Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 23

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 23

8
0

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 23

__📖 Duk wanda ya dubi fuskan Dr Hussain sai ya ji tausayin shi sosai a ranshi, kuma sai kayi mamakin wani irin so yake yiwa Hummy, domin Dr Abdallah kaɗai yake ta fice-ficen tafiyan su, amma sam Dr Hussain ya kasa yin komai, yana zaune gefe na ya kama hannu na kaman wani zai ƙwace mishi ni, muna nan haka Dr Abdallah ya dawo ya zauna gefen Amaal, yana duban Dr nah yace,

” Dr saura 15mnt jirgin su ya tashi, gashi an fara neman passinger su shiga jirgi, ina ga ya kamata mu barsu haka su wuce ko?”.

Da sauri na ɗago kaina don jin irin ƙanƙame mun hannu na da Dr Hussain ya yi, shima ƙura mun ido ya yi kaman zai furta abu amma ya kasa, sai lips ɗin shi kaɗai na gani suna ta motsawa, matsowa na yi kusa da shi na kwantar da kaina a kafaɗan shi, lokaci ɗaya na ji hawaye yana bin fuska na, murya ƙasa-ƙasa nace,

“Dr nah zamu tafi, don Allah ka kula mun da kan ka”.
ina gama faɗa mishi na miƙe tsaye, wanda shi ma haka ya saka ya miƙe amma hannun shi yana riƙe da nawa hannun, murya ƙasa-ƙasa shima ya furta.

“Baby bana son ki tafi ki bar ni, kin amince na sanar da Daddy’n ki relationship ɗin mu”.

Damƙe hannun shi na yi da ƙarfi cikin nawa, “Dr bayan zu ba, kabari mugama wannan session ɗin tukun ya sani, kayi haƙuri Baby nah, ni dai ka kula mun da kan ka”.

“Baby ki kula mun da kan ki, kiyi hankali da larabawan nan, don Allah ko brother Amaal bana son ki bashi fuska kin ji baby nah”.
haka muna ji muna gani muka tafi muka bar su Dr da sai ɗaga mana hannu suke yi.

DAMMAM.

Abbu da Ummi ne suka zo taryan mu, haka muka shiga motan su in da driver ya ke jan mu har gida, a hanya Amaal kaman zata shige cikin Ummi, sai wani shagwaɓa ta ke ta mata, akan ko ina a jikin ta ciwo yake yi ma ta, ita kuma Ummi sai rarrashin ta ta ke yi, a haka har muka iso gidan, ni dai sai bin su da kallo kawai na ke yi, don gaba ɗaya sun ban sha’awa, sai smilling na ke tayi ina kallon su.

Kai gidan su Amaal ya haɗu, domin bansan yadda zan kwatan ta muku irin kyaun shi ba, duk da gidan mu yana da kyau amma tsarin ginin larabawa ba wasa bane, duk da muma daga waje Daddy ya kawo zanen da za’a mishi, amma gidan su Amaal ya ɗauki hankali na over, muna shiga parlon gidan gaba ɗaya ma sai naji ya tafi da hankali na, gaba ɗaya wani tsari ne da bazan iya rubuta shi ba a ɗan ƙaramin book ɗi na ba, sai dai kawai ku kwatantashi.

ga wani ƙamshi na musamman da ya ke yi, ɗakin Amaal Ummi ta raka mu in da shima aka mishi gyara na musammam, duk yadda ɗaki na ya kai da girma na Amaal ma ya yi biyun shi, domin wani gyara da akaman sai ya baka mamaki, bed biyu aka saka amma duk da haka da sauran space a ɗakin, bamu daɗe ba Ummi tace muyi wanka mu fito parlor mu ci abinci, haka muka shiga muka yi wanka, wani riga da wando ɗan pakistan Ummi ta kawo mana muka saka, sai ƙamshi muke yi kaman daga paris muka fito.

Muna kan dinning babu abinda ka keji sai ƙaran spoons, sai kuma daga parlor kana jin sautin news da a keyi a TV, gaskiya larabawa sun iya girki, idan ba wai santi ba sai nace sun fi ko wani ƴan country iya abinci, domin naji daɗin abincin da Ummi ta mana, domin duk dukiya na gidan su Amaal amma Ummi tana shiga kitchen, duk da yawan masu aiki da ke gidan amma tana saka hannu a aikin kitchen kaman wata ƴar nigeria, hakan yasa naga Amaal ta iya girki kala-kala, ga snacks da drinks iri da kala da ta iya, don bansaka girman kai ba duk sai da na koya a wurin ta, nima na gwada ma ta na ƙasan mu.

Parlor muka dawo muka zauna muna ta hiran school, anan Ummi ta ke gaya mana next week Faisal ma zai zo hutun 3weeks, haka muka yita hira kaman zasu ƙashe mu.

Kullum garin Allah ya waye sai mun yi waya da Daddy, yana gaya mun irin dauriyan da yake na rashin gani na, hakan zan ta bashi haƙuri, har da yace mun dabadan wani business daya sako shi a gaba ba zai tafi china, da yazo ya mun ko 1week ne, haka kullum za muyi ta hira, kuma yana gaya mun sunyi waya da Dr Hussain.

Allah sarki Baby nah, kullum dare idan muna waya ya dinga ƙorafin wai rana baya gudu dare ma baya gudu, haka zan ta mishi dariya, watara na muna hira nace,

“Dr mu to kaje wurin su Ummin ka mana ka yi hutu, kada kaɗaici ya dame ka kaji Dr nah”.
Na faɗa kaman zan mishi kuka.

Kashe wayan yayi ba tare da yace mun uffan ba, da sauri na saka hannu na rufe baki na ina tuna ranan fa yace mun kada na sa ke mishi magana su Hassan da su Abban shi, a zuciya na nace,

“me yasa bana jin magana ne”.
Da sauri na ƙira wayan shi amma firr yaƙi ɗauka, haka na yi haƙuri na kwanta ina ta saƙe-saƙe a zuciya ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here