NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼
@wattpad AuntyNice.
SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI
SHAFI NA 30📑
__📖 A daren Abbu ya ƙira Daddy ya mishi bayani, hankalin Daddy na a tashe ya ƙirani, “Humairah nah kimun bayanin da zan fahimta, kina cikin ƙoshin lafiya dai ko? Kinaga babu wani matsalah na zamanki a gidan kafin na zo”? Duk cikin rawan jiki da tsoro Daddy yayi mun tambayoyin.
Share hawaye na nayi, na ƙwaƙulo murmushin ƙarfi da yaji na ɗaura shi a fuskana, tukun na amsa mishi a cikin nutsuwa, don bana son hankalin shi ya ƙara tashi, “Daddy na babu komai da ya faru, Allah ya kiyaye kuma ina cikin tsaro sosai yanzu, ka kwantar da hankalinka Daddy nah, yaushe zakazo”? Na ƙarasa tambayan cike da rauni a maganan nawa.
Ajiyan zuciyar Daddy naji, chan kuma yace, “Gobe insha Allahu zan taho, domin a yanxu har na neme wani egent a Abuja ya bani tabbacin gobe akwai jirgin da zai tashi kuma zai san yadda zaiyi na samu mu taho, don Allah ki kwantar da hankalinki, idan nazo ma kawai zan taho da ke Berselona ki ƙarasa hutun ki tare da ni kinji sweet heart”.
Har mun fara bacci nida Amaal sai mukaji ana knocking ƙofan mu, a razane muka tashi dukkan mu, da yake yau Ummi tace mu rufe ƙofan, mu daina barinshi a buɗe, a tsorace Amaal tayi ƙarfin halin ta tambayi waye ne?
Muryan Ummi mukaji tana ƙiran Amaal ta zo ta buɗe mata ƙofan, da sauri Amaal ta sauƙa taje ta buɗe ƙofan, wanda nima dole na natashi na zauna ina kallon bakin ƙofan da Ummi zata shigo, riƙo hannun Amaal tayi suka shigo cikin ɗakin a tare, har gefe na Ummi tazo ta zauna, kuma har lokacin idona duka suna zube akan ta, ko ƙiftawa banayi na ƙura mata su don ganin yadda sukayi ja sosai, alaman bayan tafiyan mu taci kuka ba kaɗan ba.
Hankalina gaba ɗaya naji ya tashi, lokacin da Ummi ta saka hannunta ta riƙo nawa kawai sai ta fara kuka mai ratsa zuciya, ganin haka ya saka ni ƙarasawa jikinta na rungumeta, ina kuka nace, “Ummi na mai ya sameki kuma”?.
“Humairah gobe mahaifinki zaizo, inajin tausayin shi bakaɗan ba, kuma inajin tausayinki, zai ga kaman da gangan muka bar ɗan mu zai keta miki daraja, wallahi Humairah ba halin Faisal bane, narasa dalilin da ya saka shi aro wannan ɗabi’an, kiyi haƙuri Hummy kada zumuncin mu ya ɓaci, don Allah kiyi haƙuri”? Ta ƙarasa tana mai matuƙar zubar da hawaye.
Jikina a sanyaye na fara share mata hawayen idon ta, “Ummi don Allah ki daina kuka, insha Allahu har abada zumuncin mu yana nan, ni ae ke uwace a gare ni, kuma Faisal yayah nane, kawai yanzu ma sharrin shaiɗan ne ya shige shi, amma insha Allahu zakiga Daddy nah ya fahimci komai, kuma zumuncin mu yana nan Ummi, sai ma abinda ya ƙaro”, na ƙara sa faɗi ina komawa jikinta na kwanta ina kukan, wanda Amaal daga inda ta ke a takure itama ta ke nata kukan.
Wannan ranan dai kam mutanen gidan gaba ɗaya basuyi bacci mai daɗi ba, duk zuciyar kowa babu daɗi har asuba tayi.
Wunin ranan gaba ɗaya Dr kin zuwa gidan yayi,dana gajji da rashin shi na ƙira shi amma sai ya nuna mun kanshi ne yake mishi ciwo, amma zuwa dare zai zo.
Haka dai muka wuni sukuku a gidan, kai hattah Faisal ɗin ma sai dana dawo ina tausaya mishi, saboda duk yadda akayi ya shigo gidan ƙi yayi, da aka matsa mishi yazo ayi breakfast sai ce wa yayi ya tashi da azumi, haka kowa ya zauna ranshi da zuciyan shi a dagule.
Daddy sai washegari da asuba jirginsu ya sauƙa, da yake ta sowan dare sukayi, jiki a sanyaye Abbu yaje taryenshi tare da driver, mu kuma aka barmu da haɗa breakfast, na lura Ummi gaba ɗaya a rashin walwala ta ke, ganin haka ya saka na matsa kusa da ita, a hankali na saka hannu na a kafaɗanta cikin hankali na ce mata, “Ummi don Allah ki kwantar da hankalinki, wallahi ni babu abinda zai raba mu fah, wannan abin mu ɗauke shi a Ƙaddara ne da yazo mana, don Allah Ummi ki kwantar da hankalinki, nasani kina damuwa ko Daddy na zai ƙullace ku ko? Toh ina mai tabbatar miki babu abinda zai faru, don Daddy na mai fahimta ne”, ajiyan zuciya
Ummi tayi ta juyo tana duba na cike da damuwa, “Humairah wallahi bana son kuga kaman mun bar Faisal bamu ɗauki wani mataki akai ba, kuma ina tsoron hala Daddyn ki yaƙi tarayyan ku da Amaal, gaskiya Faisal bai kyauta mana ba ko kaɗan”, ta ƙaresa faɗi kaman zatayi kuka.
Ƙara shigowan motan su Abbu ne ya saka mu saurin sauƙowa downstairs nida Amaal, da sauri nayi hanyan waje domin taryan Daddy, ina ganin shi da gudu na ƙarasa na faɗa jikin shi, lokaci ɗaya naji hawaye yazo mun, amma don bana son hankalin Daddy ya ƙara tashi sai nayi dabaran dana mayar da shi, ina rungume da shi na ɗaga kaina kawai sai naga Dr na a bayan Daddy yana duba na da murmushi.
Abbu ne yayi gyaran murya da nufin mu karasa parlor, Daddy yana rungume dani a gefen shi muka ƙarasa parlon, gaba ɗaya idon Dr yana kaina kaman zai jawo ni jikinshi.
Haka muka ƙarasa kowa ya nemi wuri ya zauna, Ummi ta fito fuskanta ɗauke da murmushi.
JAMA’A DON ALLAH KUMUN HAƘURI WALLAHI YAU MUNA TA BIKI NE, PAGE ƊIN BABU YAWA



