawon 2weeks da aka bashi hutu, daga nan ya mata sallama ya wuce lagos, inda ita kuma sauran 3weeks su koma ajin da shekaran zasu gama, wato sauran mata 1yr ta gama, kuma ya mata alƙawarin duk bayan 2weeks zai dinga zuwan mata, haka suka rabu suna ta begen junan su.

Rayuwar babu wuya, yau Aunty hauwa sun dawo hutun first term, kai tsaye misau ta wuce, domin zata jira sai Baba Umar yazo tukun su wuche lagos, domin yace wannan hutun lagos zata je tayi, domin hutun 3 weeks zatayi, shi kuma yaga ya kamata su fara sabawa da suwaiba.

Tana shiga gidansu tayi karo da Baba wato yayanta Musa, yana ganinta ya fara dariya yana cewa, ” jama’an gidan nan ku fito kuga wata afiruwa kazar mayu”, yana dariya lokacin da Goggo hussaina ta fara fitowa yana dubanta yace, “Mama don Allah kiga ƴar ki duk ta wani fige babu daɗin kallo, sai wasu ido girkima girkima kaman na hajiya umma ƴar madara”, ya ƙarisa faɗi yana dariya domin yasan ya tsukano Mama, wato goggo hussaina, harara ta bishi da shi tana kaɗa kanta tace, “kayi damu iyayenka ba namu iyayen ba, ɗan tselanƙwa mai ƙananun ido kaman ƙaramar tocilan”, ta faɗa tana kamo hannun Aunty hauwa da ta fara zuban hawayen tsokanan da Baba yake mata, domin babu hali su zauna inuwa ɗaya da shi zakaji ya tiso ta gaba har sai tayi kuka, amma yayah Auwal ɗinta tattalinta yakeyi kaman wata ƙwai, Mama tana hararanshi tace, “zakaje gidan umman neman ɗumamen safe da kunu ae, namaka alƙawarin yau zan tura ɗan saƙo ya gaya mata irin tonon sililin da kake mata”, ta jawo hannun Aunty hauwa suka shige ɗaki, ita dai Addagana tana zaune a ɗakinta tana biya karatun ta, bata wani fito ba sai dariyan drammer su kawai ta keyi daga inda ta ke, amma har cikin zuciyarta tana jin wani iri da akace hauwa ta fige, toh komai ke damun ta? Allah kaɗai ya sani.

Tunda Mama ta lura laulayin ciki Aunty hauwa ta keyi, domin suna shiga ɗakin ta dawo da bayan kaman zatayi amai tace, “Mama kaman anci miyar stew a ɗakin nan, warin shi na ke ji”, mama da sauri ta ɗauki kwanon miyan ta fitar zuwa kitchen, sannan tazo ta ɗaga labulayen ɗakin tana duban Hauwa data faɗa kan gado ta kwanta rub da ciki, cikin kallon tausayawa tace, “buɗɗo nah mai kike so toh a dafa miki?” juyar da kai kawai Aunty hauwa tayi alaman ba tason komai.

Mama tana duban ta tace, “haka bazai yiwu ba hauwa, kinga yadda kika fita hayyacin ki kuwa? Kodai bakyacin komai ne a makarantan? Kuma kin takura kanki da karatu ko? Don Allah gaya mun me kike so kafin wannan mai neman maganan yayi gaba na rasa ɗan aika”.

Juyowa Aunty hauwa tayi tana duban mama fuska a murtuƙe tace, “Mama komai naci amai nakeyi, ni bansan me zanci ba, kawai fanta nake iya sha”, ta ƙarasa faɗi hawaye yana bin idonta.

Mama na duban ta kaman ta tayata zub da hawayen tace, “toh zakici faten tsaki”? Da sauri Aunty hauwa ta tashi ta zauna tana duban mama tace, “yauwa mama amma na gidan umma nake so, wanda ta ke saka mishi gauta”, ta faɗa tana tasowa tayi parlour wurin fridge ta buɗe tana kallon ƙullin zuɓun da mama takeyi na sayarwa, har ƙasa ta zauna tukun ta ɗauki leda ɗaya mai sanyi ta ɓula ta zuƙe shi, mama kuma tayi waje tana ƙwala ƙira wa Baba ƙarami, sannan ta dawo ta nemi kujera ta zauna ta ƙurawa Aunty hauwa ido da ta ɗauki leda na biyu ta ɓula tana wani lumshe ido tana sha.

Baba ƙarami ya ɗaga labulen ɗakin bayan yayi sallama mama ta amsa, idon shi ya sauƙa akan Aunty hauwa da take shirin ɗaukan leda na uku tasha, da karfi yace, “kutt hauwa inace dai kin bada kuɗin tukun kike sha bawai kinga na bati ba ko”? Ya faɗa yana ƙara sowa cikin ɗakin baki a buɗe yana kallon mama akan tayi magana.

Bappah ne ya shigo gidan da sallama, yana dariyan halin Baba ƙarami ya ƙaraso ƙofan mama yana cewa, “kaidai baba ina ruwanka da tambaya, kasan ko duk zoɓon friedge ɗin ma ita aka yi”? “caɓɗi jam, amma ko nima dole nasha ɗaya don ita har uku fa take sha Bappah”, Baba ƙarami ya faɗa yana kallon idon mama da take binshi da harara.

Yana dariya ya karkata kanshi wurin mama yace, “mama gani ina zanje miki”?

“kaje gidan umma kace ina son faten tsaki mai gauta wa Hauwa, yanzu ta dawo daga makaranta ta kasa cin abincin mu, gwaten kawai ta ke son cin kaji”.

Juyowa hauwa tayi ta gaida Bappah daya nemi wuri gefen mama ya zauna yana dubanta da tausayawa yace, “bakiji daɗin jikin bane baɗɗo nah? Duk kin rame kin wani ɗashe gaba ɗaya kaman bakida jini? Me kike son ci nasaya miki”? Bappah ya ƙarasa faɗi shima yana duban ta da tausayawa.

“Bappah ferfesun kayan ciki nake so”, ta faɗa tana kwanciya akan ledan tsakar parlourn Maman, “kutt amma hauwa kin tunkuɗu rikici wallahi, ke kaɗanki kin shanye zuɓu leda uku, gashi yanzu kinsa za a haɗa tsuhuwa da aikin yin gwate, a haka ma mai gauta wanda da ƙyar idan umma bata sake cillani kasuwa ba, yanzu kuma kin matsawa bappan mu ya sayo mana kayan ciki a dafa mana, haba hauwa cikin mu ae baxai ɗauki abinci dayawa ba”, ya faɗa yana fita da sauri a ɗakin yana dariya, domin irin kallon da mama ta ke mishi kaman zata mare shi, yana tsayawa a tsakar gidan ya kwaɗawa Addagana ƙira yace, “fito kiga halin wariyar da mama da Bappah suke mun, don Allah Addagana nima ki saya mun kazar alka mana na huce”, fitowa tayi tana kallon shi tace, “nikan ba aikanka akayi bane Baba”? Addagana ta tambayeshi.

Haka ya fita yana cewa daga nan zan leƙa gidan yayah Auwal nace mishi zizar ƴaƴa fa tazo, gida ya kache me da girke girke, shima ya saka ƴar lukutan matar shin nan ta dafa nata ta kawo”, yana dariya ya fita a gidan.

Da yake anyi auren hauwa december, febuary akayi na yayah auwal, da matar shi da takasance ƴar bappan su ce, Ummi kyakkyawar bafulatana da suke yanayin kama da Yayah Auwal.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here